Muhimman Harkokin Dake Faruwa Tsakanin Sin da Nijeriya A Shekarar 2019

An Yi Taron Dandalin Tattaunawar Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Nijeriya Ta Fuskar Tattalin Arziki Da Ciniki A Abuja

A ranar 16 ga watan Afrilu na bana, An gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Nijeriya ta fuskar tattalin arziki da ciniki dangane da shawarar “ziri daya da hanya daya”a a birnin Abuja, hedkwatar kasar Nijeriya.
Ernest Afolabi, mataimakin ministan harkokin kasafin kudi da tsare tsare na kasar Nijeriya, ya jaddada a yayin taron cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatar ta kawo wa kasashen duniya alheri baki daya. Kana ta bai wa Nijeriya kyakkyawar damar kara azama kan yin ciniki da jawo jari daga waje. Ya kara da cewa, ci gaban fasaha ya sa kaimi ga bunkasar tasoshin jiragen ruwa, filayen jirgin sama, hanyoyin dogo da hanyoyin mota a Nijeriya.

0

Hanyar Dogo Ta Abuja Zuwa Kaduna Ta Kasar Najeriya Na Gudanar Da Aiki Yadda Ya Kamata
Hanyar dogo dake tsakanin Abuja da Kaduna a kasar Najeriya da kamfanin kasar Sin ya shimfida ya kuma samar da hidimar gudanarwa, ita ce hanyar dogo ta zamani dake na farko da kasar Sin ta shimfida a nahiyar Afirka. Ya zuwa karshen watan Afrilu na bana, hanyar dogon ta shafe sama da kwanaki 1000 tana aiki yadda ya kamata, yawan fasinjiji da aka yi jigilarsu ya wuce miliyan 1.5, hakan ya kasance wata muhimmiyar nasara da kasashen Sin da Najeriya suka cimma kan hakikanin hadin kan samun nasara tare a fannin manyan kayayyakin more rayuwa.
Hanyar dogon ta soma aiki ne a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2016, ita ce matakin farko na ayyukan zamanintar da hanyoyin dogo na kasar Najeriya, gwamnatin kasar Sin ce ta ba da rancen kudin gudanar da aikin kuma kamfanin CCECC na kasar Sin ne ya dauki nauyin ginawa tare kuma da samar da hidimar gudanarwa. Hanyar dogon ta hada Abuja, babban birnin kasar Najeriya, da kuma Kaduna, muhimmin gari a fannin masana’antu dake arewacin kasar, wadda tsawonta ya kai kilomita 186.5.
A watan Afrilu na bana, hukumar kula da zirga-zirgar hanyar dogo ta ma’aikatar sufuri ta kasar Najeriya ta ba da lambar yabo na “cika kwanaki 1000 da hanyar dogo ta Abuja zuwa Kaduna da fara aiki lami lafiya” ga kamfanin CCECC dake Najeriya.

Shugaban Najeriya Ya Yabawa Taimakon Kasar Sin Na Cimma Muradin Kayayyakin More Rayuwa
A ranar 10 ga watan Mayu na bana, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yabawa kasar Sin bisa taimakon da take baiwa Najeriya wajen cimma burinta na samar da kayayyakin more rayuwa.
Shugaban ya ce, kayayyakin more rayuwa a Najeriya sun tabarbare a wasu shekaru da suka gabata, lamarin da ke shafar yanayin rayuwar al’umma kana lamarin yana haifar da hasarar rayukan al’umma sakamakon hadduran da ake samu wadanda ba’a iya kauce musu.
“Muna matukar godiya ga kasar Sin bisa namijin kokarinsu na sake gina mana kayayyakin more rayuwa, da kuma samar da taimakon kwararru ga kasarmu. Zamu bayar da dukkan hadin kai da goyon da ake bukata, domin ganin an farfado da dukkan muhimman kayayyakin more rayuwar da suka turkushe ko kuma suka tsufa,” inji shugaba Buhari.

An Shirya Taro Kan Hadin Gwiwar Sin Da Nijeriya A Abuja
A ranar 16 ga watan Mayu na bana, an shirya wani taro mai taken “cimma ra’ayi daya tsakanin Abuja da Beijing”, ko kuma Abuja-Beijing Consensus a Turance a Abuja, hedkwatar kasar Nijeriya, wanda kamfanin jaridar Leadership ta Nijeriya ya shirya.
Zhou Pingjian, jakadan kasar Sin a Nijeriya ya bayyana a yayin taron cewa, kasar Sin tana son inganta tuntuba da cudanya da Nijeriya, da zurfafa dankon zumunci a tsakanin jama’ar kasashen 2 da kyautata hadin gwiwarsu ta fuskar tsaro, da kara azama kan aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, a kokarin kara kawo wa kasashen 2 da jama’arsu alheri na a-zo-a-gani.
Mahalarta taron ‘yan Nijeriya, sun yi kira ga gwamnatin kasar da ma bangarori daban daban na kasar, da su yi koyi da kyawawan fasahohin kasar Sin wajen farfado da kasa da fitar da jama’a daga talauci. Suna ganin cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya”, ba shawarar yin hadin gwiwa ba ne kadai ga Nijeriya, domin za ta sabunta huldar abota a tsakaninta da sauran kasashe. Sun ce kamata ya yi Nijeriya ta bude kofarta ga shawarar ba tare da wata rufa-rufa ba, ta kuma yi amfani da damar da shawarar za ta kawo mata domin gaggauta raya kanta.

Sin Ta Baiwa Dalibai ‘Yan Nijeriya 58 Kyautar Kudin Karatu Na Shekarar 2019/2020
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya ya gabatarwa dalibai ‘yan Nijeriya 58 kyautar kudin karatu na gwamnatin kasar Sin na shekarar 2019/2020 a ranar 6 ga watan Agusta na bana, tare da ba su takardar sanar da daukar dalibai, wadannan dalibai 58 sun tashi zuwa kasar Sin a watan Satumba, za su kuma kara ilminsu na digiri na farko ko biyu ko dakta a fannin injiniya, ilmin likitanci, ilmin noma, da ilmin gudanar da harkoki da dai saurasu.
Jakadan Sin dake kasar Zhou Pingjian, ya taya wa wadanda suka sami kyautar kudi karatun murna, tare da kara musu kwarin gwiwar ganewa idonsu yadda kasar Sin take yauzu, da himantu wajen karatunsu da cimma muradunsu, ta yadda za su ba da gudummawarsu ga ci gaban Nijeriya a nan gaba.

Huawei Ya Horas Da Ma’aikatan Najeriya Dabarun Tafiyar Da Harkokin Gwamnati Ta Intanet
Hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Najeriya, ta kara haifar da kyakkyawan sakamako, yayin da katafaren kamfanin sadarwa na kasar Sin Huawei ya kammala horas da ma’aikata 935 daga Najeriya, dabarun fasahar sadarwar zamani.
Shirin horon mai taken “sauyi karkashin fasahar sadarwar zamani”, an fara shi ne a watan Janairu aka kuma kammala a watan Yunin wannan shekara, an kuma gudanar da horon ne cikin rukunoni 19. Manufar horon dai ita ce, horas da ma’aikatan kasar ta Najeriya dabarun fasahar sadarwar zamani da inganta harkokin gwamnati ta intanet.

‘Yan Kasuwar Nijeriya Sun Yabawa Bikin CIIE Da Sin Ta Kira
Mataimakiyar jami’in dake kula da dangantaka tsakanin kasa da kasa ta cibiyar ciniki da raya masana’antu ta jihar Lagos na Nijeriya, Temitope Akintunde ta bayyana cewa, a halin yanzu, harkokin cinikayya tsakanin kamfanonin kasar Sin da mambobin cibiyar da suka halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, wato CIIE karo na biyu, na karuwa sosai. Ta ce lallai bikin CIIE ya samar musu damammakin ciniki da yawa, ya kuma bude musu kofar yin ciniki cikin kasuwannin kasa da kasa.
Madam Akintunde ta bayyana haka ne yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na biyu, wanda ke gudana a birnin Shanghai na kasar Sin daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamban bana.  Inda a bana, ta sake jagorantar tawagar wakilai ‘yan kasuwar Nijeriya don halartar bikin karo na biyu.
Ta kuma kara da cewa, jimilar mambobin cibiyar 13 ne suka halarci bikin baje kolin na bana, adadin da ya ninka kusan sau biyu idan aka kwatanta da na shekarar 2018.

An Yi Bikin Cika Shekaru 10 Da Kafuwar Yankin Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Nijeriya Da Guangdong
A ranar 26 ga watan Nuwamba, an gudanar da bikin taya murnar cika shekaru 10, da kafuwar yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Nijeriya da lardin Guangdong na kasar Sin. Cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata, an kafa kamfanonin kere-kere dake kan gaba cikin Nijeriya, har ma cikin dukkanin yammacin kasashen Afirka a wannan fanni, lamarin da ya zama muhimmiyar alama ta hadin gwiwar Sin da Nijeriya ta fuskar harkokin masana’antu.
Yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Nijeriya da Guangdong yana jihar Ogun dake kudu maso yammacin Nijeriya. Daga watan Yuli na shekarar 2016, kamfanin New South na lardin Guangdong ya dauki nauyin gudanar da harkokin wannan yanki. Mataimakin shugaban kamfanin New South, kana babban manajan kamfanin zuba jari a kasashen ketare Deng Yu ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, gaba daya akwai kamfanoni 63 da suka yi rajista a yankin, wadanda suka hada da masana’antun samar da kayayyaki na amfanin yau da kullum, da kayayyakin cikin gida, da kayayyakin karfe, da kayayyakin gine-gine da katako da sauransu, kuma ana bunkasa harkokin sarrafa katako, gine-gine, da cinikayya cikin hadin gwiwa a wannan yanki, lamarin da ya samar da guraben ayyukan yi sama da dubu 6 ga mazauna wurin.

Exit mobile version