Wakilinmu" />

Mu Tattauna: Bincike A Kan Auren Mace Bahaushiya Da Matan Wasu Yaren

Matar Bahaushe ta fi kowace mace gata a duniya in ban da matan Larabawa da Turawa, amma ita ce ta fi gasa wa namiji aya a hannu.

A iya binciken da na yi, matar Malam Bahaushe tana da gata sosai sama da sauran matar kabilunmu, domin Malam Bahaushe bai yarda ya ga matarsa ta fita tana aikin karfi ko wahala ba. Shi duk talaucinsa ya fi so matarsa ta zauna a gida, shi ya fita ya yi aikin karfin ko wahalar domin ya nemo musu abin da za su ci su sha da ita da yaransu.

Da wuya ka ga matar Malam Bahaushe tana zuwa daukan ruwan da za su sha ko nemo abin da za su ci, ko daukar nauyin karatun ta ko daukar nauyin gidanta da na yaranta ko da kuwa mai hali ce.

Malam Bahaushe idan mai hali ne ma hatta girki da wanki ko wanke-wanke ya haramta wa matarsa, sai dai ya dauko masu yi mata hidima. Ita sai dai ta kwanta ta ci ta sha ta yi ibada, sai kuma kula da tarbiyyar yaransu kawai. Ko unguwa za ta je akwai direba idan ba mota a ba ta kudin a dai-daita sahu.

Amma wallahi abin takaici da haushi sai ka ji Malam Bahaushe kullum yana kuka da matarsa. Sam ba ta ba shi hadin kai, kullum tana cikin tashin tada masa da hankali. Da yawa daga cikin ire-iren wadannan matsalolin ne kan sa wani namiji karin aure ko Allah zai sa ya dace ko kuma ya yi tunanin tsallakawa ya auro wata kabilar ta daban, wacce yake tunanin zai samu zaman lafiya da ita a cikin zamantakewarsa ta aure.

Wai kuwa ayya matanmu na kasar Hausa suna lura da yadda matan wasu kabilun ke fama da aikin karfi domin daukar nauyin mazansu da yaransu kuwa? Ta dalilin aikin karfin da suke yi har jikinsu ya murde ya zama irin na maza. Kuma duk da haka suna girmama mazajensu duk da irin yadda suke gallaza musu kuwa. Wasu matan kabilun fa har su fita kiwon dabbobi ko yin itacen girki, wasu su yi aikin kafinta ko daukar bulo ko gini, wasu da ciki ko goyo suke wannan aikin kuma su samo kudinsu su dawo gida su girka abincisu su ci su da mazajensu da yaransu. Ke kuma matar Malam Bahaushe me ki ka sani game da irin wadannan ayyukan wahalar?

Ni dai wallahi na kasa fahimtar me yake damun wasu daga cikin matan Malam Bahaushe ne, ko dai dadi ne ya yi musu yawa.

A Musulunce, yanda Mallam Bahaushe yake kula da matansa haka ake so ana ma so ya kara kwazo ne ba ya rage ba, to amman matar Hausawa su ji tsoron Allah su yi biyayya yanda Allah Ya ce. Mazan Hausawa suma suna da tasu laifuffukan, amman zan kara bincike a kan dalilin sakin auren da ya yi yawa a wannan zamanin.

Tambaya: Ya ya za a yi matan Hausawa su gyara halayensu su san darajan miji? Kowa ya kawo shawara domin zai taimaka mana baki daya.

Muna sauraron shawarwarinku a kan mafita.

Exit mobile version