Connect with us

BABBAN BANGO

Muhimmancin Taron FOCAC Ga Ci Gaban Alakar Sin Da Kasashen Afirka

Published

on

Daga ranar 3 zuwa 4 ga watan Satumban shekarar 2018 ne aka gudanar da taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC a takaice a nan birnin Beijing na kasar Sin.

An fara taron na FOCAC ne a birnin Beijing na kasar Sin a shekarar 2000, kuma taron shekarar 2018 shi ne taro na shida cikin jerin tarukan dandalin, bayan taron koli na dandalin da ya gudana a nahiyar Afirka a birnin Johannesg na kasar Afirka a shekarar 2015.

Tun lokacin da kasar Sin ta kulla dangantaka da kasashen Afirka, wannan dangantaka take ta bunkasa, abin da ya sa masu sharhi suka bayyana cewa, wannan dangantaka ta yi babban tasiri ga bangarorin biyu, duk da cewa, wasu kasashen yammacin duniya na yi wa wannan kyakkyawar dangantaka bahaguwar fahimta.

Sai dai duk da wannan rashin fahimta da irin wadannan kasashen ke yi wa wannan dangantaka dake tsakanin Sin da Afirka, shugabannin kasar Sin sun jaddada cewa, babban tushen dake tsakanin Sin da Afirka ba zai canja ba.

Haka kuma duk da bambancin ci gaba tattalin arziki gami da rayuwar al’umma dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, aminai kasashen biyu suna da ra’ayi iri daya wajen neman bunkasuwa da samun wadata da karfi tare.

Alkaluma sun nuna irin tallafi da moriyar da kasashen Afirka suka samu daga wannan dangantaka a bangarori daban-daban kamar su al’adu, ilmi, makamashi, sufuri, tattalin arziki, kiwon lafiya, da dai sauransu. Na baya-bayan nan shi ne shirye-shiryen da kasar Sin ta tsara samar wa nahiyar Afirka da nufin raya masana’antu da bangaren aikin gonanta yayin taron na shekarar 2015. Kuma kasar Sin ta cika alkawarinta na samar da kudin tallafi na dala biliyan 60 nan shekaru 3 masu zuwa.

Shugaban kasar Sin Di Jinping ya ce, saboda yadda tarihinsu ya kusan zama iri daya, da kuma aikin da suka sanya a gaba, kasar Sin da kasashen Afirka sun gano wata hanyar musamman ta hadin gwiwar samun moriyar juna. Har kullum kasar Sin na hada kai da kasashen Afirka bisa ka’idar sahihanci da gaskiya, da akidar “cimma muradu da kuma martaba ka’idoji.

A yayin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC da aka gudanar a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu a shekarar 2015, kasar Sin ta gabatar da manyan shirye-shirye goma na hadin gwiwar Sin da Afirka. Kawo yanzu kuma, an gama gina layukan dogo da na mota da dama, baya ga wasu da har yanzu ake kan ginawa. Baya ga haka, sassan biyu na aiwatar da hadin gwiwa a fannonin kimiyya da ilmi, da kiwon lafiya, da saukaka fatara da sauransu. Kasar ta kuma cika alkawarinta na samar da kudin tallafi na dala biliyan 60.

Al’ummar Sin da kasashen Afirka ne suka fi kowa sani game da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashensu. Har kullum Sin na ba da muhimmanci ga marudun al’ummar Sin da kasashen Afirka, kuma tana kokarin zurfafa hadin gwiwar sassan biyu, domin cimma moriyar al’ummarsu. Kasar Sin na son hada kai da kasashen duniya wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a nahiyar Afirka. Kasar Sin na maraba da dukkanin abubuwan da za su yi amfani kasashen Afirka.

A wannan karo ma yayin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a birnin Beijing, kasar Sin ta gabatar da sabbin matakan raya alaka da kasashen Afirka guda 8 da ake fatan aiwatar da su cikin shekaru uku masu zuwa da ma nan gaba, wadanda suka shafi, raya masana’antu,samar da kayayyakin more rayuwa, aikin gona, saukaka harkokin cinikayya da kare muhalli da sauransu.

A game da saukaka harkokin cinikayya, kasar Sin ta yanke shawarar kara shigo da kayayyaki daga kasashen Afirka, musamman ma kayayyaki da ba su shafi albarkatun kasa ba, kuma tana goyon bayan kasashen na Afirka, wajen halartar bikin baje kolin kasa da kasa a kasar Sin, tare da yafe wa kasashen Afirka da suka fi fama da rashin ci gaba kudin halartar bikin. Tana kuma mara wa kasashen Afirka baya wajen gina yankin ciniki cikin ‘yanci, kuma za ta ci gaba da tattaunawa tare da kasashe da shiyyoyi na nahiyar Afirka, wadanda ke da niyyar gudanar da ciniki cikin ‘yanci.

Saboda muhimmancin wannan dangantaka dake tsakanin bangarorin biyu, ya sa aka kafa wannan dandali, abin dake kara nuna karfafa wannan dangantaka mai tarin alheri ga sassan biyu.

Bugu da kari, shugaban kasar Sin Di Jinping ya yi alkawarin kafa wasu ma’aikatun Labun guda 10 don horar da matasan kasashen Afirka sana’o’i. Ma’aikatun Luban wani shiri ne na samar da horon sana’o’in da kasar Sin ta kafa a kasashen ketare, kuma kawo yanzu Sin ta kafa irin wadannan ma’aikatu a kasashen Thailand da Pakistan.

Wani muhimmin mataki na kara zurfafa alakar Sin da Afirka ita ce sabuwar manufar diflomasiya a fannoni biyar da shugaba Di Jinping ya gabatar, na farko, kasar Sin ba za ta kawo cikas ga kokarin da kasashen Afirka suke yi domin samun ci gaba bisa hakikanin yanayin da suke ciki ba. Na biyu, ba za ta tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba. Na uku, ba za ta yada manufofinta a kasashen Afirka ba. Na hudu, ba za ta gindaya wani sharadin siyasa yayin da take samar wa kasashen Afirka tallafi ba. Na biyar, ba za ta nemi samun moriyar siyasa yayin da take zuba jari a kasashen Afirka ba.

Kasar Sin na goyon bayan kafa cibiyar hadin gwiwar Sin da Afirka kan kirkire-kirkire a yunkurin karfafa hadin gwiwar kirkire-kirkire a tsakanin matasa, kuma za ta bullo da wani shirin horar da wasu mutane 1000 daga kasashen Afirka wadanda suka kware a fannoni daban daban, tare kuma da samar da tallafin kudin karatu ga matasan Afirka dubu 50 da ma horar da matasan kasashen Afirka dubu 50, baya ga haka, za ta kuma gayyaci matasan kasashen Afirka dubu biyu zuwa kasar Sin a matsayin shiri na musaya.

Yanzu haka nahiyar Afirka ta kasance wani muhimmin sashe na shawarar “Ziri daya da hanya daya” da shugaba Di Jinpjng ya gabatar, bayan ‘yan shekarun da suka gabata, ta kasance nahiyar dake cimma karin nasarori wajen shawarar “Ziri daya da hanya daya”. Ga misali, layin dogo daga Addis Ababa zuwa Djibouti da ya hade kasashen Habasha da Djibouti, da layin dogo daga birnin Mombasa zuwa birnin Nairobi, babban birnin kasar Kenya da tashar ruwa Mombasa ta kasar, da dai sauransu, wadanda kasar Sin ta dauki nauyin gina su, dukkansu sun soma aiki.

Taron kolin FOCAC na Beijing ya sake hade shugabannin Sin da kasashen Afirka bayan tsawon shekaru 12, kuma a sakamakon shigar da kasashen Gambia da Sao Tome and Principe da kuma Burkina Faso dandalin, a yanzu yawan kasashen Afirka mambobin dandali ya kai 53.

Masu fashin baki na cewa, muddin ana bukatar cin gajiyar wannan dangantaka yadda ya kamata, wajibi ne bangarori biyu su ci gaba da mutunta alkawuran da suka dauka, mutunta juna, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu a bangarori gwamnatoci da al’ummomin kasashen biyu. (Marubuci: Ibrahim Yaya, ma’aikacin sashen Hausa na CRI).

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: