Mudubin Imani

Sunusi Shehu Daneji +2348135260786 sshehudaneji52@gmail.com

 TAURARI

 Duka Taurari da mu kan gani a Samaniya da daddare idan gari ya yi wasai, wani kwallo ne curare na hautsinin sinadaren iska me kamanceceniya da Tauraruwarmu Rana.

Yayin da duk Allah ya sanya a dararenmu sararin sama ya yi wasai, idanuwanmu suna iya ganin taurari 19,000,000,000,000,000 ƙarara.

Kusancinmu da Rana shi ya kansa mu fi ganin hasken Ranar, kuma mu fi ganin girmanta a kan sauran biliyoyin taurari da ke can kololuwa a Samaniya.

Haka nan kuma a wayewar gari da ba mu ganin sauran taurari sai ita Ranar ba wai don su sauran taurarin basu nan ne ba, illa dai hasken Ranar da ke daf da mu ne ya kan dusashe hasken sauran taurarin. Lallai Kam Rana ta fi bamu haske da dimi da kuda ne saboda kusancinmu da ita sosai.

Rana tauraruwa daya rak ce daga cikin biliyoyin taurari da ke Samaniya suna nunkaya da dawafi,

Taurari wasu manya manyan Halittu ne da Allah mahalicci ya halicce su da sura curarriya kuma suke haskawa daga hasken jikinsu.

A cikin sararin Samaniya, musamman a cikin Biranen Taurari da ba su da iyaka, akwai biliyoyin Taurari da ke dawafi cikin katantanwa da nunkaya a ko da yaushe cikin tsari na bai daya.

Da yawa daga cikin Taurarin nan, su na da duniyoyi da suke kewaya su cikin tsari yayin da wasu kuwa su suke kewaya ‘yan uwansu Taurari cikin yanayi na katantanwa.

Ire iren wadannan Taurari da kan kewaya junansu sune TAGWAN TAURARI.

Tagwan Taurari ta ALGOL da ke Burijin Taurari na TAURUS suna kewaya junansu.

Taurari mafi kusa da mu a Samaniya na ALFA su ma tagwan taurari ne.

Dukkanin Taurari suna farawa ne daga wata mahaifar Taurari da ke wuri wuri a cikin biranen taurari. Wannan abu haka yake a birnin Taurarinmu na Milky way.

MAHAIFAR Taurari kanta tana farawa ne daga Taurarin da ke raye yayin da suke fidda sinadaran jikinsu na yau da kullum, ko kuwa daga burbushin kuwwar ragowar sinadaran matattuntaurari da ajili ya cim musu.

Ire iren wadannan sinadarai ne Allah me iko ya sanya su kan tattaru su cude a wata mahaifar don kuma samar da wasu sabbin Taurarin.

Tun can asali, lokacin da kan Dan Adam ya fara wayewa, mutane sun fara amfani da taurari ne don fahimtar da kansu sanin hanyoyinsu na tafiye tafiye, a ruwa ko a Hamada ko a kungurmin daji don samun fahimtar yanki yanki.

A Kokarin gane abubuwan da yawa a Samaniya ne ya sanyailimin kimiyar sararin Samaniya ya samo asali da tushe.

Sannu a hankali, kuma saboda kokarin yau da kullum dan Adam ya gano yadda zai yi amfani da wani tsari na taurari ta wata hanya da ba ta kimiya ba don yin tsubbu na al’amura ga kansa.

Tun daruruwan shekaru da suka shude, mutane suka rinka fahimtar wasu hadaka hadakada ke cikin wani ayari na Taurarin da suke iya hange a sararin samansu cikin wata surar abubuwan da suka sani na yau da kullum, ya alla surar ta dabbobi ce ko ta wasu kwari da suke iya shaidawa.

Da yawan wadannan surorin ne suka zama burujai da mutane ‘yan duba suka dora chamfe chamfensu a kai saboda zaton wani abu.

Duka Taurari, cikin hikima ta mahalicci Allah suna fara samuwa ne daga wani babban hautsini na sinadaran iska me launi daban daban da ke murtuke.

A zahiri wannan zarra-zarra ta sinadaran iska me tarin sinadarin HAIDIROJIN da HELIYOM da ke hajijiya da majajjawa mai karfi ne ke mulmula kansu su kan zama kwallon taurari.

Saboda kasancewar kuwwar karfi ta Magana dison kwazon da ke ga kowanne sinadarai da ke cikin hajijiyar nan yana da karfi sosai, sai Allah me iko yakan sanya su kan zuke kansu su cure ga wani dunkule. Daga nan sai hanzarin hajijiyar ya karu fiye da yadda ya fara.

Bayan wani lokaci duka dunkulan nan sai ya kan zama wani mulmulan curi mai tsananin kuda da yake cunkushe da gundarin makamashi mai yawa.

Yayin da Allah me iko ya sanya tsananin zafin dake ga mulmulan nan ya kai kololuwar zafi, wato ya kai kimanin awon zafi na miliyan 1. na awon zafi na salshiyos, kwayoyin zarra na sinadin makamashin da ke cikin curin zuciyar Tauraruwar, sai sinadaren su kan fara kyasta kansu da kansu don samar da haske na dundundun.

Kamar yadda mahalicci Allah ya tsarawa duka abubuwan halitta rayuwa haka tsarin rayuwar Taurari yake a gare su.

Daga matakin farko har ya zuwa mataki na karshe. Duka Arzikin tauraruwa na makamashi da karancinsa, tun farkon halittar Tauraruwa yake a tare da ita yayin haduwarta.

Duka taurarin da ke Samaniya wadanda muke iya gani da wadanda ba ma iya gani, Allah cikin iyawarsa ya sanya musu tsarin rayuwa kamar yadda yake ga kowanne abu.

Tsarin rayuwar taurari ya kasance yana kan wani tsari ne mai mataki mataki da ya dogara kacokan ga adadin makamashin da Allah ya sanya Tauraruwar ta ke da shi bias ga dangantaka da bukatuwar sararin samanta gabadaya.

Duka Taurari masu tarin gundarin makamashi me yawa taurari ‘yan ajin farko, suna da tsarin da Allah ya sanya su kai bai daya.

Haka nan kuma su ma taurari masu matsakaicin gundarin makamashi, wato irin su Rana, ‘yan ajin tsakiya.

Su kuwa taurari ‘yan ajin karshe su ne taurari wadanda gundarin makamashinsu ke kasa da na su Rana.

Adadin gundarin makamashi bias ga la’akari da gwargwadon bukatuwar amfani da makashin zai yi ga Tauraruwa shi ne yake nuna adadin dadewar da makamashin zai yi wannan Tauraruwar tana amfani da shi.

Bisa ga wannan tsari, na awo da gwargwajewar adadin gundarin makamashi a tare da rayuwar Taurari ne gwargwadon ajalin duka tauraruwa, Ga missali RANA tana daga Taurari masu matsakaicin gundarin makamashi da zai iya rayar da ita shekaru biliyan 10 tnu daga farkon samar da ita da Allah me iko ya ƙaddara.

Yayin da Tauraruwa PROƊIMA CENTAURI wadda ta fi kowacce Tauraruwa kusa da tawagarmu a duka Taurari na Samaniya, ita kuma take cikin taurari wadanda ke da dan gwargwadon gundarinmakakmashin da zai iya rayar da ita zuwa shekaru biliyan 100.

Tauraruwa SPICA wadda ke da gundarin makamashi ninki goma na kwatankwacin makamashin da Rana ke da shi, duk da yawansa za ta rayu shekaru miliyan 10 ne kawai.

Mafiya yawan taurarin da ke Samaniya, Allah me iko ya sanya suna daga cikin taurari ne da ke da matsakaicin gundarinmakamashi me karancin dawainiyar aiwatar, don haka rayuwarsu za ta tsawaita tsawon lokaci.

Rana tana daga cikin ire iren waɗannan Taurari.

 

Tauraruwa SPICA

Akwai kuma daga Taurari da a tun farkon halitarsu Allah madaukaki ya kan sanya su sami tarin makamashin da ya yawaita, amma yanayin sararinsu yakan sanya bukatuwar amfani da makamashin ta yawaita yadda a cikin kankanin lokaci su kan karar da duka makamashin.

Taurarin da kan fi tsawon rayuwa su zama su ne Taurarin da a tun farkon samuwarsu su kan zama suna da karancin amfani da dan makashin da ke tare da su saboda karancin bukatarsa ga yanayin sarinsu.

 

Exit mobile version