Muhimmancin Shan Ruwa Da Sassafe

Ruwa

Al’amarin shan ruwa musamman ma da sassafe kafin a samu cin abinci, wata hanya ce ta samun karuwar lafiya. Fara shan ruwa kafin cin komai da sassafe hakan na taimakawa wajen kare mu daga kamuwa da wasu cututtuka masu yawa, daga cikinsu akwai:

Ciwon kai da ciwon jiki da saisaita bugun zuciya da raguwar kiba da ciwon huhu da ciwon numfashi (Asthma) da tarin Shika da kyanda da ciwon koda da na bututun mafitsara da Amai  da gudawa da ciwon sikari da cushewar ciki da duk nau’ukan matsalar ido da na mafitsara da kuma rikicewar al’adar mata har ma da matsalar kunne da hanci da kuma makogwaro.

Ga yadda ake amfani da shi:

Da zarar ka farka da safe, kafin ka wanke bakinka da kuma yin asawaki ko burushi, sai ka sha ruwa kimanin kofin gilashi hudu (4) ko kuma 640 ml, daga nan kuma sai a wanke bakin amma kar da a zauna sannan kar da a ci ko shan komai har sai bayan tsawon minti arba’in da biyar.Daga nan kuma ana iya ci ko shan duk abincin da ake bukata hakan. Bayan an ci abincin rana da na dare, to kada a ci komai har na tsawon awanni biyu da daddare. Amma ga tsofaffi ko wadanda ba su da lafiya da ba za su iya shan kofin gilashi hudu na ruwan, wadannan suna iya farawa da ko da kadan ne, gwargwadon yadda za su iya, daga baya kuma sai su rika karawa har ya kai mizanin yadda  aka yi bayani da farko. Muddin aka yi amfani da wannan  shawarar, zata taimaka matukar gaske wajen bayar da kariya daga kamuwa da cututtuka masu yawan gaske sannan kuma da karin amfanuwa da abubuwan da ruwa ke ba gangar jiki.

Ga wadanda suke fama da cutar hawan jini, sai suyi amfani da shi tsari har na tsawon kwanaki talatin (30) ko kuma wata daya, su kuma wadanda suke da matsalar rashin iya cin isasshen abinci, za su aikata hakan, har na tsawon kwana goma (10) kawai.

Ciwon sikari shi kuma, ana yin irin wannan shan ruwa ne shi ma har na tsawon kwanaki talatin (30) Cushewar ciki da rashin narkewar abinci, ana yi ne tsawon kwanaki goma (10) kawai. Su kuma masu fama da cutar tarin TB Fuka (Shika), sai su yi irin wannan shan ruwa shi ma har na tsawon kwanaki talatin (30).

Wani abu kuma idan idan dai yadda ake bukata  ne, kamata yayi idan aka fara wannan shan ruwa a cigaba da yin hakan har na tsawon rayuwa, ba tare da wata tsayawa ba, domin cigaba da samun cikakkiyar lafiya da kwarin jiki.

Karuwar amfani da shan ruwa kafin cin komai yake sanadiyar kashe sinadarin gubar jiki. Da zarar mun sha ruwa, jikinmu kan wartsake musamman ma ta hanyar ba kayan cikinmu damar kasancewa cikin sauki, kuma sai ya koro duk wadansu sinadarai masu cutarwa ta hanyar fitar da su waje, shan ruwa kafin cin komai kan kammala aikin korar sinadaran na guba zuwa wajen jiki. Shan wadataccen ruwa na samar da karuwar sinadaran gina jiki da kuma samar da kwayoyin halittar jini. Yana  taimakawa jiki wurin narkar da abinci ga kuma saukakawa jikin wajen wahalar da yake sha lokaciin narkar da abinci da kimanin kashi 24, hakan kuma zai  matukar taimakawa maras lafiya musamman wadanda likita ya tsarawa abinda za su rika ci domin rage kiba.

Sakamakon wanke jiki da shan ruwa kafin cin wani abu hakan na taimakawa wajen rage sinadaran gubar jiki, wanda hakan ke taimakawa sassan jikinmu wajen narkar da abincin, bugu da kari kuma zai sa rashin jin yunwa, da kuma sha’awar cin abincin da sauri wanda shi ke taimako domin kare mu daga yin kiba da nauyi musamman ga masu dabi’ar ci sosai. Konewar zuciya sakamakon wanke jiki da shan ruwa kafin cin komai yake yi daga sinadaran gubar jiki, wanda hakan yake taimakawa sassan jikinmu wajen narkar da abinci.

Mukan ji zuciyarmu kamar ta kama da gobara wasu lokutan, hakan na faruwa ne a dalilin karancin sinadarin yawun (miyau) da ke taimakawa wurin narkar da abinci, shan ruwa kafin cin wani abu na taimakawa wajen samuwar wannan sinadarin da zai magance matsalar da kuma kimtsa jiki kafin karin kumallo.

Gyaran fata da shekin jiki: Karancin ruwa a jiki na haifar da tauyewa da kuma tsofar da mutum cikin sauri, kamar yadda wani binciken da aka yi ya nuna, shan ruwa cikin babban kofi kamar kimanin (500 ml) wannan na taimakawa sosai wurin gudanar jini, cikin sauki da kuma gyaran fata, ta rika sheki da kyalli tare da santsi. Karuwar gashi da sanya shi ya yi santsi. Rashin ruwa a jiki ba karamar illa ba ce ga jiki ba, samuwarsa kuwa na taimakawa wurin girma da kyan jiki ko akasin hakan.

Exit mobile version