Connect with us

MU KOYI ADDINI

Mukaddima A Kan Azumi Da Hukunce-Hukuncensa

Published

on

 Assalamu’alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Wannan karatu ne a kan azumi kuma ga kadan daga cikin abin lura

 

 • Azumin watan ramadana farilla ne, yana daga cikin shikashikan musuluncin nan biyar

 

 • Wanda yayi niyyarsu tun acikin daren farko na ramadana, niyyar nan guda ta wadatar domin azumin watan ramadana dukansu

 

 • Idan mace ta shafa tozali tun gabanin alfijir, ko kuma mutum ya saka magani a cikin hancinsa, to ko maganin nan ya gangaro ga makogaro da rana azumi bai karye ba.

 

 • Idan kuwa ya karya shi ne da gangan, ko kuwa ya ki daukarsa bada wani uzuri ba, to zai rama shi ta kowane hali, sannan kuma ya kara da yin kaffara.

 

 • An halatta wa matafiyi, tafiya irin wadda ta hallata a gajarta sallah dominta, ya sha azumi, amma yayi ramuwa.

 

 • Mai  itikafi ba zai fita masallaci don gai da marasa lafiya ba, sai idan dayan iyayensan ne. Kuma ba zai fita don sallah a kan mamaci ba, ko don yin ciniki ba.

 

Mun Fara Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai, Dukkan Yabo Da Godiya Sun Tabbata Ga Allah Ubangijin Talikai, Tsira Da Amincin Allah Su Kara Tabbata Akan Shugabanmu Annabi Muhammad, Da Mutanen Gidansa, Da Iyalansa, Da Sahabbansa Baki Daya.

 

Azumi

Azumi shi ne kamewa daga dukkan abin da ciki da farji ko zakari suke sha’awarsa, tun daga alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin ibada.

Azumin watan ramadana farillane, yana daga cikin shikashikan musulunci guda biyar.

Tabbatar Tsayuwar Wata

Tsayuwar watan ramadana yana tabbata da samuwar daya daga cikin abubuwan nan biyu da zamu ambata;

Ganin sabon watan ramadan da ido, a ranar da sha’aban ya cika kwana ashirin da tara. To, idan mutum biyu adalai suka ga wata da  idanunsu, kama azumi ya wajaba ga dukan wanda ya sami labarin ganin wata. Adali shine wanda baya aikata manya zunubai Kuma yana kokari ga barin kananan zunubai da galibinsu.

Haka kuma kama azumi yana wajaba idan taron mutane da yawa wadanda ba adilai ba suka ce sun ga wata, alhali kuma don yawansu har baya yiwuwa a ce ko sun hada kai ne don su fadi karya. Amma idan mutum guda daya ne yaga wata, ba za’a kama azumi domin ganinsa shi kadai ba koda kuwa yafi mutanen duniya gaskiya da adalci. Amma shi wanda yaga wata ko da ba adali bane wajibi ne akansa ya dauki azumi tare dashi da iyalansa kadai, sauran mutane kuwa ba ruwansu.

Kuma wajibi ne akan wanda duk yaga wata ko da fasiki ne, yaje gun sarki ko shugabannin addini na garinsu ya sanar.

Idan an ga wata a wata kasa mai nisa can gabas, idan mutanen wata kasa ta yamma dasu suka sami labari daga garesu, a wani kauli na malamai ya halatta su dauki azumi tare dasu, a wani kauli kuma bai halatta ba sai dai idan duk malamai sunyi ittifa’i cewa idan tsakaninsu akwai nisa kwarai bai halatta suyi koyi dasu ba. Kamar tsakanin indiya da spain.

Dalili na biyu wanda zai tabbatar da tsayuwar watan ramadana shine cikar watan sha’aban kwana talatin cif. To, ko da ba’aga watan ramadana ba sai ayi azumi hakan.

Dalilin da aka bi don tabbar da tsayuwar watan ramadan sune kuma za’ayi aiki dasu don tabbatar da tsayuwar watan shawwal. Wato watan karamar sallah.

Sharrudan Wajabcin  Azumi Da Ingancinsa

Sharrudansa Bakwai Ne 7;

 1. Niyya; Wajibi ne mutum ya yi niyya ya ce; Na yi niyyar yin azumin watan ramadana, farilla. Tun daga faduwar rana har zuwa fitowar alfijir duk lokaci ne na yin niyya. Amma ana fadan hakane acikin zuciya.

Wanda yayi niyyarsa tun a cikin daren farko na ramadana, niyyan nan guda ta wadatar domin azumin watan ramadana har yagama dukansa. Amma da sharadin kwanakin azuminsa su bi juna, basu yanke ba. Idan ko da kwana daya ne ya baci, ko kuma bai saudi azumi a cikinsa ba don rashin lafiya, ko tafiya, ko haila ko jinin biki, to wajibi ne ya sake wata sabuwar niyya domin ragowar kwanakin ramadana. Ya hallata ga wanda yayi niyya tun da magriba akan ya ci, ya sha, yayi jima’i da matarsa har zuwa alfijir. Wanda bai yi niyya ba tun daren farko naganin wata to bashi da azumi.

 1. Tsarki Daga Jinin Haila Ko Jinin Biki;

Mace mai haila ko jinin biki bazatayi azumi ba, kuma ba zatayi salla ba. Amma zata rama dukan azumi da ta sha, ban da sallah. Ba zata rama sallah ba. ya wajaba ga mace mai haila ko jinin biki ta duba farjinta da yar auduga, ko farin kyalle a kusan fitowar alfijir, don ta gani ko azumin gobe zai wajaba akanta, zatayi hakane saboda tagane ko jinin ya tsaya.

 1. Hankali;

Babu azumi akan mahaukaci, kuma bai inganta ba, amma zai rama dukan azumin daya sha bayan warkewarsa.

 1. Balaga;

Azumi bai wajaba akan yaro ko yarinya wadanda basu balaga ba.

 1. Musulunci;

Babu azumi akan kafiri.

 1. Samun Iko; Azumi bai wajaba ba akan wanda baya iya yinsa domin ciwon kishirwa ko ciwon yunwa Ko don tsufa tukuf.
 2. Barin Yin Jima’i Ko Fitar Da Maniyyi, Ko Maziyyi Da Rana, Da Barin Shigar Da Wani Abu A Cikin Ciki Da Rana;  wanda yayi daya daga cikin wadannan babu azuminsa. Mutum ko da tsakuwa ce ya hadiye har ta kai ciki, azuminsa ya karye. Idan kuwa abu ruwa-ruwa ne, da ya kai ga makogoro, shikenan azumi ya karye don baya yiwuwa ya maido shi baya. Kofofin jiki wadanda idan wani abu ya shiga ta cikinsu har ya kai ciki azumi zai karye shidane kawai. Sune Baki, hanci, idanu, kunnuwa, dubura da farjin mace. Dura magani ko wani abu ta kofar zakari ko ta wani kurji mai zurfi daura da ciki ba zai karya azumi ba(Allura).

Haka kuma idan mace ta shafa tozali tun gabanin alfijir ko kuma mutum ya saka magani a cikin hancinsa, to, ko maganin ya gangaro ga makogoro da rana, azumi bai karye ba. Abin da dai aka hana shine aikata dayan wadannan bayan fitowar alfijir, wannan kam azumi zai karye idan sun gangaro ga makogwaro.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: