Fasto Yohanna Y.D. Buru" />

Muhimmancin Jaje A Wannan Lokaci

Wurin Karatu – Romawa 12:15:  “Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka” (Romawa 12:15).

Shalom!

A yau za mu juya akalar maganarmu zuwa gefen jaje ne. Litaffin Maitsarki (Bible) na koyarwa Kiristan duniya zamantakewa da kowane irin mutumin duniya, ba tare da nuna wani bambanci. Kiristan duniya na da bukatu na jiki da na Ruhaniya, kuma ba zai iya cimma wadanan burika ba ko ya sami biyan bukatarsa ba tare da ya yi mu’amula da wasu mutane ba.

Domin bukatan juna dole ne Kiristan duniya ya kyautata mu’amula da sauran al’umma da ya ke zaune tare da su. Akwai abinda zai shafi makwabcinka ko kuwa zai shafe ka da ka na bukatar taimako ko wanda zai taimaka ma ka.

Ta wurin wannan ne Manzo Bulus ya ruwaito wa Kiristan Romawa da na duniya cewa: “Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka” (Romawa 12:15).

A yau mun wayi gari a kasarmu Nijeriya zaman lafiya ya zama bakon abu. Ay au maganar tsaro ya tabarbare zuwa ga wata matsayi da talakawa su na cikin zaman zulumi a kowane lokaci, domin rashin cikakken tsaro a wadansu wurare, tun ba ma a Arewa ba, har ma zama lafiya na karanci fiye da yadda a ke tsammani.

Domin tsanani rashin zama lafiya wadansu sun yi kaura sun bar wurarensu. Kashe-kashen Bil Adama ya zama ruwan dare gama duniya. Ga kashe-kashen irin na ’yan ta’ada, ga masu garkuwa da Bil Adama domin neman kudin fansa. Fada tsakani Fulani da manoma, ita ma ta zama ruwan dare gama gari.  Har ma ya kai ga yadda su ma sun rasa mahallinsu. Kuma a  ko ina a Arewa na cike da ‘ Yan Gudun Hijirah. Kusan da gwamnati da talakawa suna cikin wahala a ko ina.

Ga  Ambaliyan ruwa da mutane da yawa su ka rasa gidajen su, dukiyarsu da rayukansu. Ambaliya na Jihar Katsina na cikinsu domin da haka za mu dauki wannan lokaci domin muyi wa yan’uwan mu da makwabtanmu jaje da dukan abunbuwan da ke faruwa a kasarmu tun ba Arewa ba.

A takaice, a Arewa akalla jihohi 13 da babu dawamamen zaman lafiya baicin:

1.Gombe

2.Bauchi

3.Jigawa

4.Kano

5.Sokoto

6.Kebbi

Wadanan Jihohin su ne kadai da ke da kwarya-kwaryar zaman lafiya, amma sauran jihohin, to ga su nan dai!

Don da haka Ina so in idar da sakon  jajena da na iyalina da na Ekklisiya da na al’umma Kiristan Arewa da Kiristan Nijeriya ga makwabtanmu, watau da Musulmi, Kirista da mabambantan addinai bisa ga abubuwan da ke faruwa a Arewa da Nijeriya gabadaya.

A kwanakin baya jihar Bauci ta sami nata kason na ruwa sama da ta barnatar da dukiyoyi har ma rasa rayuka da kuma  jihar Katsina. Har ma da wasu wurare a Arewa da wasu wurare ma a Nijeriya, domin da haka mu na yi ma ku jaje. Allah ya sawaka.

A karshen makon da ya wuce ’yan Boko Haram sun kai hari a sansani sojoji Nijeriya a jihar Yobe har an karkashe sojoji da Nijeriya da yawa. Mu na yiwa  sojoji Nijeriya da iyalinsu jaje da  mutuwan yan’uwansu.

Fadace-fadace da ke tsakanin Fulani da manoma ya kai ga rasa rayuka dubbanni a Arewa kadai. Kuma ’yan gudun hijira sun karu domin rashin mahalli na zama. Mu na rokon Allah Ubangiji ya kawo ma na cikakken zaman lafiya. Amin. Kungiyoyi masu dauke da makamai, kama masu garkuwa da mutane, domin neman kudin fansa da ke karkashe jama’a mu na rokon Allah ya kawo ma na saukin wannan bala’in.

Duk kashe-kashen da ke faruwa a jihohin 13 na Arewa, watau a Zamfara a  kowane rana ko mako, ya Allah ka tausauya wa talakawanka. Amin. A Jihar Kaduna daga bangaren birnin Gwari, Chikun, da kudancin Kaduna, Shiroro a jihar Neja, jihar Kwara, jihar Kogi, jihar Filato, jihar Adamawa, Nasarawa, Taraba, Borno, Yobe, Benue da wasu wurare  a Nijeriya. Mu na masu jaje wannan abubuwan da ke faruwa mu na kuma rokon Allah Ubangiji mai jin kai da rahama ya kuma yaye mana halin da mu ka sami kanmu. Mu na yiwa malaman addinin Kirista da na Musulunci jaje da kuma rokon Allah ya yaye ma na wannan bala’in. Muna yiwa sarakunanmu, gwamnoninmu, shugaban kasa, iyalin da abin ya shafe su a ko’ina a Nijeriya da uwa uba dukan talakawa da ke cikin zama zulumi a kowane lokaci a kuma ko’ina domin rashin tsaro.

Mu na kuma rokon shugabannin kananan hukumomi da gwamnonin jihohi har ga gwamnatin tarraya da dukkan jami’an tsaro da su nemi mafita tsakanin masu dauke da makamai a ko’ina a Nijeriya domin a sami zaman lafiya. Don Allah a sasanta, domin a sami dauwamammen zaman lafiya a Nijeriya.

Allah ya ba mu zaman lafiya.

Shalom!  Shalom!!  Shalom!!!

 

Exit mobile version