Hanyoyi 22 Na 17: Ka samar da taron mako-mako da iyalinka.
Hakan zai bada damar sanin abin da ke tafiya a rayuwar kowa da tattauna abubuwa masu mahimmanci da ci gaban iyalin. A nan kowa na iya bada labarin irin ci gaban da ya samu ko matsalar da ya ke fuskanta a harkar rayuwarsa. Haka na taimakawa matasa saboda harkar rayuwa na kara girmama ne a yayin da yaro ke kara girma, haka bukatar tallafin shawara na kara karuwa. Ana son a rika mutunta ra’ayin matasa duk da cewa iyaye na da kyau su bada shawarar da ya dace da matsalar da ake fuskanta.
18: Samar da lokacin shakatawa na Halal sau daya a wata.
Wasu na da tunanin cewa shakatawa haramun ne, suna tsangwaman musulmin da suke wasanni domin neman shakatawa saboda haka sai a ka guji hanyoyin shakatawa na musulunci irin su wakokin addini da wasu wasanni. Shirya lokaci da ‘ya’yanka za su baje kolin fasahar da Allah Ya basu na wake-wake da rubutattun wakoki, a tsara ka’idojin gasan tsakanin yaran gida a kuma bayar da kyaututtuka domin kara karfafasu a kan fito da baiwar da Allah Ya ba su.
19: Shiryar da su zuwa ga wadanda za su dauka ababen koyi a rayuwa daga cikin magabata.
Bayan kasancewar ka abin koyi ga yaran ka ta hanyar aikata koyarwar addini, ya na da kyau ka sama musu lattatafn tarihin Manzon Allah (Tsira da Mincin Allah su tabbaba a gare shi) da na Sahabbansa maza da mata in baka yi haka ba mutane da suke kallo a finafinai da talabijin yau da kullum za su zama abin koyi gare su. Ka rinka tattauna yadda rayuwar sahabbai ya kasance tare da kwatantasu da yadda a ke gudanar da rayuwa a halin yanzu, tare da bayar da misalai da sahabbai irin su Abubakar da Aisha.
20: Ka karanta litattafai da ke bayani a kan tarbiyar yara.
Litattafan na iya kasancewa na wadanda Musulmai suka rubuta ko wandanda ba musulmi ya rubuta ba matukar bayanan da ke ciki ba su kauce wa koyarwar addinin musulunci ba.
21: Ka aurar da su da wuri.
Harkokin da ke gudana a cikin al;umma a halin yanzu na tilasta tunannin badala a cikin rayuwar yara, hotunan da ke fitowa a talabijin na karantar da jima’i, manyan alunan talla a kan titi da cikin motocin haya kusan duk in da ka duba sai ka ga wasu hotuna da ke bayyanar da tsiraici, saboda haka matashi na fuskantar rikice-rikicen ribatar shaidan, aurar da su da wuri zai yi maganin wannan matsalar kuma ba sai sun dakatar da karatunsu ba idan suka nuna bukatar aure to ka taimaka musu in baka yi haka suna iya fada halin jima’i a waje, tabbas kana da laifin a kan haka, a kokarin ganin ka aurar da ‘ya’yanka ta tabbabar ba ka yi musu auran dole ba, ka bar su auri wanda suke so.
22: Daga karshe kuma ka lizimci addu’a.
Ka yi addua domin Allah ne ke shiryar da wanda ya so, ka yi naka kokarin a matsayinka na mahaifi, Allah Zai shirya maka da yaran ka su zama mutanen kirki, ka lizinci musu adduar a gabansu tare da bayyana musu kana kaunarsu kana kuma musu fatan alhairi.