Mohammad Bala Garba" />

Mu Sadakar Da Fatun Layyarmu Ga Gidauniyoyin Gajiyayyu Don Kara Mu Su Karfin Gwiwa

DGidauniyoyin CHNF (Creative Helping Needy Foundation) da CED (Women and Children Dream) gidauniyoyi ne da suka shawara wajen tallafawa nakasansu da marayu da marasa galihu a fadin kasar nan (musamman a yankin Arewa).

Manufar wadannan gidauniyoyi, shi ne, tallafawa gajiyayyu da raunana da nakasansu da marayu da marasa galibu da kuma ‘yan gudun hijira ta hanyar bada tallafin da suka samu daga hannun jama’a da kuma aljihunsu wajen siyawa mabuka kayan abinci, sutura, kula da lafiyar su, nema musu muhalli, saka yara a makaranta, da dinka musu kayan makaranta, biya musu kudin ragista da dai sauran nau’ikan abubuwan bukata na rayuwa.

Saboda halin da ake ciki ayau na wahalhalu, wanda ya sanya kullum matsaloli da fargaban rayuwa sake yawaita suke a cikin garuruwa da karkara, wanda yake haifar da idan mutum ya gamu da jinya hatta yadda za a je asibiti ma ba a samu. Idan kuwa an je asibitin, sai dai a dawo gida a zauna ba tare da an sayi magani ko an nemi jinyar da ta dace ba, har mutum ya galabaita wani lokaci kuma rai ya yi halinsa. Lamarin da ke kara zama kalubale ga gwamnati da kuma al’umma, musamman ganin yadda a wannan lokaci mutane ke fama da kansu cikin wahalhalu ba tare da samun yadda za su lura da kan su da iyalan su ba. Ko kuma abin da za su ci.

A wannan lokacin, sau da dama akan samu iyayen da ke gudun hijra ko iyayyen da ke da ‘ya’ya mata marayu ko marasa galihun da yawancinsu sun kai munzalin aure, amma iyayyen ba su da halin da za su musu kayan daki don aurar da su. Wadannan gidauniyoyi suna nemawa ire-iren wadannan taimakon kayan aure don kai su dakin mazajensu saboda kada a zuba musu ido don rashin galihu su lalace.

Sau da dama irin wannan tallafin yakan yi karanci a ofisoshi masu hali, saboda yadda mutane ba su cika bayar da tallafi ba, ko cika alkawarin abin da su ka dauka na bayar da taimako ga nakasansu ko marayu ko marasa galihun da kullum kara yawaita su ke a cikin al’umma. Sannan idan mu ka duba da irin wadannan mutanen, sun cancanci a taimaka musu.

Ya kamata mu san cewa idan aka wayi gari masu raunin cikin mu suna kwana da yunwa, ‘ya’yansu ba sa karatu kuma ba su da jari ko aikin da za suyi samu abin da za su kai bakin salati, to babu makawa za a wayi gari sun kasance barazana ko annoba ga al’ummarsu kamar yadda muke fama ayau. Saboda irin wahalar da aka shiga ayau, marayu da dama sun lalace, ‘yan mata sun shiga miyagun hanyoyi, matasa sun shiga shaye-shaye ko aikata laifuka, yayin da hatta iyayensu mata gwagware sun shiga munanan hanyoyi domin neman abin da za su ci su da ‘ya’yansu da ke gabansu. Wannan babban hakki ne a kan shuwagabanninmu masu kwashe dukiyar mu suna gina kansu da ‘ya’yansu. Sannan kuma kalubale ne ga wadanda Allah ya bai wa halin tallafawa irin wadannan mutane don gujewa irin bala’in da zai iya sauko wa al’umma saboda yin watsi da hakkin da Allah ya dora musu.

Haka itama gwamnati da mawadata muna fatar Allah yasa su lura da irin mawuyacin halin da mutane suke ciki a wannan lokaci, su sassauta manufofinsu na tattalin arziki domin tara wa gwamnati ko iyalansu dukiya alhali wasu na kwana da yunwa wasu na mutuwa da jinya ba tare da an taimaka musu ba.

Wannan kadai ya ishi mai hankali fahimtar bai wa wadannan gidauniyoyin kyautar fatan layya ko kudin fatan tamkar ba da gudunmawa ne wajen taimakon marasa galihu.

Saboda haka muke kira ga daukacin al’ummar musulmai wadanda Allah ya ba su ikon yin layya, da su sadakar da fatun layyansu ko kudin fatun ga wadannan gidauniyoyi domin samun gwaggwabar lada tare da karawa wadannan gidauniyoyi karfin guiwa wajen cigaba da tallafawa nakasansu da marayu da marasa galihu na fadin kasar nan.

Ga wadanda suke da niyyar ba da wannan taimakon domin dacewa da wannan gwaggwabar ladan tare da karawa wadannan gidauniyoyi karfin guiwa wajen cigaba da tallafawa nakasansu da marayu da marasa galihu na fadin kasar nan, za su iya turu da kudin fatun layyan nasu ga gidauniyoyi.

Exit mobile version