Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home HANTSI

Muhimmancin Aurar Da ‘Yan Mata Lokacin Da Suka Bukata

by Sulaiman Ibrahim
January 29, 2021
in HANTSI
2 min read
Muhimmancin Aurar Da ‘Yan Mata Lokacin Da Suka Bukata
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Lallai akwai babbar illa ga tarbiyyar yara mata lokacin da suka bukaci yin aure aka hana su. ‘Yan mata da yawa sun fada cikin gurbacewar tarbiyya lokacin da suka bukaci yin aure aka hana su. Wani lokaci yara mata kan bukaci yun aure, amma sai iyayensu su hana su, ko don saboda karatu ko kuma wanda suka kawo su iyayen ba sa son su, ko kuma saboda wadansu dalilai na su na daban, wanda yin hakan ba karamar raunata tarbiyyar yara mata ya ke yi ba.

Sakamakon hakan, sai ka ga sun fada shaye-shaye, karuwanci da sauran wasu
hanyoyi da ba su dace ba. Kamar wata yarinya da ta bukaci mahaifinta ya yi mata aure, kuma har ma ta kawo wanda ta ke so, amma mahaifin nan ya ki, daga karshe yarinyar ta rubuta masa wasika cewa, “Na tafi idan ka zo Allah ya yi mana shari’a.” Sai ta hau saman bene, ta fado ta mutu har lahira. Haka zalika, an wata yarinyar da ta samu mahaifinta ta bayyana masa cewa, ya yi mata aure ko kuma ta lalace ta bi duniya.
Idan za a samu irin wannan lamari, to ya kamata iyaye su tashi daga barcin da suke yi wajen aurar da ‘ya’yansu a lokacin da suka bukaci hakan, ko da kuwa mahaifin nan bai da kudin aurar da ‘yarsa.
Idan har aka kai ga irin wannan matakin, to ya kamata shi uban ya kira saurayin nata ya bincika ya ga idan har mutumin kirki ne, to sai ya zauna da shi ya bayayyana masa cewa, shi fa bai da kudi, ya kawo abin da ya sauwaka sai a daura musu aure, domin yin hakan shi ne mafita.
Lallai iyaye su sani cewa Allah zai tsai da su ya tambaye su hakkin ‘ya’yansu ranar alkiyama, su daina cutar da ‘ya’yansu wajen hana su aure lokacin da suke bukata,
domin ba su san yadda suke ji ba. Idan har ‘ya mace za ta iya tunkarar mahaifinta a kan ya yi mata aure, to lallai hakan yana nuni da tura ta kai bango. Kamata ya yi iyaye su rika jin tausayin ‘ya’yansu wajen tashin hankali da suke fuskanta lokacin da sha’awa ta same. Ba dai-dai ba ne a ce, iyaye sun yi sanadiyyar lalacewar ‘ya’yansu wanda Allah dankasu amanarsu a hannunsu.
Daga karshe ina kira ga iyaye su rage son abin duniya, domin abin duniya yana karewa
ya mutum, ko kuma mutum ya tafi ya bar abin duniya. Nuna kwadayin a kan sai ‘ya’ya mata sun kammala karatun boko kifin aure, wannan ba dilili ba ne. A aurar da mace idan mijinta ya bari ta ci gaba da karatu, to sai ta ci gaba, idan kuma ya ki yarda, to sai a bar ta da wanda ta samu tare da rokon Allah ya sa masa albarka. Ina fatan iyaye za su amfana da wannan karamar shawara tawa da kuma yin amfani da ita na barin ‘ya’yansu su yi aure a lokacin da suke bukata.

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda Albarkatun Iccen Gora Suka Taimaka Wajen Fitar Da Al’umma Daga Kangin Talauci A Kasar Sin

Next Post

Auren Da NaKe Muradi

RelatedPosts

Auren Da Nake Muradi

Auren Da Nake Muradi

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

Daga Yusuf Shuaibu Matasa wannan sashi ne na musamman da...

Yana Da Matukar Mahimmanci Ma’aurata Su San Wadannan Abubuwa

Yana Da Matukar Mahimmanci Ma’aurata Su San Wadannan Abubuwa

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

Daga Yusuf Shuaibu Ya zama wajibi mu yi kokarin wanin...

Ma'aurata

Muhimmancin Yarda Da Juna A Tsakanin Ma’aurata

by Muhammad
2 weeks ago
0

Yarda na nufin amincewa da bambamcin halayya da ke tsakanin...

Next Post
Auren Da NaKe Muradi

Auren Da NaKe Muradi

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version