Gusau, " />

Mubayi’ar Katukan Tsafe A Gidan Wakkala: Yadda Abin Yake

Abin takaici ne ainun irin yadda wasu ke amfani da kowace irin dama domin cimma wadansu burace-buracen siyasa wanda ya hada har da ‘karerayi da yarfe wanda aka daina yayi a irin wannan lokaci na siyasar wayewa. Wannan kuwa ba zai zama abin mamaki ba ga manazarta siyasar Zamfara musamman idan aka yi la’akari da salon siyasar magoya bayan tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara Malam Ibrahim Wakkala wanda a wannan sabuwar gwamnatin ya ‘kara samun kusanci fiye da sauran abokan tafiyarsu na ‘G-8’ kai har ma da wasu jiga jigan da aka kafa PDP’n dasu, ta hanyar kutsa kansa domin samun gindin zama ko ta halin ‘ka’ka.

Wani abin yabawa da ya faru a jiya jiyan nan (Asabar) shi ne yadda tsohon mataimakin gwamnan ya kai ziyarar yaukaka zumunci wa iyalin Engr Abdullahi Abdul Karim (Katukan Tsafe) a gidansa dake Kaduna domin dubiyar mai dakin Katukan Tsafen wacce ta dawo daga jinya a kasar Masar (Egypt) ba da jimawa ba, kuma wacce suke da kyakkyawar alaka da uwargidan Mal Ibrahim Wakkala; ziyarar ta kasance ne bayan shi Malam Wakkala ya nuna bukatarsa wa Katukan akan cewa yana so ya ziyarce shi sai Katuka ya bashi lokacin da za a iya samunsa a gidan a wannan ranar, kuma cikin ikon Allah Malam Wakkala ya zo gidan a Kaduna, sai dai a lokacin ziyarar, ya zo da tawagar magoya bayansa ne da wasu ‘yan siyasa a cikin ‘yan rakiyarsa.

Bayan kammala ziyara da adduo’i na neman ‘karin samun sauki da Malam Wakkala ya gabatar sai aka fara daukar hotuna a wurin, wanda tun farko hakan bai yiwa Katukan dadi ba domin za a iya amfani da wannan akan wata manufa,  amma la’akari da wasu ababen sai ya kauda kai bai nuna rashin yarda ba, aka yi musafaha yayi godiya aka yi ban kwana da juna.

Ba a kai ko’ina ba, kwaram sai muka ga hotunan an fara cillowa a kafafen sadarwa na zamani (social media), a na kuma barbada labari a gari cewa ‘wai’ tsohon shugaban ma’aikata a fadar gwamnatin Zamfara ya kai ziyarar mubayi’a wa gwamnatin PDP a gidan tsohon mataimakin gwamna Malam Ibrahim Wakkala. Abin mamaki kuma shi ne daga cikin masu yada irin wannan karerayi har da wani na hannun daman Dr Dauda Lawal wanda yana cikin ‘yan rakiyar Malam Wakkala a lokacin.

Abin tambaya a nan shi ne, shin a yaushe aka bude ‘kofar yiwa sabuwar gwamnatin PDP ta Zamfara mubayi’a ta hannun Mal Wakkala ne?.  Shin a duk cikin ‘ya’yan PDP na akida babu wanda ke da kusanci da gwamna Matawalle ne har sai an biyo ta hannun dan APC wanda a jiya jiya suka sauka daga mulki?.

Magana ta gaskiya dai wadannan maganganu da ake yadawa ba gaskiya bane, illa ‘batanci wa Katukan Tsafe da kuma neman samun gindin zama da kusaci da ake son ko ta halin ‘ka’ka sai Malam Wakkala ya samu a wannan gwamnati ta PDP ya kuma zama ‘alif ja’ a tsakanin dukkan makusantan Matawallen Maradun na yanzu.

Katukan Tsafe Engr (Dr)  Abdullahi Abdulkarim yana nan daram akan jam’iyyarsa ta APC kuma bisa akidar maigidansa Dr Abdul’aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) ba gudu ba ja da baya. Bai kuma tafi gidan KOWA da sunan yiwa sabuwar gwamnati mubayi’a ba, illa dai yana mata fatar alheri.

A karshe, muna kira ga masu yada irin wannan maganganu da su sani cewa ba taimakon gwamnatin Matawalle suke yi ba illa zagon ‘kasa da wata ‘boyayywar manufa da suke da ita wacce za ta bayyana a nan gaba. Hakazalika za mu dauki matakin shari’a da dukkan wadanda bincikenmu ya tabbatar cewa da hannayensu a wajen yad’a irin wannan ‘karerayi domin ‘bata sunan maigidanmu Engr (Dr) Abdullahi Abdulkarim (Katukan Tsafe).

Allah ya tabbatar mana da ci gaba a jihar Zamfara da Najeriya baki daya, albarkar watan Ramadhan da na shagulgulan Sallah, amin.

_______________________
*Nasir ya rubuto wannan ne daga Gusau, za a iya samunsa a wannan lambar: 08036532789

Exit mobile version