Connect with us

BABBAN BANGO

Muhimman Bayanai Game Da Annobar Cutar Numfashi Ta COVID-19

Published

on

Yanzu ana namijin kokarin dakile da kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19 a sassan duniya. Kawo yanzu dai mutane fiye da miliyan 3 ne aka tabbatar sun kamu da wannan mummunar annobar a duk duniya, yayin da fiye da dubu 220 suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da annobar. A wasu sassan duniya, an rufe garuruwa, birane, da ma kasar baki daya, tare da bukatar mutane su zauna a cikin gidajensu, su kaucewa fita waje, a kokarin hana yaduwar annobar.
Wasu mutane na tsoron kamuwa da annobar. Idan sun ji alamar zazzabi, su kan damu sosai ko sun kamu da cutar COVID-19, to mene ne bambancin da ke tsakanin cututtukan mura, Flu da COVID-19?

Cutar mura, wani nau’in cuta ce da a kan kamu da ita yayin mutum ya gaji, ko yake jin sanyi. Alamomin kamuwa da cutar sun hada da toshewar hanci, yoyon majina, yin atishawa. Babu zazzabi kuma babu kasala. Haka kuma babu alamar ciwon kai, gabbai, da ma duk jiki baki daya. A yawancin lokaci, cutar murar ba ta da hadari sosai, ba ta yaduwa tsakanin mutane.
Annobar cutar Influenza, wani nau’in cuta ce wadda ke saurin yaduwa tsakanin mutane sakamakon yanayin kwayoyin cutar guda 3 wato A, B, da C. Annobar tana yaduwa ne ta hanyar yawu ko majina da suka bi iska, ko mu’amala da mai dauke da ita ko kuma taba wani abu da kwayar cutar ta taba.

Idan wani ya kamu da annobar, ya kan ji alamu masu tsanani cikin sauri, kamar zazzabi inda a wasu lokuta zafin jiki ya kan wuce digiri 39 cikin kwana guda, ciwon kai, rashin karfin jiki ko kasala, da rashin son cin abinci. Annobar cutar ta Influenza ta kan yadu a lokacin sanyi da lokacin bazara. A kan yi fama da munanan cututtukan da suka biyo bayan kamuwa da annobar, har ma wasu su kan kai ga rasa rayuka, musamman ma tsoffafi, kananan yara, masu juna biyu da marasa lafiya da ke doguwar jiyya.
Ruwa da miyau dake fitowa daga hanci da baki da kuma mu’amala da jama’a, su ne manyan hanyoyin yada annobar cutar numfashi ta COVID-19. Ana hasashen cewa, ana iya yada cutar yayin da aka sha ruwa ko shaki gurbatacciyar iska, sakamakon shigar najasar da ke dauke da kwayoyin cutar cikin iskar ko ruwan. Ban da wannan kuma akwai yiwuwar yada cutar ta hanyar iska wato yayin da aka yi tari ko atishawa da ke dauke da kwayoyin cuta.
Idan mutum ya kamu da annobar, zai rika jin alamomin zazzabi, rashin karfin jiki, da tari. Ba safai a kan yi fama da toshewar hanci da yoyon majina ba. Yawancin wadanda annobar ta harba su kan warke daga annobar cikin sauri kuma ba su cikin hali mai tsanani. Amma tsofaffi da marasa lafiya dake doguwar jiyya su kan fuskanci babbar barazana. Hakika mafi yawancin wadanda suka kamu da annobar a kan sallame su daga asibiti bayan an tabbatar sun warke daga cutar.

Wannan shi ne bambancin da ke tsakanin cutar mura da annobar cutar Influenza da kuma annobar cutar numfashi ta COVID-19. Ta yaya za mu yaki da cutar idan ba mu taki sa’a ba, mun kamu da su?
Cutar mura, annobar cutar Influenza da kuma annobar cutar numfashi ta COVID-19, dukkansu cututtuka ne da masu kamuwa da cutar suke fi dogaro da garkuwar jikinsu na yaki da cutar, idan cututtukan ba su yi kamari ba, akwai bukatar wadanda suka kamu su huta sosai a gida, su kwanta, su kebe kansu daga iyalansu da abokansu, su sha ruwa da yawa, su ci abinci mai ruwa-ruwa masu gina jiki. Bayan sun ci abinci, su wanke baki da ruwa mai dumi ko kuma ruwan gishiri mai dumi. A rika kuma wanke hannu a kai a kai. Kada a taba ido da hanci da baki da hannaye masu kazanta. Amma idan cutar ta yi kamari, ko kuma an kamu da cututtukan da suke biyo bayan kamuwa da cutar ta mura da annobar cutar Influenza da kuma annobar cutar numfashi ta COVID-19, to ya zama tilas a je asibiti ba tare da bata lokaci ba don ganin likita da samun jiyya yadda ya kamata.
Ta yaya za mu iya kare kanmu daga kamuwa da cutar?

Wajibi ne a rika sanya abun rufi baki da hanci, a rika wanke hannu da ruwa mai tsabta da kuma sabulu a kai a kai, a guji taba ido da baki da hanci. A nisanci wadanda suke tari ko atishawa a kalla mita 1.5. A tabbatar iska na shiga cikin daki a kowane lokaci, sa’an nan a guji zuwa wuraren taruwar mutane. Haka zalika kamata ya yi a rufe baki da hanci da kyalle ko takardar goge baki yayin da ake tari ko atishawa, ko kuma a rufe baki da hanci da gwiwar hannu a lokacin da ake tari ko atishawa don magance fitar ruwa da miyau daga hanci da baki.
Tun bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, masana kimiyya a duk fadin duniya sun fara nazarin gano asalin wannan mummunar annoba. Amma abin bakin ciki shi ne ya zuwa yanzu ba a tabbatar da asalin annobar ba tukuna. Kila za a dauki shekaru da dama don tabbatar da asalin annobar. Duk da haka, mai magana da yawun hukumar lafiya ta duniya WHO Fadela Chaib, ta bayyana a ’yan kwanakin baya cewa, dukkan shaidu sun yanke shawarar ce, cutar numfashi ta COVID-19 na da asali da dabba, kuma ba wani ne ya kirkiro ko ya samar da ita a dakin bincike ko a wani wuri ba.

Da take yi wa manema labarai karin haske yayin taron da aka shirya ta kafar bidiyo, madam Fadela ta ce, “WHO ta fada, kamar yadda na bayyana cewa, a matsayinta na hukuma mai kwarewa a fannin kimiya, muna tunanin cutar ta samo asali ne daga dabba,” watakila akwai ta a jikin jemaga, amma har yanzu ba a gano yadda dan-Adam ke daukar cutar daga jikin jemagen ba.
Ta kara da cewa, hakika akwai dabbar dake yada wannan cuta daga jemagu zuwa jikin dan-Adam. A don haka, ta yi alkawarin cewa, WHO tana maraba da dukkan kasashe, da su goyi bayan kokarin da ake yi na gano asalin kwayar cutar, tana mai cewa, kungiyoyi da dama, ciki har da masanan kasar Sin, suna can suna kokarin gano asalin wannan kwayar cutar.
A yayin da wannan annoba ta kasance abokiyar gaba ta dukkanin bil Adama, allurar rigakafi ita ce dabara daya tilo da za ta sa a cimma nasarar yakar annobar gaba daya. Masanan kasa da kasa suna dukufa wajen nazarin allurar rigakafi, kuma dukkanin al’ummomin kasa da kasa, suna mai da hankali kan yaushe ne za a samar da allurar a hukumance.
Bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, nan take, kasar Sin ta fara nazari kan allurar rigakafi. A ranar 12 ga watan Afrilun bana, hukumar kula da ingancin magunguna ta kasar Sin ta baiwa cibiyar nazarin kwayoyin halittu ta Wuhan, iznin gwajin allurar rigakafin cutar numfashi ta COVID-19, wadda za ta taimakawa jiki bijiro da garkuwa ta “Inactivated vaccine”, wannan shi ne izinin gwaji na farko da aka samar kan allurar rigakafi ta cutar COVID-19 a mataki na kasa da kasa. Sa’an nan kuma, an fara matakin farko na gwajin allurar rigakafin zagaye na farko a lardin Henan na kasar Sin. Cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta lardin Henan, ta aiwatar da wannan aikin gwaji, kuma gaba daya akwai masu aikin sa kai guda 32 da suka yarda a gwada allura a kansu a matakin farko.

A halin yanzu, al’ummomin kasa da kasa suna mai da hankali matuka kan aikin nazarin allurar rigakafi na cutar COVID-19, sabo da har yanzu babu takamaiman maganin wannan cuta. Izinin gwajin da aka bayar game da allurar rigakafin cutar COVID-19, ya nuna cewa, an dauki wani muhimmin mataki na samar da allurar rigakafi ga jama’a.
Sa’an nan, a kwanan baya, tawagar masanan dake karkashin jagorancin madam Chen Wei, wata kwararriya a cibiyar nazarin ilmin hallitu ta sashen likitanci na kwalejin kimiyya, da fasahar harkokin soja ta fara aikin gwajin allurar rigakafi da aka yi da kwayar cutar Adenovirus, dake dauke da sinadarin garkuwa, wato “Adenovirus vector vaccine” zagaye na biyu. A ranar 13 ga watan Afrilu, an yiwa Xiong Zhengxing mai shekaru 84 allurar rigakafin, wanda ya zama mutum mafi tsufa cikin dukkanin masu aikin sa kan.
Idan aka kwatanta da aikin gwaji zagaye na farko, za a ga cewa, aikin gwajin allurar rigakafin da aka yi da kwayar cutar Adenovirus dake dauke da sinadarin garkuwa zagaye na biyu, ya kunshi masu aikin sa kai wadanda suke da shekaru sama da 60. Chen Wei ta ce, sabo da tsofaffi sun fi saurin kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 mai tsanani, tabbas allurar rigakafin za ta samar musu garkuwa mai inganci.
A ranar 26 ga watan Janairu, tawagar Chen Wei ta je birnin Wuhan, ta kuma yi hadin gwiwa da sansanin masu nazari dake birnin Beijing, domin fara aikin nazarin allurar rigakafi. A ranar 27 ga watan Maris, ta kammala aikin gwaji zagaye na farko, inda ta yiwa masu aikin sa kai guda 108 allurar rigakafin. A halin yanzu, ana sa ido kan wadannan masu aikin sa kai, kuma ya zuwa yanzu, dukkan su suna cikin koshin lafiya.
Yanzu haka, annobar cutar numfashi ta COVID-19, ita ce babbar abokiyar gaba daya tak dake addabar daukacin bil-Adama. Abu mafi muhimmanci, shi ne mu guji yada jita-jita, mu yi kokarin dakile da ma kandagarkin annobar ta hanyar kimiyya, mu kuma ba da goyon baya da ma barin masu ilmin kimiyya, su yi aikinsu yadda ya kamata. (Marubuciya: Tassallah Yuan Daga CRI Hausa)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: