Daga Muhammad A. Abubakar
MATSAYIN MAKARANTA A CIKIN TARBIYYA
Makaranta ita ce wuri na biyu da yara ke samun tarbiyyyarsu, saboda haka tana da babban matsayi a cikin rayuwarsu (rayuwar yaro). Domin a makaranta ne yara sukan san girman Ubangijinsu da girman Manzonsa (s.a.w) da girman mahaifansu da girman Malamansu da sauran mutane baki daya. Kuma a makaranta ne yara ke koyon rubutu da karatu. Shi kuma amfanin koyon karatu shi ne yaro ya fadada tunanin sa akan al’amura daban-daban. Bayan haka makaranta wuri ne da ake koyon al’adu iri-iri daga Malamai da kuma su kansu yaran a tsakanin junansu. Makaranta kuma wani wuri n a saka tunani da samar da alkiblar rayuwa ga dalibai.
MAKARKATA
DAIDAITUWAR TARBIYYAR GIDA DA MAKARANTA
Dole ne a samu daidaito da karfafan juna a tsakanin tarbiyyar da yaro ke samu a tsakanin gida da makaranta, me yasa ake so a samu daidaito a tsakanin biyun nan? Dalili kuwa shi ne; idan abin da makaranta ke koyarwa yana warware kyakkyawan tarbiyyan da yaro ke samu a gida ne, to makaranta a nan ta zamo ‘Makarkata’. Haka nan kuma idan gida ne ke warware kyakkyawan tarbiyyar da makaranta ke koyarwa, a nan gida ta zamo mai karkatarwa. To me ye abin yi? Yawwa! Abin bukata a wurin iyaye shi ne; samun taimakon makaranta a kan yaro, kan kyakkyawan abubuwan da ake koya wa yaro. Ka ga kenan lazim ne (abin bukata ne) ya zama iyaye su sanya yaro a makarantar da za ta taimaka masa (shi yaron ko yarinyar) akan irin akidar da ake so ya rayu akai ko ta rayu akai.
KULA DA MAKARANTAR YARO
Wajibi ne Uba (Mahaifi) ya tsaya a matsayinsa, ya yi nazari kuma ya kula da makarantar da yaransa suke yi saboda makaranta wurin koyon alheri ne, idan makarantar ta kasance mai kyau ce. Idan kuma makarantar ta zamo maras kyau, to, wuri ne na koyon sharri. Duk abin da Uba (Mahaifi) ya fahimta dangane da makarantar yaro, shi ne zai sa shi, ya kuma karfafe shi akai ya fahimci ko ya canza masa wata makarantar ko kuma ya bar shi a wanda ya saka shi, duk zai yi haka ne kuwa saboda kyautatuwar tarbiyyar dansa. Makaranta na da tasiri kwarai da gaske akan duk wanda ya shige ta (na san me karatu zai yarda dani akan haka don ko ba komai na taka wadannan matsayi na shiga makaranta). Alal misali, za ku ga iyaye bana kwarai ba, amma saboda ingancin makarantar da suka sanya dansu a ciki, sai wannan dan nasu ya gyaru ya zamo mutumin kirki. Haka nan kuma za ku ga iyaye mutanen kirki ne, amma dansu ya lalace saboda tasirin makarantar da suka sanya dansu a ciki.
HANYA MA MAKARANTACE
Hanyar da yara ke bi domin tafiya zuwa makaranta ita ma makaranta ce. Eh, haka ne makaranta ce. A bisa ka’idan na matakan tarbiyya na kwarai, ba a son yaro ya rika tafiya makaranta da kafarsa idan ya kasance karamin yaro ne, ko idan makarantar a nesa take da gidan su. An fi so a dauki yaro a abin hawa akai shi makarantar domin a raba shi da miyagun yara ko wani mummunan abin da zai iya koya a tsakanin gida da makaranta. Akwai bambanci mai girma wajen kyautatuwar tarbiyyar yaron da ake kai shi makaranta akan abin hawa, idan kuma an tashi aje a dauko shi. Shi wanda ake kai shi a dauko shi, an san irin abin da yake gani a hanyar makarantar, kuma a wasu lokuta ma ya kan yi tambaya ko wata magana wanda za ta sa a ba shi amsa mai kyau saboda inganta tarbiyyarsa. Amma yaron da ke tafiya makaranta da kafa ba a da tabbacin abubuwan da zai rika gamuwa da su akan hanyar makaranta. Wadanda duk suna da tasiri akan rayuwarsa.
SHIN HAKKIN MAKARANTA CE TA SAMAR DA MOTAR DAUKAR DALIBAI?
Dangane da iyayen da ba su da halin kaiwa da komowa da ‘ya’yansu zuwa makaranta akan abin hawa kuwa, ya hau kan hukumar makaranta ta samar da motar da za ta rika dauko yara kuma tana mai da su gidajensu. Duk za ta yi haka ne kuwa saboda kyautatuwar tarbiyyarsu, kuma yin hakan mai sauki ne idan makarantar na da isassun kudade. Sai su sayi mota ‘bus’ ko dai wata motar da zata iya diban dalibai na wasu adadi masu yawa. Yaran kuma su rika biya duk wata ko sati ko kuma a kowanne zangon karatu tare da kudin makaranta. Saboda su Malamai masu ba da tarbiyya ne, kuma sukan yi hakan ne domin samar da dalibi mai tsoron Allah wanda zai kai al’umma tudun mun tsira. Idan har Malami ya fahimci haka, to, hakan mai sauki ne. Kun ga kenan Malamai na da ta su gudummawar da za su bada wajen gina tarbiyyar dalibai.
DAWAINIYAR MAKARANTA
Wajibi ne uba (mahaifi) ya yi shirin daukan nauyin makarantar dansa, saboda sauke nauyin da ya hau kansa na karantar da ‘ya’yansa. Akwai wani kuskure da iyaye kan yi a wa su lokuta na gwada rashin halin-ko-in-kula da al’amarin ilimin ‘ya’yansu. Misali; kamar idan yaro ya gudo daga makaranta, sai su ce; “ai kai ne zai amfane ka”. Haba Uba ko Uwa (Mahaifi ko Mahaifiya), mene ne amfanin hankalin da Allah ta’ala ya baka? Kuma mene ne amfanin karfin da Allah ya baka akan Yaro a matsayinka na mahaifi? Ai idan Yaro zai iya gano Muhimmancin makaranta a rayuwarsa (kamar yadda Uban ko Uwar suka fada na cewa; “ai kai ne zai amfane ka”), ka ga kenan, shi ma ya zamo babban mutum kenan? Ya kamata mu fahimci cewa tarbiyyar ‘ya’yanmu yana da matukar muhimmanci ga rayuwar mu da ci gaban wannan al’umma da samar mata da alkibla madaidaiciya (mai kyau). Kuma mu sani cewa ‘ya’yan nan amana ce garemu. Allah yasa mu dace, ya kuma bamu ikon rike amana. Amin summa Amin.