Mu Yi Koyi Da Hakurin Manzon Allah (SAW), Sai Duniya Ta Zauna Lafiya – Shehu Isma’ila Almaddah

Shehu Isma’ila Almaddah

Daga Sulaiman Ibrahim

Tawagar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group bisa jagorancin Shehu Isma’ila Umar Almaddah sun gabatar da gagarumin Maulidin Annabi Muhammadu (SAW) a garin Kaduna inda dubban al’ummar musulmi daga sassa daban-daban na kasar nan suka halarta.

Maulidin wanda ya gudana a cikin daren 12 ga watan Rabi’ul Awwal na shekarar Musulunci ta 1443 zuwa wayewar garin ranar, ya kunshi karatun Alkur’ani mai girma, da zikirori da yabon Annabi Muhammadu (SAW) da kuma karanta tarihinsa tun kafin haihuwa har zuwa lokacin da aka haife shi.

Yanayin yadda aka tsara gudanar da maulidin ya yi matukar birgewa musamman yadda galibin mahalartansa suka yi shiga ta fararen tufafi da jajayen huluna da kuma fararen fitilu da aka kawata rumfuna da mazaunan baki a filin maulidin da ke gaban Zawiyyar Shehu Isma’ila Umar Almaddah a Unguwar Sabon Garin Tudun Wadan Kaduna.

Wani karin abin sha’awa a maulidin shi ne yadda aka fassara hudubar maulidin da Shehu Isma’ila ya gabatar a farkon bude taron da harshen Turanci, da Faransanci, da Fulatanci da kuma Ebiranci (Ebira) daya-bayan-daya.

Da yake jawabi kan falala da rahamar daren Maulidin a tattaunawarsa da ‘yan jarida, Shehu Isma’ila Umar Almadah ya bayyana cewa samuwar Manzon Allah (SAW) shi ne asalin rahamar Allah Ta’a’a.

Wani sashe na mahalarta maulidin

“Alhamdulillah, wannan dare, dare ne na farin ciki, dare ne na murna, dare ne na addu’a, dare ne na dabi’antuwa, dare ne na hakikantuwa, dare ne na shugabantaka, dare ne na farin ciki sabida samun ainihin Rahma, shi ne Annabi Muhammad (SAW) wanda Ubangiji da kansa ya gaya mana a cikin Alkur’ani cewa: bai aiko Annabi Muhammad (SAW) ba face rahama ga duk halitta. Wama’arsalnaka illa rahmatan lil alamin. Abin da malamai suka fassara da ‘Alam’ shi ne duk abin da ba Allah ba, Manzon Allah ya zama rahama a gare shi (SAW). To meye ma’anar Rahama din nan, jinkan Allah da tausayi na Ubangiji Tabaraka wa ta’ala, da shigar da mu Aljannah da Ubangiji zai yi duk rahama ce ta Annabi Muhammad (SAW). Fasalamun laka min ashabil yamin. Malamai sun fassara da cewa: ai ‘yan Aljannah suna samu wannan rahama da ni’ima ne sabida kai Yarasulullah. To kuwa, ai duk wanda ka samu alkairi da shi ba za ka taba mantawa da shi ba, ballantana wanda ka kubuta daga azabar wuta sabida shi.

“Don haka wannan dare kamar yadda muka fada, Daren Rahama ne, Daren murna da farin ciki ne da samun Rasulullah (SAW), da samun alkairai duka, da samun daukaka. Ya zo mana da Alkur’ani wanda shi ne tushen ilimi duka, Alkur’ani ya tafi da kimiyyar zamani duka. Za ka ga masu binciken fasahar kimiyyar zamani, sai sun yi bincike sun zo da sabon abu sai su ji malaman Musulunci a Jami’ar Azhar sun ce ai Kur’ani shekara kaza kenan ya fade shi. Akwai wani mutumin faransa, sabida wannan mu’ujiza ta Alkur’ani tasa ya tattaro Injila, Attaurah da Alkur’ani sannan da ilimi ya yi bincike a kansu, sai ya jinjina wa Alkur’ani cewa ba inda Alkur’ani da ilimin zamani suka rabu. Sai ka ga sun tabbatar da abin da yake Alkur’ani.

Wani bangare na kwalliyar da aka yi wa mazaunin maulidin

“Wannan dare, dare ne na addu’a gare mu sabida Lailatul kadri ya samu albarka sabida ya samu saukar Mala’ika Jibrilu ne da sauran Mala’iku. Wannan dare da Mala’ika Jibrilu da sauran Mala’iku suke sauka a cikin Watan Ramadana ya fi shekara 83, sabida saukar Mala’iku. “Salamun hiya hatta Madla’il fajr” inji Alkur’ani.

“Sabida haka, duk Malamai suka ce to ina darajar Daren da Aka haifi Annabi Muhammad (SAW)? Wannan dare, aminci ne ga rayuwar mu duka kamar yadda yake aminci ga lahirar mu. Sabida haka, za mu ci gaba da addu’a ga kasar mu, ga kanmu, shuwagabanninmu, malamanmu, iyayenmu da dukkan ma’abota alkairi na daga al’ummar Annabi Muhammad (SAW).  Allah ya kiyaye mu ya kiyaye shuwagabannin mu, ya sa adalci a cikin zukatansu su raya ‘yan kasa, ya dauke mana duk abin da ya fi karfin mu, ya kawo mana arziki albarkacin Rasulullah (SAW). Ya kara mana imani, ya taimake mu ya kara kiyaye mu albarkar Annabi (SAW).

Dangane da koyi da kyawawan halayen Ma’aiki (SAW) kuwa, Shehu Isma’ila Umar Almaddah ya bayyana cewa da za a dauki koyi da hakurinsa, duniya za ta zauna lafiya.

Wani sashe na mazaunin mata a maulidin

“Sannan dare ne na dabi’antuwa kamar yadda muke gaya wa kanmu dabi’un Manzon Allah (SAW), kyawawan halayensa, kyawawan sifofinsa sannan mu yi koyi da su. Kai ko daya muka dauka, misali mu dau hakurinsa, sai duniya ta zauna lafiya, mu dau juriyarsa, mu dau kokarinsa (SAW). Yana daga kokarin Manzon Allah (SAW), kila sau biyu ne kacal bai ja limancin masallacinsa ba. Na daya, ya tafi yana rabon gado cikin garin Madina, lokacin sallah ya yi sai Sayyadina Abubakar ya shiga ya ba da Sallah. Na biyu, Ranar yakin Tabuka, Manzon Allah (SAW) ya zagaya daji ya yi nisa sai sahabbai suka zata ana mai wahayi ne sai Sa’adu bin Abi Wakas ya shiga ya ba da sallah kila sai kuma na rashin lafiya inda ya umarci Sayyidina Abubakar ya ba da sallah. Manzon Allah (SAW) ya zauna shekara 63, shi yake shugabancin komai amma bai taba barin shugabancin ibada ba sai sau biyu kacal, lallai wannan ya nuna tsantsar kokarin sa (SAW).”

Almaddah ya kuma kara wa musulmi kaimi dangane da son Manzon Allah (SAW) da neman sanin sa kamar yadda ya kamata.

“Wannan dare ne na hakikantuwa da Manzon Allah (SAW), mu zurfafa soyayyar mu ga Annabi Muhammadu (SAW), mu zurfafa son sa, mu zurfafa ilimi a game da shi, don ya tambayi sayyidina Umar yana cewa ” Ya Umar, shin ko kasan ni waye?” Ta nan Malamai suka ce to wani ilimi ake nufi, don in sani ne na zahiri, Umar tare suka taso da Annabi kuma sirikinsa ne, ashe yanzun wata magana ce kuma. Ya dace mu zurfafa son sa da sanin sa, tun gabanin, ba wai sai munje kabari za a tambaye mu ba. Hadisai ingatattu wadanda Bukari da Muslim suka hadu a kansa na cewa duk wanda aka bizne a kabarinsa, za a zo masa da Annabi a tambaye shi “Meye ka sani game da wannan mutumin” in ya fadi kyakkyawar magana kan Annabi sai a ce kwanta ka yi bacci, amma da yace ban sani ba za a buge shi da guduma, kuma duk halittun duniya sai sun ji, sai dai Mutum da Aljan ne kawai ba za su ji ba.

“Dare ne na hakikantuwa da Annabi, ma’ana in dai ka hakikantu kuma ka dabi’antu da abu, to za ka zama kalifansa. Ma’ana mu zama na’ibansa wajen isar da sakonsa a aikace kafin a surutu. Allah yasa muyi koyi da shi, mu ganshi ko da a bacci ne, don ko a bacci ka gan shi to ka ribanta. Hadisi yazo Wanda Bukari da Muslim suka tabbatar da shi yana cewa ” Duk Wanda ya ganni a bacci to ya ganni a gaske, kuma sai ya ganni a falke don Shaidan ba ya kama da ni (SAW).”

Da aka tambayi Shehu Isma’ila kan gudummawar da ta kamata malamai su bayar kan abubuwan da ke faruwa na rashin tsaro kuwa, ya yi kira ga Malamai da su rika wa’azi ga mabiyansu da dabi’o’in Manzon Allah (SAW) da karatun da yazo da shi.

“Wata rana Firaministan Ingila ya yi zagaye a kasashen Musulmi, bayan ya koma garin sa, sai ‘yan majalisarsa suka tambaye shi a kan, me zai ce game da tafiyarsa, sai ya amsa da cewa ” In dai Ka’aba tana nan kuma Kur’ani yana nan, to musulunci yana nan cikin aminci.

“Alhamdulillah, har wanda ba musulmi ba ya san Ka’aba tana da girma amma duk da wannan girma da darajarta, wata rana Manzon Allah (SAW) ya kalli Ka’aba ya ce “Jinin Mumini ya fiki” kuma Allah ya kara da cewa ” Duk Wanda ya kashe mumini da gangan to sakamakon sa wutar Jahannama…”.

Wani sashe na mahalarta maulidin

“Su Malamai nasu fadakarwa, to ya dace su dinga fadar hadarin kashe rai. A zamanin Kalifancin Sayyadina Aliyu, Akilu bin Abi Dalibi dan uwansa ya zo wurin Sayyidina Ali yana cewa ya kai dan uwana ka ga yanzu kai ne shugaba ni kuma ban da kudi, ba za ka ba ni wani abu ba na arziki, Sayyidina Aliyu ya ce kwarai kuwa zan ba ka. Sai ya ce masa mu je Makera, da Isar su sai Sayyidina Aliyu ya dauki karfe ya sa a wuta, bayan ya yi jajawur sai ya dauko ya nana masa a jiki, sai Akilu ya yi kururuwa ya ce dan uwana ya haka? sai ya ce masa ka kasa daukar wutar duniya shi ne kake so in ba ka ta lahira?

“Al’ummar Annabi daraja ce da ita, wata rana Annabi yana zaune an zo shigewa da wata gawa sai Annabi ya mike, sahabbai suka ce Ya Rasulullah, Bayahude ne, sai ya amsa da cewa “amma dai rai ce!” Don haka malamai su fadakar a kan hadarin kashe rai.” Ya bayyana.

A yayin gudanar da jawabin maraba da baki a maulidin kuwa, Shehu Isma’ila Almaddah ya bayyana cewa duk abin da suka yi na shirya maulidin na’ibanci ne.

“Alhamdulillah, muna maraba da ‘yan uwa al’ummar Ma’aiki Annabi Muhammad (SAW), wadanda suka halarto wannan waje a cikin dare mai albarka. Muna yiwa ‘yan uwa bakin Annabi Muhammad (SAW) barka da zuwa, muna na’ibantar Manzon Allah (SAW), Shehu Tijjani da Shehu Ibrahim Kaulaha ma’abocin Faila cikin yi muku sannu da zuwa sabida shi ne Hadimin Annabi (SAW) bakinsa sai ya fi isarwa.

“Muna yi wa shuwagabanninmu na nan cikin garin Kaduna daga Shugaba Imam na babban Masallaci IRA moskue da ya buDe mana taro da addu’a da kuma dukkanin shuwagabanni na cikin gari, kowanne da sunansa da ainahinsa, kune masu saukar baki kuma a gidanku ne, kuma bakin a gidanku ake yi.

“Muna yi wa ‘yan uwa na duk garuruwa sannu da zuwa tin daga Zaria Kachia, Kura, Karfi, Kubau, Rahamar Wali, Gubuci, Miyere, Kano – Asimatul Faidah, Katsina (Sanah-sanah), Jibia, Kangimi, Gwarmai, Sabon gida, Bagama, Bauchi, Azare, Shirah, Dogon Jeji (Muna rokon Allah ya ba wa ‘yan uwa lafiya, sun samu hadari akan hanyar su ta isowa Kaduna Babbar zawiya Mauludin Annabi Muhammad (SAW). Wata rana Shehu Ibrahim ya yi Hajji, a kan hanyarsu ta zuwa Jidda sai jirgi ya fara tangal-tangal a sama, jama’a duk sun dimauce, sai Shehu ya ce me ye abun tsoro: Ko dai mu tafi Al’jannah ko mu sauka a Jiddah). Da sauran garuruwa irin su Shirah, Akuyam, Madara, Sarah, Sakuwa, Gadau, Gombe, Adamawa, Mabalwa, Taraba, Lau, Sagau, Hardawa, Bukur, Gusau, Sokoto, Illela, Rijau, Bago, ‘Yan Kwamin Larabawa, Gamawa, Dungun Mu’azu, Funtua, Zaki, Hadejia, Birnin Kudu, Jama’are, Lagos, Obajana, Lafia, Ilorin, Ibadan, Okene, Kebbi, Jega, Bagudu, Bakin Ruwa, Masha, Yauri, Shagogo, Mainari, Kiyawa, Soba, Gumi, Tsafe, Wusulu, Madalla, ‘yan Nono, Awai, Gwaranyo, Jahun, Neja, Dutse, Malam Madori, Rido. Wadanda ba a Fada ba, an fada gari daya, duk mu ‘yan garin ne.

“Mu ji mu cikin Annabi Muhammad (SAW), Allah muke roko da harshen martabarsa, wacce ta tattare Sifarsa, Sunansa da Zatinsa ya kiyaye mu gaba dayan mu da imani, ya tabbatar da mu a bisa Failar Shehu wacce ita ce Son Manzon Allah (SAW) da masoyansa da Neman alkairi ga kawunanmu da dukkan halitta, ya kawar mana da duk abinda mu da Duniya duk muke tsoro, ya azurta mu ya sanya mu ‘yan uwa Duniya da Lahira.

“Allah ya fada mana cewa, ‘Yan uwantakan duniya, in dai cikinsa ne tana amfanuwa a Lahira. Shehu Ibrahim yana cewa: “Mun gode Allah da muka yi ‘yan uwantaka cikin Allah duniya da lahira, duk wanda ya je shiga Aljannah ya tambaya, dan uwansa ya shiga, in aka ce bai shiga ba, to kar ya shiga har sai yak ama hannun dan uwan nan nasa.

“Alhamdulillah, ya zo cikin Hadisi, ranar Alkiyama Allah zai ce ina Muminai, ku shiga Aljannah da Falalata, ku kuma kowa ya kama hannun Fasiki daya ya shigar da shi Aljannah, shi kuma yazama albarkarku. Mu dukkanmu jiki ne guda daya, mun gode wa Allah mu Musulmai ne, Sufaye ne, Tijjanawa, ‘yan Faila abisa zuciya daya, mun taru a waje daya don Zatin Allah, don Manzon Allah (SAW). Hidimar wannan Mauludin, mun gode Allah ba mu mika hannu wurin kowa a waje ba don neman taimakon Naira, daga Naira daya har zuwa Miliyan ‘yan uwa Ahlul Faidati Mai Diwani Group suka hada kayansu.

“Alhamdulillah, Ahlul faidati Mai Diwani Group sun yanka manyan shanu guda biyu a Mauludin haihuwa, akwai ta Uku, an ajiye ta don Mauludin Suna. Annabi Muhammad (SAW) da muke koyi da shi, ga zuhudu ga babun a wancan lokacin amma a Arafa sai da ya soke Rakumi 63 da hannunsa, sannan Sayyidina Aliyu ya taimaka suka karasa sauran 37. Dukkanmu zuciyarmu daya, wannan shine duk muradun Addini hadin kan musulmi, duk wannan karatuttuka da ibadu abin da take so shi ne a yi soyayya a zama abu daya. Wannan ne babban abun da duniya take wa Shehu Ibrahim godiya a kansa da ya hada zuciyoyi wuri daya, duk da yana cewa “ina ma dai ni waliyyi ne, da karamar da zan yi, a kan zuciyoyi zan yi in hada kan ‘yan Adam.” Alhamdulillah, ya yi haka kuma.

“Annabin mu ya fi mu farin cikin wannan haduwa, yau ga al’ummarsa ta hadu waje daya, mun hadu waje daya don Zatin Allah. Annabi Muhammad (SAW) ya ce “Mumini madubin Mumini ne”, Sabida haka, muna yi wa Manzon Allah murnar wannan taro, muna yi wa Shehu Tijjani murnar wannan taro, muna yi wa Kalifan Shehu Tijjani, Shehu Ibrahim Kaulaha murnar wannan taron, sannan muna yi wa kanmu murnar wannan taro da muka halarta.  Ahlul faidati Mai Diwani Group mun kira kanmu da wannan lakabi, don ya zama sila ta yadda za mu iya ba da umarni a bi kuma mu san ta ina za mu fara, amma duk ‘yan faila Ahlul faidati ne, Alhamdu lillah.” Ya bayyana.

Bayan kammala wannan jawabi ne, sai Shehu Isma’ila Umar Almaddah ya dora da karatun maulidi a kan tarihin haihuwar Manzon Allah (SAW) inda aka kammala daidai goshin asalatu, aka kira sallah, bayan jam’i aka yi addu’a, baki wasu suka kama hanya, wasu kuma suka jira sai bayan an yi Maulidin Suna da za a gabatar ranar Litinin 25 ga Oktobar 2021, daidai daidai da 18 ga Rabi’ul Awwal zuwa wayewar garin 19 ga watan cikin yardarm Allah.

 

Exit mobile version