Yarda na nufin amincewa da bambamcin halayya da ke tsakanin juna. A cikin zamantakewa na aure, yarda da juna yana nufin sadaukarwa ga abokin zama tare da girmama juna a zahirance da sauraron juna lokacin da ake bukatar tattaunawa. Ba a bukatar boye wa abokin zama abubuwan da suke damun juna a cikin auratayya.
Dole ne a samu girmama juna a cikin zamantakewar aure idan ana so a yi zama mai daurewa tare da karfafa wa juna kwarin gwiwa. A cikin zamantakewar aure bai zama dole sai an bayyana wa juna duk abin da ya shigo cikin zuciya. Zai iya kasancewa ana da wani abu na kashin kai wanda z aka boye a cikin zuciyarka ba sai ka fada wa abokin zama ba.
Yarda da juna ba wai yana nufin dole sai an yi musayan kayayyaki da juna, kamar irin su wayar salula da kwafuta da dai sauran su. Za a iya musayar wadannan kayayyaki a lokacin da aka samu lamari na gaggawa. Amma idan ba haka ba, ba a bukatar duba wa juna wadannan abubuwa domin suna haddasa rikici a cikin zamantakewa.
Idan aka samu rashin jituwa a tsakani, akwai bukatar a dawo da aminci a cikin zamantakewa. A nan ga wasu hanyoyi da ya kamata a bi wata kila za su iya aiki cikin gaggawa ko kuma nan gaba kadan.
A kauce wa yawan yin karya cikin zamantakewar aure. Domin yin haka yana kawo rashin yadda da juna musamman ma lokacin da aka sami sabani. Idan ma’aurata suka yi matukar mahimtar yadda za su yafewa juna da yarda da juna lokacin da suka sami sabani, to za su yi matukar yin zamantakewar aure ne ban sha’awa wanda mutane za su dunga kwatance da su.
Ka yi kokarin yafe wa kanka kafin ka yafe wa sauran mutane, sannan ka yi kokarin yarda da kanka kafin ka yarda da sauran mutane, wannan yana da matukar mahimmanci a cikin zamantakewa. Idan ka yi kokarin yin haka, to za ka sami sauki wajen gudanar da zamantakewa.
Muna fatan masu karatu za su bi wadannan shawarwari sau da kasa domin gina zamantakewarsu ta aure. Allahi ya bayar da iko.