Mugabe: Ba-Yabo-Ba-Falasa, in ji Mutanen Zimbabwe

A Zimbabwe, yayin da ake zaman makoki, ana ci gaba da bayyana ra’ayoyi masu karo da juna bayan rasuwar tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, wanda ya cika a wani asibiti da ke Singapore a ranar Juma’a yana mai shekaru 95.

Yayin da wasu ke bayyana shi a matsayin mutumin da ya samarwa kasarsa ta Zimbabwe ‘yanci, wasu kuwa cewa suke ya sha tafka magudin zabe da lalata tattalin arzikin kasar, kana ya yi ta muzgunawa jama’ar kasar.

“Ina ga Mugabe shugaba ne na gari, tun bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Zimbabwe, ya dora ta akan tafarki mai kyau, muna fatan Allah ya jikan shi.” Inji Rosemary Moyo, ‘yar kasar ta Zimbabwe.

“Mugabe ba Shugaba na gari ba ne ta kowacce fuska ka duba, ni ban san me na ke ji dangane da mutuwarsa ba, amma duk da haka, idan ka duba, shi ma dan adam ne, dole ne mutum ya girmama shi.” A cewar Tsiamo Moeng, wanda shi ma dan kasar ta Zimbabwe ne.​

Marigayi Mugabe ya kwashe shekaru 37 yana mulkar kasar ta Zimbabwe bayan da ya karbi mulki a hannun Turawa marara rinjaye da ke kasar a shekarar 1980.

Exit mobile version