Muhimmancin Kalaman Soyayya

Yana da matukar mahimmanci masoya su iya furta kalamai masu dadi ba lallai iya kalmomin da aka saba furtawa ba ko kuma aka saba jinsu kamar: ina Sonki, ina kaunarki – a’a, iya magana ta yadda dadin hirarki ko hirarka kadai ya isa ka sace zuciyarta ko kuma ki sace zuciyarsa.

Kalamai masu dauke hankalin masoyi ko masoyiya ta yadda zai tattara hankalinsa gareki ko kuma ta tattara hankalinta gareka. Wasu sukan rasa abin cewa yayin da suke kiran masoyansu, wasu ma sukan fara da hirar kwallo ko ta biki, wanda a fannin soyayya masoya sun fi son zantuka masu dadi da hira me dadi irin ta masoya ba hirar gari ko kuma ta fim ba. Bayyana mata yadda soyayyarta take gareka, yaba kyawun halittarta ta yadda za ta ji tamkar babu wata wadda ka taba gani ‘ya mace face ita. Ban ce a yi karya ba, amma dai a yi kalaman da za su kwantar da zuciya ta yadda ko an tuno su yayin da ake cikin bacin rai za a ji sanyin rai.

Bari in dakata a nan don ina da abubuwan fada sosai sai dai wajen ya yi kadan na fayyace muku su, ku biyo ni sati me zuwa domin jin da me na tawo muku.

Kuna iya aiko da sakonin tambaya, shawara, labari ko kuma tsokaci a wancan lamba da take sama.

 

Exit mobile version