Bai zama sabon labari ba, ko wata sabuwar bidi’a, yin gwaje gwaje-gwaje don tabbatar da lafiyar wadanda ke shirin yin aure. Birni da kauye yanzu wannan tsari ya zama gama-gari, ko da yake ba zan ce ko’ina ne tabbas ake hakan ba. Amma lallai jama’a da dama, malamai da kungiyoyin addini sun karbi wannan tsari saboda muhimmancin sa, ga tsaron lafiyar ma’aurata da zuriyar da za a samu.
Muhimmai daga cikin gwaje-gwajen da ake yi su ne na sanin nau’in kwayar halitta wato gwajin ‘Genotype’, inda ake kokarin gane ko kwayoyin halittar jikin ma’auratan ya dace da samun ‘ya’ya masu koshin lafiya. Sai kuma gwajin cutar HIB, wato cuta mai karya garkuwar jiki, wacce daga cikin hanyoyin da ake iya dauka har da ta hanyar jima’i tsakanin ma’aurata da sauran su.
Ana karfafa yin wadannan gwaje-gwaje ne, domin cika ka’idar tabbatar da ingancin lafiyar ma’aurata kafin cika sharuddan yin aure, da kuma samar wa yaran da za a haifa ta dalilin wannan aure idan Allah ya yarda, za su rayu cikin ingantacciyar lafiya da kuzari.
Da dama jama’a sun fi gane wa muhimmancin gwajin cutar HIB, saboda yadda masana kiwon lafiya suke ta kokarin wayar da kai, a asibitoci, gidajen rediyo da sauran kafofin watsa labarai, domin ganar da jama’a illolin wannan cuta da hadarinta ga lafiyar jikin dan Adam, ta yadda aka samu wayewa da fahimta, birni da kauye. Matsalar da aka fi samu ita ce a bangaren gwajin nau’in kwayar halittar jini, wanda ke gadar wa ‘ya’yan da za a haifa cutar Sankarar Jini da aka fi sani da Sikila, idan ba a dace da jituwar kwayoyin jinin ba.
Likitoci suna cewa, idan ma’aurata masu nau’ikan halittar jini mai lakabin AA da AA, ko AA da AS, ko kuma AA da AC suka yi aure to, yaran su sun kubuta daga cutar Sankarar Jini. Amma idan kwayoyin halittar su AS da AS ne, ko AS da SS, ko SS da AC, ko kuma SS da CC ne, ba zai yiwu su yi aure ba sam, don kuwa kwayoyin halittar su ba za su jitu da juna ba, za su iya haifar yara masu Sikila, wato Sankarar Jini, ko da kuwa ba dukkan su.
Cutar Sankarar Jini kuwa cuta ce mai matukar hadari ga lafiyar dan Adam, wacce ke hana yara kuzari ko girma kamar sauran yara, kuma suna rayuwa cikin yawan laulayi da kwambarewar gabobin jiki. Kuma akasarinsu ma ba sa tsawon rai. Kawo yanzu dai ba a gano takamaimen maganin wannan mugunyar cuta ba. Sai dai kokari da masana sirrin harhada magunguna ke yi na gano makarin wannan cuta. Shi ya sa likitoci ke ba da shawarar a daina gaggawar hada auren masoya mace da namiji da ke sha’awar aure, har sai an tantance nau’in kwayar halittar jinin su ta hanyar yin gwaji.
Saboda kalubalen da ake fuskanta wajen dakatar da auren da ake gab da daura shi bayan a gano rashin jituwar jinin ya kamata a ce tun lokacin da iyaye suka tabbatar da wanda za su bai wa ‘yarsu, shi ma kuma namijin iyayen sa suka tambayar masa matar da yake so har suka hadu da iyayen ta aka tattauna tun a matakin farko to, tun kafin a kai ga matakin BADA SADAKI ko DAURA AURE a je a yi wannan gwajin, saboda babu wasu iyayen da za su ji dadi a ce sai an tara mutane an hadu don daurin aure a ce a fasa, saboda sakamakon da gwajin ya bayar.
Shawara dai ga iyaye a nan ita ce tun kafin tafiya ta yi nisa yaransu su shaku da juna, har rabuwar su ta iya zama da matsala to, a yi wadannan gwaje gwajen, don sanin makamar alakar su. Kada a bari sai abin ya kai wani matsayi da raba su zai zama da wahala, ko kuma ta kai matakin da za su ce tun da ba za su samu damar yin aure ba to, za su je su aikata abin da zai jefa su cikin fushin ubangiji. Ko kuma su masoyan su samu kansu cikin wata matsala da za su jefa rayuwar su cikin tsaka mai wuya!
Allah ya sa wannan fadakarwa ta amfanar da mu, mu kiyaye kawunan mu da iyalan mu daga fadawa cikin wata rayuwa mawuyaciya.
Rabi’atu Ahmad Mu’azu Jos, ita ce Edita ta Arewa Media Writers a karamar hukumar Jos ta Arewa, a Jihar Filato