Connect with us

KIMIYYA

Mugun Sabo Da Wayar Hannu Ne Yake Kawo Lallacewar Tarbiyya

Published

on

Al’ummar yankin arewa ta tsakiyar Nijeriya sune ganin mugun saboda da wayar hannu ne babban musababbin lallacewar tarbiyyar a cikin al’umma, musamman tarbiyyar matasa, wadanda su al’ammarin yafi yawa a cikinsu.

Masu da akayi hira da su sun ce a nasu ganin mugun sabo da wayar hannun shine babban musababbin hadurra na ababen hawa da ake yawan samu yanzu, musamman a cikin biranen kasar nan, a yayin da wasu suke ganin wannan shine ya jawo mummunar dabi’ar nan ta rashin son karatu.

Wani mahaifi da akayi hira da shi mai suna Abdullahi Sanusi mazaunin garin Jos, ya ce mafi yawan matasa suna bata kusan fiye da kashi 60 cikin 100 na lokacinsu wajen amfani da wayar hannu, inda suke kalle-kalle da jin wakokin disko, sannan suna amfani da wayoyin nasu wajen yin mu’amala da bata dace ba da ‘yan mata.

Mugun sabo da wayar hannu yana hana matasan yin abubuwa masu amfani a rayuwarsu, misali yana hana su sana’a da karatu da sauran abubuwa masu amfani, misali yakamata ace suna taimakon iyayensu wajen ayyukan gida da sauransu, amma ina suna can suna amfani da wayoyinsu.

Matasa maza sun fi mata amfani da wayoyin hannun, don haka yawan adadin matasa maza da suka yi mugun sabo da wayoyinsu ya fi na mata sosai, duk da su ma matan ba a barsu a bay aba, suna kusan duk abinda matasa mazan suke yi da wayoyinsu na hannu.

Matasa mata suna amfani da wayoyinsu don shiga kafofin sada zumunci, irinsu Facebook, Whatsapp, da sauran shafukkan sada zumunta na zamani, su kuma matasa maza suna buga wasannin intanet, suna shiga sha’anin siyasa da wasanni, musamman wasan kwallon kafa, maimakon su dinga shiga shafukkan da zasu karo da abubuwan ilimi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: