Mukabala: Ganduje Zai Gurfanar Da Sheikh Abduljabbar Gaban Malamai

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Bayan muhimmiyar ganawar da Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya gudanar da manyan malaman Musulunci a bangarori daban-daban kan bukatar tattaunawa tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da sauran malaman da su ke jayyayar ilimi da shi, gwamnan ya amince da gudanar da tattaunawar mukabala a tsakanin bangarorin biyu nan da ‘yan kwanaki kadan, kamar yadda Daraktan Yada Labaran Gwamnan Jihar, Malam Abba Anwar, ya shaida wa LEADERSHIP A YAU a cikin wata sanarwa jiya a birnin Kano.

Akwai fitattun malamai daga kowane bangare da za su halarci tattaunawar, wanda Kwamishinan Ma’aikatar Shari’a, Dakta Muhammad Tahar Adam, Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Kano, Dakta Ali Haruna Makada, da kuma tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Kano Malam Salihu Sagir Takai da sauransu.

Bayan ganawar an samu amincewar gwamna, ya Amince da tattaunawar tsakanin bangarorin biyu, domin amsa bukatar da Abduljabbar ya yi kan bukatar a yi masa adalci.

An Amince cewar, dukkan bangarorin zasu samu wakilci a lokacin taron tattaunawar ya yinda za’a gayyaci wasu fitattun Malamai daga wajen Jihar Kano, domin halartar tattaunawar.

Gwamnati za ta samar da wurin da za a gudanar da taron tattaunawar tare da samar da cikakken tsaro a lokacin tattaunawar da kuma bayan kammala shi.

Wadanda za su kasance alokacin tattaunawar an basu mako biyu domin kammala hujjojinsu da zasu gabatar a lokacin tattaunawar da Abduljabbar ya jima yana bukatar aiwatarwa.

Haka kuma Gwamna Ganduje ya amince da gudanar da tattaunawar ta hanyar sauraro kai tsaye ta gidajen radiyo na ciki fana waje. Don haka sai ya bukaci jama’a da su kkwantar da hankalinsu tare da zaman lafiya alokacin gudanar da tattaunawar, haka ma bayanta.

Exit mobile version