Mukaddashin Shugaban NIS Ya Ziyarci Filin Jiragen Saman Abuja Da Legas Domin Inganta Aiki

Shugaban NIS

Daga Yusuf Shu’aibu,

 

A ranar 15 ga watan Nuwambar, 2021, Mukaddashin Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice, Ag.CGI, Isah Jere Idris ya kai ziyarar aiki a filin jiragen sama na Abuja da na Legas, domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan tabarun inganta ayyuka a dukkanin filin jiragen saman da ke kasar nan.

Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar 15 ga watan Nuwambar, 2021, ta hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da shige da fice, Amos OKPU, ta bayyana cewa, mukaddashin shugaban hukumar ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 10: 15, inda ya fadu da wani bangare na jami’an da ke gudanar da aiki a filin jirgin da sauran hukumomin.

 

Ya bayyana cewa wannan ziyarar tasa tana da matukar muhimmanci bisa rahotannin da ya samu na rashin kwarewa ga wasu jami’an hukumar da ke gudanar da aiki a filin jirgin saman. Ya kara da cewa yana da mutukar muhimmanci ya hadu da dukkan masu ruwa da tsaki da ke filin jiragen saman, domin tattauna yadda za a hada hannu da karfe wajen bullo da sababbin dubaru da za su kawar da wasu munanan dabu’u da jami’an filin jirgin sama suke gudanarwa wadanda za su iya zubar da kiman kasar nan da kuma hana baki shigowa kasar.

 

Mukaddashin shugaban hukumar ya bukaci hadin kai da sauran shugabannin hukumomin da ke gudanar da aiki a tashoshin jiragen sama domin yakir jami’an da aka kama da hannu wajen gudanar da dabi’un da dokokin kasa ba su amince da su ba. Ya kuma shawarci fasinjoji da kar su amince da duk wasu hanyoyin cin hanci da rashawa tare da tona asirin jami’an da ke nuna dabi’un rashin kwarewa a tashoshin jiragen sama. Fasinjojin za su iya kai korafinsu ta daya daga cikin wadannan hanyoyin sadarwa kamar haka: wayar salula mai lamba kamar haka +2348021819988 da kafar sada zumunta ta Facebook ko ta Tuwita ta ………@nigimmigration da kuma adireshin emal ta nis.pro@immigration.gob.ng/nis.serbicom@nigeriaimmigration.gob.ng

Da yake mayar da jawabi, babban jami’i da ke kula da filin jirgin sama, Mahmud Liman Sani ya amince da matakin da mukaddashin ya dauka, haka kuma ya bayyana cewa hukumar da ke kula ta tasoshin filiyen jirgin saman Nijeriya (FAAN), za ta yi duk mai yuwuwa wajen kokarin tsaftace filayen jirgin sama daga jami’an masu nuna rashin da’a. Ya kara da cewa a kwanakin da suka gabata ana samun irin wannan lamari, amma a yanzu da taimakon dukkan shugabannin hukumomi da ke filin jiragen sama an magance wannan matsala gaba daya.

A nasa jawabin, babban jami’in hukumar kula da shige da fice a filin jirgin saman, CIS Babali Mohammed ya sha alwashin inganta ayyukan jami’ansa domin bai wa mutane ingantaccen aiki a filin jirgin saman.

Jim kadan bayan da mukadashin hukumar ya bar filin jirgin saman Abuja ya garzaya zuwa filin jirgin saman Legas, inda ya hadu irin wadannan jami’ain hukumar a filin jirgin saman. Ya jaddada kiransa ga sauran hukumomin da ke filin jirgin wajen inganta aiki domin ya dace da bukatun matafiya da ke shigowa kasar nan.

Da take yi wa mukaddashin maraba, shugabar hukumar kula da tasoshin jiragen sama (FAAN) ta yankin Kudu maso Yamma, Misis Bictoria Shinaba ta nuna farincinta da wannan ziyara tare da bayyana cewa sun hada hannu da dukkan hukumomi da ke filin jirgin saman domin tsaftace filin jirgin saman kasar nan daga gurbatattun dabi’un da a amince da su ba. Ta bayyana cewa sun gyara dukkan kamarori na sirri da ke filin jirgin saman Legas, ta kuma bukaci fasinjoji da su dunga kai rahoton duk wani jami’in da ya kasa gudanar da aikinsa yadda ya kamata ga hukumomin filin jirgin saman domindaukan mataki. Ta kuma yi kira ga hukumomi da ke filin jirgin saman da su dunga kulawa da ma’aikatansu wajen tabbatar da an nisanta jami’an daga zargin da ake musu na gudanar da dabi’u marasa kyau.

Tun da farko dai, mataimakiyar shugaban hukumar kula da shige da fice da ke kula da Zone “A” a Legas, ACG Oluremi Talabi ta yaba wa mukaddashin shugaban hukumar wajen bata lokaci zuwa Jihar Legas, saboda tattaunawa da jami’an hukumar da sauran hukumomi da ke filin jirgin saman, domin magance rashin ingantuwar aiki. Ta kara da cewa sako ya isa wajen da ake bukata tare da tabbatar jami’an sun bai wa dukkan fasinjoji ingantaccen aiki.

Exit mobile version