Mu Tattauna A Kan Auren Da Alkali Ya Kashe Saboda Gaza Ciyarwa

Alkali

A kwanan baya, wata Kotu a jahar Bauchi ta warware igiyar wani aure na biyu bayan da aka tabbatar da cewa mijin ya kara aure na biyun ne da keke Nape din da matarsa ta saya masa bayan ta sayar da gonar gado ta saya masa keken tunda bai da aikin yi don a rufa wa kai asiri.

Daga bisani ya sayar da Keke Nape din ya kama haya kuma ya rangada sabon aure na biyu.

Mijin matar mai yara biyar an tabbatar da cewa yaransa uku a gidajen abokansu suke kwana saboda gidan da suke ciki babu inda yaran za su rinka kwana.

Sai dai mijin ya kada baki inda ya ce, aure nufi ne na Ubangiji kuma Allah ne Ya ke ciyar da bawa ba wayau ko darbarasa ba inda ya ce yana da kwarin baya da ya ke ganin mace daya ba za ta gamsar da shi ba.

A ra’ayinku, kuna ganin Alkali ya yi masa adalci da ya kashe masa auren sabuwar amaryarsa?

Wannan tambayar ta sama da na yi a shafina ta jawo cece-kuce. Tabbas ma fi yawan masu bibiyar shafin sun yi amanna da cewa alkali ya yi daidai har inda wasu suka jijjina masa sannan wasu suke ganin da ya kara da tura shi gidan kaso.

Wasu kam sun yi, Allah wadai da wannan hukunci na alkali inda suka zarge shi da rashin sanin shari’a ko addininsa.

Ban ji mamaki ba don dama duk inda batu ya ke, za ka ga akwai bambanci ra’ayi. Sai dai a nan ba ni tare da wadanda suka kushe alkali har da amfani da addini don bayyana hujjarsu.

Akwai wani ra’ayi da ya fi ja mani hankali inda mai shi ya dage cewa alkali bai kyauta ba ko bai san kan shari’a ba don bai da hujjar kashe auren amarya.

Na ji dadi yadda wasu suka yi iya kokarinsu na fahimtar da shi cewa alkali ya kyauta tunda daga dukkan alamu, wannan mutumin ba zai iya ciyar da gidansa ba tunda ba ya da sana’a kuma ga nauyin da Allah Ya daura masa na wannan matarsa na farko da ‘ya’yanta bai iya saukewa ba.

Caraf shi wannan Bawan Allah sai ya kawo hujjoji guda biyu da suka ba ni mamaki a kokorinsa na nunawa cewa kashe auren bai dace ba. Na farko ya ce, ai karantarwar Musulunci ta nuna cewa, a kwai lokacin da akan zauna da yunwa a gidan Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi. Ya kara da cewa, ai Musulunci ya amince da auran bashi, don haka babu hujjar kashe auren.

Tabbas wannan gurguwar hujjar da ya kawo ta sa wasu sun amince da shi wanda nike ganin gara na kara tambaya, lallai da na buga wannan ra’ayina kan wannan batu inda nike kushe tunanin Malam Bahaushe, na samu mutane da dama sun yi mani raddi, wasu sun kira ni a waya don neman sanin hujjata da kuma mani gyara don rubutu ba tare da an samu rashin fahimta ba.

Zan kawo ra’ayin malamai na uku daga cikin ra’ayoyin da na samu kan wannan zance, a kasar rubutun, Farfesa Mansur Sokoto wanda a kowane lokaci in na yi rubutun da zai kauce hanya, ya kan fadakar da ni, ko ya karfafa mani gwiwa ne, baya kasa a gwiwa wajen yin haka. Abinda ya ce ba tare da dogon bayani ba shine, “Fahimtar addini da wasu suka yi kenan.”

Malam ya kara da cewa bayan na jaddada masa cewa mutumin nan ya ce za a iya zama da yunwa a aure ko a yi auren bashi kuma ya dage da ba da wannan a kan hujja,

“Mairo Muhammad Mudi Maganar ba ta dace ya yi ta ba. Wannan tauhidin kuda ne. Da Allah bai ce wadanda ba su iyawa su yi hakuri su kama kansu ba. In dai ya ce ana ba talaka aure amma yana nemon abinci wannan ana sauraren sa. Allah ma Ya ce, “Idan su talakawa ne zai wadatar da su” amma bai ce su zauna da yunwa ba.”

 

Hon, (Yallabai) Abdullahi Mahuta, ya jawo hankalina inda ya hore ni da na guji amfani da kabilanci ko addinin mutum maimakon haka gara na yi amfani da sunan mai wannan ra’ayi. Da zarar na ambace cewa, “mutumin Arewa” wasu za su ji zafi inda maimakon su dauki darasi da ke cikin wannan rubutu.

Yallabai ya fadakar cewa dole aure, yana ginuwa ne bisa yarjejeniya kamar na ciyarwa, shayarwa, muhalli duk yana kan namiji sai dai in matar mai hali ce ta dauke masa da kansa.

A kan wannan shari’a, Yallabai ya ce, ya kamata a tambayin amaryar ko iyayenta, in za su dauki nauyin ciyarwa da muhalli, har in sun amince a kan haka, bai halasta a kashe mata aure ba. Ya bayyana cewa alkali ba ya da hujjar kashe aure bisa karar da wani ya shigar dabam, misalin in matarsa ta farko ta kai kara kan dukiyarta, abinda  da alkali ya kamata ya yi shine ya tambaya kyauta ce ta ba shi ko kuwa bashi ko aro, in har kyauta ta bayar babu ruwanta da abinda ya yi da kyautar amma in bashi ne ko aro dole a tursasa shi ya biya ta abunta amma babu yadda zai yi ya kashe auren amaryar kan karar da uwargida ta yi.

Amma in amaryar ce ko iyayenta suka kai kara, dole ya cancanta alkalin ya sauwake mata saboda daga dukkan alamu mijin ba ya da halin rike ta.

Sannan ba zan rufe kawo ra’ayin wadanda nake tunkahon sune malamai na na ilimi ba sai na fadi yadda muka yi da Abdurrazak Yahuza Jere watau Editan wannan jaridar, inda ya kara ilmatar da ni cewa, tabbas ana auren bashi amma miji ba zai kusanci matarsa ba ko da an daura aure har sai ya biya wannan bashin sadaki. Sannan zancen ciyarwa, ya ce dole ne sai namiji na da halin ciyarwa kafin ya yi aure saboda wajibi ne a kansa ciyar da matarsa. Ya kara da cewa bayanin da mutumin nan ya yi cewa ana zama da yunwa agidan Annabi (SAW) ya yi wa abin gurguwar fahimta.

“Tabbas akwai bayanin da Nana Aisha (RA) ta yi, Malam Mai Littafin Ashafa ya kawo, cewa ana yin kwana uku ba a dora sanwa (girki) a gidan Ma’aiki ba (SAW), aka tambaye ta to me kuke ci? Ta ce “bakake guda biyu” ma’ana dabino da ruwa. Kin ga wannan ya saba da tunanin wancan mutumin, ba zama da yunwa ake yi a gidan Ma’aiki ba (SAW), akwai abincin da ake ci, dabino da ruwa. Kuma dabinon da za a ci a gidan Ma’aiki ai ba irin wannan dabinon namu ba ne busasshe da ake sayarwa. Dabino ne mai dadi da ya samu albarkar Manzon Allah (SAW). Na tabbatar dabinon da aka ci a gidan Annabi (SAW) ya fi naman da ake ci a gidajenmu, saboda albarkar Annabi (SAW). Sannan rashin dora girki yana karantar da mu ne talakawa kar mutum ya sanya kanshi a halaka wurin nema, ya yi kokari ya fita nema duk abin da Allah ya ba shi ya kawo wa iyalansa, su kuma su yi hakuri, su san cewa dole wata rana za a samu yadda ake so, wata rana kuma hakuri za a yi da abin da ya samu”.

Ina godiya ga duk wadanda suka ba da gudumawa kan wannan batu, da wadanda ra’ayinmu ya zo daya, da ma wadanda muka samu sabanin ra’ayi tare da manyan Malamai na wadanda ba su gajiya da ilmatar da ni a kowane lokaci.

Abun da zan kara kira ga jama’a tun wadanda suke da ra’ayin amfani da wasu misalai da ya faru lokacin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare Shi, da su nemi ilimi wajen malamai gudun kar su yi wa misalai gurguwar fahimta.

Misali, don an samu lokacin da aka zauna ba a yi girki a gidan Annabi (SAW) ba, ba shi ne hujjar da za ta sa ka hana matarka abinci ba, saboda ka fahimci abin a baibai, don ita kanta ciyar da matarka yana cikin dole a gare ka a sharuddan sunnan aure.

Kuma ina ga wannan misali, shi ne don ana son a koya mana hakuri in muka tsinci kanmu a wani irin yanayi inda za mu iya cewa hakan ya taba faruwa a gidan Fiyayyen Halinta kuma ya yi hakuri balle mu.

Kazalika in sunnar Annabi wannan Bawan Allah ya ke son ya yi koyi da ita, me zai sa hana shi koyi yadda Manzon Allah (SAW) ya ya zauna da Nana Khadijat (RA) ba inda Ya tafiyar mata da dukiyarta har ta samu inganci a sana’arta?

Shi wanda matarsa ta sayi masa Keke Napep don rufan asiri, ba a ce ya yi amfani da Keken da wannan sunar ba, sai a ce ya kau da abin da ya zama dole a kansa sannan ita ta zauna da yunwa?

Allah Ya datar da mu, Ya sake sada mu a mako na gaba a wannan shafi naku.

Exit mobile version