Abba Ibrahim Wada" />

Muhammad  Salah Ya Na Tasiri A Kan Yara Idan Su Na Kallon Sa

Mohamed Salah! Dan wasan kwallon kafa  Mohamed Salah ya zama abin kwaikwayo ga yara kuma tauraron Kasar Masar da ke haDa kan al’umma saboda yadda tauraruwarsa take haskawa

Wata uwa Musulma Rabiya Limbada ta bayyana yadda dan wasan na Liberpool, Muhammad  Salah, ya yi tasiri ga rayuwar ‘ya’yanta saboda yadda yake kamanni da su a matsayinsa na Musulmi.

Ta ce, “Gidanta ya rude da ihu a yayin da Mohamed Salah ya fara zura kwallo a ragar Roma a gasar zakarun Turai a daren Talata.”

Ta ce ‘ya’yanta Hanaa, mai shekara takwas da Muhammad mai shekara shida sun ruda gida da murna a yayin da muke kallon lokacin da Salah ya kai goshinsa kasa, kamar yadda ya saba idan ya ci kwallo.

Yana da wahala a samu gidan da ba a damu da martabar dan wasan na Liberpool ba a sassan Ingila, ko ma duniya baki daya saboda yadda yake kan ganiyarsa, Mohamed Salah yana hada kan al’umma.

Ya na addu’a a fili, sannan ya yi wasa da gemunsa, kuma yadda yake buga wasa yana kayatar da mutane a bana.

Matar ta ci gaba da cewa a gabashin Landan aka haife ta kuma ta girma, iyayenta sun yi hijira zuwa Ingila daga Yemen da Burma.

Ta ce ba kamar sauran mutane da suke shekaru daya da su ba, bata taba damuwa da ra’ayin kasancewa a matsayin ‘yar kasa ba.

Duk da haka,” ina da masaniyar cewa yara a zamanin nan daga addinai daban-daban tunaninsu ya bambanta”.

Tasirin labaran duniya da suke saurare kan iya zama dalilin da zai sa su yin taka-tsan-tsan wajen nuna addininsu don haka ba abin mamaki ba ne idan dan wasa kamar Salah ya ratsa zukatansu. In ji matar.

‘Yata Hanaa tana jin dadi a lokacin da take kallon Salah ya daga hannayensa sama yana addu’a bayan ya ci kwallo tana cewa “Mama, mu ma muna yin haka.

A na ta nuna magoya bayan Liberpool a Anfield rike da hoton Salah an rubuta Sarkin Masar Wasu magoya bayan Liberpool sun yi ta rera waka a kan masallaci da Musulmi a Ingila saboda kaunar Salah, al’amarin da ya burge Musulmi a sassan duniya.

Salah ne ya taimaka wa kasarsa ta Masar samun gurbi a gasar cin kofin duniya a Rasha dalilin kwallon da ya ci a fanareti.

Ko ya na buga wa Liberpool ko Masar wasa, a cikin minti 90 na kwallo yana hada kan al’ummar kasarsa inda ake yin watsi da duk wani bambanci na siyasa domin kallon tauraron kasar.

Mohamed Salah yana canza yadda wasu suke kallon musulmai, kuma wannan wani abu ne sabo. A karon farko, musulmi bai koma wani abin tsoro ba.

 

Exit mobile version