Daga Dr Aliyu Kankara Ibrahim,
Kwana biyu da suka gabata, wani babban malami na Jami’ar Bayero kuma mai bibiyar al’a umurran Shata ya yo ma ni waya, ya tambaye ni ko wanene Lalo? Na yi masa bayani cikakke.
To sai kuma ya bukaci in bayyana ma Duniya domin amfanin masoya Dodo na BS.
Muhammadu Lalo, asalinsa a Gwarzo aka haife shi, ta Kasar Kano. Wansa da ake kira Isah makeri shi ya yi sanadiyyar zuwan sa Ketare, ba ubansa ba. Sbd hk su makera ne, a nan Ketare. Gidansu na nan bayan gidan Na-Laye, uban Uban Garba Toli da Mare (wadda ta yi ma Shata rawar Asawwara, kuna ya yi ma ta waka).
Tsohon zama a Ketare ya san cewa daga gidan su Danjuma mai keke, sai gidan Jummai mai koko, sai sai gidan Balan Magajj (yaron maigarin Ketare) sai kwana.
Da mutum ya sha kwana, kamar za ka tafi unguwar gabas, babu wani gida da za ka taras a hannunka na hagu sai gidan su Lalo, ana kuma kiran sa da gidan makera. Gidan na duban yamma, bayan gidan maigari.
Muhammadu Lalo ya yi kirar farfaru (abun wuya, cunko, ‘yankunne, da sauran su.
Lalo baki ne, kusan ma bakikirin, dogo. Kuma za ya girmi Shata da kimanin shekara biyu ko abin da ya dara haka. Kuma, kada a manta, ya zo Ketare tun kafin 1940.
A nan Ketare Shata ya tarar da shi. Da shi da Shata, wanda ya yi sanadiyyar haduwar su a Ketare shi ne Dan maihura, dan sarkin marokan Ketare, watau Nazundumi, wanda ya zauna a hayin Kugun, kusa da gidan su Mammada. Shi Dan maihura, da shi ke waka a Ketare kafin bayyanar Dodo can a cikin 1940. Saboda hka, Shata ya gaji Lalo daga hannun shi Danmaihura, tunda shi ya ke ma amshi.
Shata kan same shi a gidan yana kira, sai ya ja shi su tafi ‘zage’.
Abdullahi Inde magajin Musawa ya shaida ma Ni cewa Lalo na daga cikin mutane biyar da suka raka Shata Bakori lokacin da ya gayyace shi da ya koma can da zama cikin Yuni 1943. Sannan, Abu na Binta da ‘Yar Auta ya taba yi ma ni tsokaci akan Lalo, ya ce ma ni da suka bata shi da Shata, sai ya dawo tashar kuka ya na yin kamasho. Bilhasali ma tare suka dan yi zama a nan tasha na wani lokaci.
Shima Sani Gadagau kuma Madawakin Magana na Sarkin Zazzau, watau Bakatoshi, ya yi ma ni tsokaci akan Lalo. Ya ce a da lokacin da ake yin rawa kasa-rika, kusan a cikin bataliyar ma’amsa ko Adamusawa, daga shi (Bakatoshi) sai Lalo, su kadai ke iya bin Shata wajen juyi,amma daga ba su ba, da an yi nisa ga juyi, to kowa sai ya fadi kasa amma ban da su uku.
Sannan, babban malamin Jami’ar ya ce in yi sharhi akan wata hira da ya ji Isa Zaki kanen matar Shata ya yi na cewa Lalo dan uwan Shata ne. To a shaida ma Isa Zaki, Shata ba ya da alaka ko dangantaka ta jini da Lalo. Saboda babu wani ko wata ‘yar uwar Shata da ya, ko ta fito daga fuskar Gwarzo ko Ketare.
Tasirin Wakokin Mata Ga Wadanda Aka Yi Ma Su Na Dokta Mamman Shata Katsina
Mata Ma’aikatan Gwamnati
Hajiya Binta ‘Yar Masaka Kakumi (1957) malamar tsabta ce a Dutsin-Ma a tsakanin 1957. Wakar da makadin ya yi mata a West End Hotel Dutsin-Ma. Duk da yake Bakandamiya wakar ‘mazan jiya’ ce, kamar yanda Shatan ya yi hasashe, amma an dauki amshin ta an yi ma Binta waka. Yana cewa a ciki: Malam ‘Yar Masaka, idan uban ki ke saka, to sako man bullan. Wakar ta kara jawo mata kwarjini da soyayyar jama’a a ko’ina. Wasu abubuwa da dama da a da kafin Shatan ya yi mata kirari sun fi karfin ta, bayan ya yi mata waka sai su ka kasance ma ta da sauki. Shata ya wake malaman tsabta da ‘yan doka, don dai zancen sub a ya cikin wannan takardar (Kankara, 2010a; 2010b; Gundawa, 2011; Maifada, 2007)
Matan Da Ba Su San An Yi Masu Waka Ba
Yana da nuna tausayi kwarai, in ji Safiya Garba (2014) da Mu’azu (2002) don hakane ma yak an yi ma wasu waka tun ma ba su da wayau. A wannan ajin akwai Hajiya Magajiya (Fatima) Hamza Kankara (1948), Hajiya Karime diyar Sarkin Pauwa Muntari Nadabo (1968) da Malama Maryam Umar Garba Hadejiya (Nuwamba,1994) Duk da yake wannan ajin aji ne na mata da su jingine suke da iyayen su ko mazanjen su ko kuma duka, cewa dalilan iyayen aka yi masu waka amma wakokin sun yi tasiri a gare su matuka (Rediyo Gangara, 2018) Ita Karime da aka yi ma taken Karime Diyar Makama, Karime Mulki ta gada/ ita da kan ta ba za ta iya tantancewa ba na abinda ya faru, amma ta nuna cewa mutane da dama sun sha ce mata Shata ya yi mata waka. Da yake lokacin da aka yi wakar shekarun ta biyu da haihuwa. Shatan ne ya sauka wajen mahaifin ta Muntari Nadabo Hakimin Kankara daga 1957 zuwa 1970. Yana wasa a kofar gida da dare sai Hakimi ya aiko Karime da kudi fam biyu ta kawo ma Shatan. Da ta kawo masa shi ne itama ya yi mata waka. Wannan ya nuna tausayi da son yara kanana da makadin ya ke yi, na kula su har yake yi masu waka.
Wannan Makaman da ya ambata ya na nufin Makaman Katsina Idris Nadabo kawun ta (Sule, 2001) To hakama ranar sunan Magajiya babbar diyar Alhaji Hamza Kankara a garin Pauwa cikin 1948 Shata ya je can ya yi mata waka. Karin wakar shi ne: ‘Yar Guzuma ‘yar Nuhu, Fatima jikar Dala/
Ita Maryam diyar Umar dan Garba Hadejiya, daga abokin mahaifin ta ya aurar da ‘yar sa, an kira Shata, su kuma sun kai masa abinci a makarantar iramare ta Guri shikenan sai da dare ya yi mata waka (Maryam, 2017)
Kammalawa/Rufewa
Duk macen da Shata ya yi ma waka, da an gan ta a wuri, za a zagaye ta ana kallon ta. Sirrin farin jinin wakar Shata ga wadda aka yi ma wakar shi ne: shi yana yawan tara masu kasa, ita ko mace abin da ta fi so ke nan. Idan ya kira mace doguwa, to watakila ma gajera ce. Idan ya ce ‘ga ki fara jajajir…’ to watakila baka ce, bakikirin ma. Barira Musawa baka ce kuma gajera. Amma a wakarta ya bayyana doguwa ce kuma fara. Sannan ya bayyana surar gashin ta, cewa kamar gashin karen ruwa…gobe a aske, jibi ya toho. To gashin Barira bay a da yawa ballantana har ya yi tsayi. Ka ga duk abin da ya fadi sabanin abin da ke akwai ga surar jikin ta ne. To wannan kambamar zulakin yana daukar hankalin matan da ya wake.
Wakokkin mata na Shata wani bangare ne na bunkasa adabi da harshen hausa, da adabi, wanda ya kunshi siyasa, ci-gaban kasa da kawo zaman lafiya. Wakokin sa sun buwaya, sun kawo canji mai matukar yawa a harshe da al’adar Hausa. Saboda dadi da azanci da hikimomin wakokin mata na Shata suka shige cikin tarihi da har abada a cikin adabin Malam Bahaushe ba za a taba mantawa da su ba.