Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Mujallar The Economist: Masu Zuba Jari Na Da Kyakkyawan Fata Ga Makomar Tattalin Arzikin Sin

Published

on

Kwanan baya, mujallar The Economist ta kasar Burtaniya ta fitar da rahoton dake cewa, kasar Sin na da cikakken jerin sana’o’i, da kyautatuwar manyan ababen more rayuwa, da babbar kasuwa. Bayan bullar annobar COVID-19, an gano cewa, a matsayinta na kasuwar duniya, masu zuba jari na ci gaba da rike da kyakkyawan fata kan makomar tattalin arzikin kasar ta Sin a nan gaba.

Rahoton ya ce nasarar da aka cimma wajen shirya bikin baje kolin hada hadar cinikayya na Guangzhou ta intanet, ya nuna karfin kasar Sin a fannin samar da kayayyaki. Rahoton ya nuna cewa, cikakkun nau’o’in masana’antu na daya daga cikin bangarorin da kasar Sin ta nuna fifiko a fannin kere-kere. A yayin da ake dakile annobar, yadda kasar Sin ke samar da marufan baki da hanci, ya nuna karfinta a fannin.
Wani bangare na daban da kasar Sin ke da fifiko a fannin kere-kere, shi ne tana da babbar kasuwa. Ganin hakan ne ma ya sa, wasu manyan kamfanoni na kasashen ketare kamar su kamfanin BASF na kasar Jamus, da kamfanin Tesla na kasar Amurka da dai sauransu, suka zuba jari a kasar Sin.
Rahoton da aka bayar ya nuna cewa, bisa yanayin da ake ciki, kasar Sin na samun yawan kaso a fannin ci gaban tattalin arzikin duniya, kuma masu jarin waje za su ci gaba da nuna sha’awarsu wajen zuba jari a kasar. Masu zuba jari na kasashen ketare suna da kyakkyawan fata game da bukatun masu sayen kaya na kasar Sin, kuma bisa sassaucin kayyade masu jarin waje a fannin mallakar hannayen jari cikin kamfanonin da suka zuba jari, suna kara gudanar da ayyukansu a kasar Sin. (Mai Fassarawa: Bilkisu Xin)
Advertisement

labarai