Sabo Ahmad" />

Muhimmancin Shiga Mota A Tasha

Tashoshin mota dalilin da ya sa aka yi su bai wuce a kan tituna-tituna a samu rage cunkuson motoci wadanda za su iya kawo cikas, ga abubuwan hawa da kuma mutane masu tafiya a kasa ba, su ma suna samun sauki yadda za su yi tafiyarsu ba tare da  wata matsala ba. Ga dai direbobi da kuma motoci masu zuwa garuruwa daban-daban duk in da mutm ke da bukatar zuwa, wadanda kamar yadda aka samu ci gaba yanzu ana rubuta sunayen fasinjoji abin da aka fi sani da manifestor, da kuma garuruwan da za su tafi, bugu da kari kuma ga nambobin wadanda za a iya tuntuba koda a ce wani abu zai auku a kan hanyar su ta zuwa inda suka dosa. Babu wanda zai yi fatar wani abu ya faru, amma kuma Allah ai shi ne ke da al’amarin shi, shi kuma ya barma kan shi sanin hakan, saboda ai kowa kuma ya san kaddara ta riga fata. Kafin dai ita motar ta bar tashar  ana barin kwafe na bayanan dukkanin fasinjojin da suke cikin  motar tare kuma da shi suna direban,  da kuma  lambar motar da yake tukawa, akwai tikiti na shaidar nuna cewar shi fasinjan ya biya kudin  mota. Baya ga ma maganar shiga mota a tasha, har ila yau akwai bukatar duk fasinja wanda zai yi tafiya ya rika tafiya da wani abu, a matsayin sheda wanda za a ayi saurin gane shi da kuma daga inda ya taso, da kuma wurin da zai je, wannan  abu da nake magana bai wuce wani kati wanda ke nuna mutum ga sunan shi, wurin da yake yin aiki, ko na  gwamnati ne ,  ko kuma na kamfani mai zaman kan shi. Ga kuma sauran kungiyoyi na sana’oi daban daban  saboda yanzu duk an himmatu wajen yin wannan kati mai  nuna cewar ko wanene mutum da kuma abin da yake yi.

Wannan ba wani abin tashin hankali ba ne da har wasu fasinjoji za su rika nuna rashin ba da goyon baya a kansa tsarin da aka yi, wanda kuma an yi shi ne saboda a taimake ma su, ba kuma wani abu bane ake amsa daga gare su ba wanda ya danganci kudi bare suce ana takura masu, suna fa ne, da wurin da mutum zai je, sai kuma wani wanda za a iya tuntuba, ko dai ya rubuta da kan shi ko kuma da kanta, amma sai abin ya zama tashin hankali, har wasu ma su fara bata rai, bayan taimakon su ne ake son  yi, amma su kuma gani suke yi tamkar ana matsa masu ne.

Wannan jan aiki ne wanda kungiyar direbobi ta kasa  NURTW ta bullo da shi wanda kuma sauran kungiyoyi  ma daga baya kamar su NARTO da dai sauransu suka bullo  da nasu tsarin da . Dalilian da suka sa bullo da shi wannan tsarin shi ne yanzu al’amura sun canza ba kamar da ba, koda yake dama can ana samun hadurra akan hanyoyi, shi ya sa bullon da shi tsarin wanda za a yi saurin gane fasinja ko wanene shi, manufa sunan shi da kuma nambar wani na shi da za a iya tuntuba, koda wani abu ya kasance, a iya kiran danuwan sa a sanar da shi irin halin da yake ciki,  ko kuma wurin da hadarin ya auku. Idan danuwan yana da halin zuwa sai ya je saboda duk za ayi bayanin yadda za a same su. Idan kuma ta Allah ce ta kasance duk dai ba sai an samu wata matsala ba, wajen gano wadanda suka samu rauni ko kuma wadanda suka riga mu gidan gaskiya daga cikin fasinjojin saboda ita rayuwa ba ta da wani tabbas.

Bugu da kari kuma yanzu an samu bullar ‘yan fashi da makami wadanda wani lokaci sukan ma tsare motoci, su yi ma fasinjojin fashi, wani lokaci ma har kashe wasu daga cikinsu suke yi wasu kuma su samu nakasu wajen raunuka. Wannan abu na farko ke nan na biyun kuma yanzu akwai bullar wasu ‘yan ta’adda wadanda ake kira ‘’One chance’’, wato su, su nuna mota dama ta kusa cika, kai da kaga za ka iya shiga motar ta su a bakin titi kaim kadai ne suke jira,  su ma wani nau’i ne na barayi amma kuma suna fita  ce da suffar direbobi, amma kuma ba direbobin bane barayi ne su kuma ba a cikin tasha suke nasu lodin ba, a bakin titi ne suke yi. Ba kuma  a baka wani rasidi, ko kuma a rubuta sunanka ba abin da zai nuna kai matafiyi ne, saboda su dama suna da tasu manufar. Idan ma akwai tunani tun ma kafin motar taku ta tashi, kai ma ka san da akwai matsala ba kuma karama ba. Babban matsalar irin wadannan one chance  ita ce wasu ba suyin nisa da fara tafiya zasu fara nasu operation  na cin mutunci, da kuma tausayi, saboda kuwa idan da akwai tausayi tun farko ma, da ba zasu fara shiga ita harkar ba. Kai dai zaka tafi a matsayin matafiyi , amma ko an je tasha, ba za a samu wani bayanin kaba, saboda kuwa ai ba a cikin tasha ka shiga motar ba. Duk ma wani abinda ya same ki , ka, ku, su, ba za a san ko wanne irin hali ake ciki ba, sai dai ayi ta hasashe na watakila, ai ga abin da ya samu ko ma wanene , sai dai a yi ta karatun dankama.

Shi yasa da akwai bukatar wanda, wadda, wadanda, kai ko ma wanene idan dai ba mota yake da ita ba, ya kamata aje tasha a shiga mota, tafiya sannu sannun kwana nesa, suma tashoshin ai suna yi ma fasinjoji rangwame ga duk wanda ya bukata, ga kuma kwanciyar hankali tunda ai an san wurin da aka shiga motar, ko zuwa aka yi za a samu bayani koda ma an ji shiru ba wani labari.

Exit mobile version