Bashir Dauda" />

Mu Tattauna

Ranar 24-3-2018 ce ranar da kungiyar Muryar Talaka Reshen Jihar Katsina ta gudanar da taron da ya kunshi masu ruwa da tsaki wadanda suka hada da shugabanni, kungiyoyin farar hula, ‘yan siyasa, ‘yan jarida da daidaikun jama’a. Taken taron shi ne: Tattaunawa game da yadda za a inganta rayuwar talaka. An fitar da fannoni guda uku da akai tattaunawar kansu. Wadannan kuwa sun hada da Kasafin kudi, kiwon lafiya da kafafen yada labarai.

Wannan tattaunawa ta gudana a dakin taro na otel din Katsina Motel, kuma an fara gudanar da taron wajen karfe goma da minitina 40.

Dalilin shirya wannan taron kamar yadda shugaban kungiyar Muryar Talaka Reshen Jihar Katsina, Kwamared Kabir Shehu Yandaki ya bayyana shi ne idan akai la’akari da dimbin matsalolin dake fuskantar Talakan Nijeriya, to har yanzu bukatar shirya tarukan nemo mafita ba sui kadan ba. Taron karawa juna sani a kasa kamar Nijeriya inda rashin gaskiya da kokarin boye gaskiya ya kazanta abu ne mai matukar muhimmanci. Har yanzu lokaci bai yi ba da za a daina tara mutane domin a fada ma juna gaskiya, koma ba domin komai ba, kasar kwata-kwata shekarunta 58 da samun ‘yancin kanta. A ma wannan lokaci har yanzu ba a fita daga magagin mulkin mallaka ba. Kai wasu ma na ganin fa har yanzu mulkin mallakar ake yi ma Talaka. Bambancin kawai shi ne, yanzu ‘yan uwanmu bakake, wani lokacin ma Allah daya ake bautamawa amma ke mamu mulkin fir’aunanci.

Idan aka dubi matsalolin da taron yai bita kan su, abubuwa ne da suka shafi rayuwar talaka kai tsaye. Misali mu dauki kasafin kudi. Duk wata karya da wani dan siyasa ko wani shugaba zai yi na inganta rayuwar talaka, to dole fa sai an kai abin a cikin kasafin kudi. Kasafin kudi doka ce cewa ba a taba kudaden gwamnati haka kawai. Kuma tsari ne dake yi ma gwamnati jagora wajen gudanar da aikace aikacenta. Ayyuka kalilan ne, wadanda basu da muhimmanci za a iya gudanarwa ba tare da an sanya su cikin kasafin kudi ba.

Sai dai kash duk da muhimmancin kasafin kudin, an maida shi wani abu kamar na wasu ‘yan tsirarru. Mutanen da suke rike kasafin kudin su yi yadda suka ga dama da shi ba su wace ‘yan majalisu da bangaren zartaswa ba, sai kuma shugabannin hukumomin gwamnati. Sai sun kammala komi, sannan za su kira ‘yan kungiyoyin farar hulal da suke so, su zo taron jin ba’asi inda mafi akasari ba aiki ake da shawarwarin kungiyoyin ba.

Idan ma talakan bai cikin kungiyoyin, to bama zai san abin da ake ciki ba. A mukalar da ya gabatar wajen taron Injiniya Muttaka Rabe Darma ya ce duk da kasafin kudin da ake yi duk shekara, Katsina na cikin jihohin da suke fama da talauci. Ya samo hujjojinsa daga wasu cibiyoyi masu bada alkalumma kan ci gaba. A cikin kasidar kuma ya nuna kasafin kudin da ake yi a Katsina bai kunshi bukatun talaka wa ba. Komai dai menene a bayyane take cewa ba kasafai ‘yan siyasa ke maida hankali kan abubuwan da suka damu talaka ba. Misali, akwai kauyukanmu dake cikin lunguna inda babu asibitoci, amma sai a dawo cikin birane da manyan garuruwa ana gyaran asibitoci. Wani kauyen, ruwan korama ake sha shekara da shekaru, maimakon a samar da ruwa, sai a dauki kudin karamar hukuma a gina masu kasuwannin zamani, inda daga karshe kasuwannin ba zasu inganta tattalin arziki, kauyen ba, sai dai su koma mafaka ta ‘yan shalisha da kodin, da masu lalata kananan yara.

Ko kuma matsalar ilimi ta karancin malamai ce a makaranta kaza, amma sai aje ana fenti, a bar makarantar ba mai koyawa. Mafi akasarin ma, makarantun da aka fi gyarawa sune wadanda ke bakin hanya, amma an bar na cikin lunguna a lalace. Wasu masana, na ganin dalilin da yasa ‘yan siyasa suka fi baiwa gine-gine muhimmanci shi ne, an fi satar kudi ta nan. Misali nawa za a sata ta hanyar daukar ma’aikata? Kusan ba a bin da ake samu sai ma hidima da zata karu. Maimakon a maida hankali wajen horas da malaman makaranta da na asibiti, ko wurin gina dakunan karatu da na bincike da zuba masu ingantattun kayan aiki, sai a koma wani abu daban. Wannan kwaskwarimar ce ta hana komi ci gaba a Nijeriya.

Mukala ta biyu wadda Dokta Abubakar Kurfi ya gabatar, ta maida hankali kan matsalolin kiwon lafiya, musamman Inshorar kiwon lafiya. In ba yanzu ba da aka samu dan arewa na jagorancin NHIS, mu nan Arewa ma ba mu damu da muhimmancin inshora ba. Wasu ma in kai masu maganar Inshora suna iya kafirta ka. Yanzu ne Farfesa Yusuf ke kokarin wayar da kai a Arewa, inda har ta jawo masa bita-da kulli daga ministan shi.

Matsalolin kiwon lafiya a Nijeriya yawa gare su. Kullum ana kasafin kudi akan kiwon lafiya, amma a banza. A cewar Dokta Abubakar Kurfi, talakawan kasashen da suka ci gaba ba su sayen kiwon lafiya. Koda suna saye, to baida wani tsada. Ya ce a inda mutum keda daraja, to duk abin da ya shafi kiwon lafiya, ilimi to gwamnati ce ke bada su.A nan Nijeriya, abun ba haka bane. Masu kudi ne ke iya samun kulawa mafi inganci , domin idan mutum yana son kada ana magani daban kaba daban, to dole ya tafi asibitin kudi. A nan Nijeriya babu ma wadatattun cibiyoyin kula da lafiyar. Indiya da Masar can masu kumbar susa ke zuwa a duba lafiyarsu. A nan sai dai ka je asibiti, inda za ka hadu da wulakancin nas ko likita. Muna jin yadda ake kashe mutane a asibitocinmu. In da sauran shan ruwa, mutum zai fuskanci wulakanci, kusan wasunmu na tunanin ko wulakanta majinyata na cikin kwasa-kwasan da ake koyawa a makarantun horas da malaman asibiti!

Wai ga wanda ma keda ikon zuwa asibitin. Wasu ai sai dai asha maganin na wagini baban Ai’sha magananin dake maganin kowace irin cuta. In da sauran jahilci kuma sai dai a tai wurin dan tsibbu, mutum na fama da cutar daji, dan tsibbu na gaya mai sihiri ne.

Saboda lalacewa da cin hanci da rashawa da tai ma sashen lafiya dabaibayi, cututtukan da tuni aka magance su a wasu kasashen da suka san ciwon kansu, mu har yanzu kokari ake a magance su da hano da katsari. Allah ya kyauta.

Mukala ta karshe da muka tattauna wajen wannan taro ita ce, wadda Muhammad Bashir Ruwan Godiya yai kan yadda za a inganta aikin jarida. A cewar Dokta Mukhtar El-Kasim malamin koyar da jarida a kwalejin kimiyya ta Hassan Usman Katsina, ‘yan jarida sun zubar da mutuncinsu, inda suke hada baki da barayin gwamnati ana tauye talaka. Ya ce dubi dakin taron nan, dan jarida nawa ya zo? Amma yau da ace taron gwamna ne da ka gansu birjik, saboda nan za a bada kudi, amma taron Talaka

Exit mobile version