Connect with us

MANYAN LABARAI

Mu Nemi Taimakon Allah Shi Kadai: ‘Dan Majalisa Ya Shawarci ‘Yan Siyasa

Published

on

A yayin da zabukkan shekarar 2019 suke gabatowa, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Awe/Doma/Keana, Ogoshi Onowa ya shawarci ‘yan siyasa da su dogara da Allah kadai a matsayin mai bada mulki, ya fadi hakan ne a yayin da yake gabatar da fam din shi na tsayawa takara a garin Lafiya dake jihar Nasarawa.

‘In da duk ‘yan siyasa zamu fahimci cewa Allah kadai ke iya bada mulki da duk wasu matsalolin mu sun kau, misali yanzu Sanata Suleiman Adokwe dan uwa na ne, amma tsarin dimokradiyya ba zai hana in kalubalance shi a takara ba, saboda tsarin yaba kowa damar yin takara.’ Inji Onowa

Onowa ya kara da cewa, yanzu kowa zai gwada sa’ar shi ne a tsakanin mu duk wanda Allah ya ba wa nasara zamu taru mu goya mishi baya, babban abunda muka sa a gaba shine jam’iyyar mu ta yi nasara a zabukkan shekarar 2019, kuma dukkan alamun sun nuna jam’iyyar mu ta PDP za ta yi nasara a zabukkan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: