Mukalar Alhamis: Dambarwar Kwankwaso Da Ganduje Ko Za Ta Haifar Da Da Mai Ido?

Yasir Ramadan Gwale yasirramadangwale@gmail.com        +23408099272908

Lokacin zabubbuka na kara kusatowa a kasarnan, yayin da a jihar Kano dangantakar Siyasa ke kara yin tsami tsakanin tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje. Wannan rikici na Kwankwaso da Ganduje abu ne da yake kara ci gaba a kusan ko da yaushe, mai makon kurar fadan ta lafa sai kara turnukewa take kara yi. Musamman yadda magoya bayan bangarorin biyu ke kara zafafa kalamai kan juna.

A baya bayan nan, an ga yadda aka yi rikici a unguwar Chiranchi dake yankin karamar hukumar Gwale, inda ake zargin wasu ‘yan Gandujiyya masu biyayya ga tsohon Shugaban jam’iyyar APC tsagin Gandujiyya Abdullahi Abbas su ne ke da hannu kan wannan farmaki da aka kaiwa ‘yan Kwankwasiyya a ranar lahadin da ta gabata a wajen wani daurin aure a unguwar, har ma ake cewar an raunata dan uwan Abdullahi Abbas Sunusi.

Wasu bayanai sun tabbatar da cewar, Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano tayi awon gaba da Abdullahi Abbas wanda shi ne Kwamishinan ma’aikatar Ayyuka na Musamman da kuma wasu ‘ya ‘yansa guda biyu Abbas da Sani da kuma wani da ke yiwa Abdullahi Abbas din aiki a gida, inda ake zarginsu da hannu wajen jikkata mabiya Kwankwasiyya a ranar wancan daurin aure da aka yi a unguwar Chiranchi a karamar hukumar Gwale inda nan ne unguwar da Abdullahi Abbas yake da zama.

Ance daya daga cikin mutanan da aka raunata a yayin wannan dambarwa, akwai kani ga shi Abdullahi Abbas da ake kira Walid ko kuma Walidin Kwankwasiyya. Walid Abbas Sunusi, ance kani ne ga Abdullahi Abbas, wanda shi Walid din yake mabiyin Kwankwasiyya da Abdullahi Abbas yake adawa da ita.

Ana ganin wannan abu ya auku ne, bayan da aka jiyo Abdullahi Abbas yayi wasu kalamai a wani faifan bidiyo da yake kira ga magoya bayansu da su yiwa tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso jifan Shedan a Dakatsalle a shirye shiryen zuwan tsohon Gwamnan Kano a ziyarar motsa siyasar da zai kawo jihar Kano. Wannan ziyara dai ta tsuma magoya bayan Kwankwason, inda ake ta ganin suna sayen sabbin jajayen huluna da kuma sabbin fararen kayan da zasu tarbi Kwankwason das u a ziyarar da zai kawo jihar kano.

Tun da jimawa, masu fashin bakin siyasa na cewar, wannan rigima tsakanin Kwankwaso da Ganduje ta yi wuri. Tun bayan da Ganduje ya karbi mulki  a 2015 ba da jimawa ba aka fara samun takun saka tsakanin Ganduje da Kwankwaso, har dai ta kai, Ganduje ya salami Sakataren Gwamnatin jihar Rabiu Suleiman Bichi wanda na hannun daman Kwankwaso ne, wannan korar da Ganduje ya yiwa Rabiu Suleiman Bichi ita ce ta fara nuna jan dagar da Ganduje yayi da ‘yan Kwankwasiyya.

Babu ko tantama, wannan rikici na Ganduje da Kwankwaso za ayi haihuwar guzuma tsakanin kowanne bangare. Domin kuwa ga dukkan alamu yanayi na nuna cewar, kowanne bangare tsakanin Gandujiyya da Kwankwasiyya zai yaki dan uwansa a zaben 2019 dake tafe, wanda in anyi hakan kuwa, kowa zai taba kasa tsakanin Ganduje da Kwankwaso matukar Kwankwaso takarar da zai yi ta Sanata ce a jihar kano, tun farko ma ana ganin ba lallai a tsayar da Kwankwaso takara a jam’iyyar APC din ba.

Ganduje Gwamna ne karkashin tutar jam’iyyar APC, kuma yana neman sake tsayawa zabe a karo na biyu, haka shima Kwankwaso Sanata ne wanda ake zaton zai yi takarar Shugaban kasa in kuma bata yuwu ba ya koma takararsa ta Sanata. To, da alamun kowa zai kwan a ciki. Domin zaben da za’a fara yi shi ne na Shugabana kasa da kuma ‘yan majalisun dokoki na tarayya da Sanatoci, wannan zaben idan har Kwankwaso ya tsaya takarar Sanata kuma aka kayar da  shi to ba shakka shima zai tsaya kai da fata wajen ganin keyar Ganduje ta taba kasa.

Haka nan shima Gwamna Ganduje, dukkan alamu sun nuna cewar yanayin dukkan abin da yake so domin tadiye kafar Sanata Kwankwaso a yunkurinsa na yin takara a 2019, ko dai ta Shugaban kasa ko kuma ta Sanata. Babu tabbas ko Kwankwaso zai ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC, wasu na hasashen zai tsallaka zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP.

To, masu Magana na cewa, siyasa babu abokin din-din-din babu kuma makiyi na din-din-din. Idan Kwankwaso ya tsallaka zuwa jam’iyyar PDP to zai hadu da tsohon abokin burminsa na siyasa Malam Ibrahim Shekarau, kuma wannan abu indai ya tabbata, to Kwankwaso da Shekarau zasu hadu a PDP su kayar da Ganduje idan har an tsayar da Malam Salihu Sagir Takai takarar Gwamna, domin kuwa, Takai ne dan takarar da PDP din take dashi da baya bukatar a tallata shi matukar ance shi ne dan takara.

Idan PDP ta yi sa’a, Takai ne dan takara, kuma Shekarau da Kwankwaso suka hadu a jam’iyya daya, to babu makawa zasu kai keyar Gwamna Ganduje kasa a kakar zabe ta 2019, Domin Babu alamun za’a iya sasantawa tsakanin tsohon Gwamna Kwankwaso da Ganduje, domin ana iya cewar bakin alkalami ya bushe, rikicin kullum kara rincabewa yake yi tsakanin gaggan ‘yan siyasar biyu.

Wasu da dama na tunin shin ko tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau zai sauya sheka idan Kwankwaso ya dawo PDP? Amma a wata amsa da tsohon Gwamnan ya taba bayarwa, yace shi bashi da wata matsala tsakaninsa da Kwankwaso, alamun da yake nuna cewar, Malam Shekarau ba zai tsallaka zuwa jam’iyyar APC ba idan Kwankwaso ya dawo PDP.

Malam Ibrahim Shekarau shi ne jagoran jam’iyyar ta PDP yanzu a kano, ko ya za ta kaya idan Kwankwaso ya dawo? Wannan ba wata matsala bace, domin da Shekarau da Kwankwaso duk tsofaffin Gwamnoni ne, sai dai ana ganin dukkansu suna da bukata iri daya ta neman takarar Shugabancin Najeriya, domin tuni Malam Ibrahim Shekarau ya ayyana cewar zai tsaya takarar Shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, kuma har ya aikewa da uwar jam’iyyar bukatarsa ta tsayawa takarar, to, sai dai shima tsohon Gwamna Kwankwaso ana ganin zai tsaya takarar Shugaban kasa matukar shima ya tsallako zuwa jam’iyyar PDP, kamar yadda mabiyansa suke kiraye kirayen ya tsaya.

Koma dai ya za ta kaya, Malam Shekarau da Kwankwaso suna da bukata iri daya a mataki na tarayya, domin ana ganin dukkansu na son tsayawa takarar Shugaban kasa, haka kuma, a Kano, kowannensu yana da burin ganin an kayar da Gwamna Ganduje daga kujerar Gwamnan Kano, domin shi Kwankwaso a yanzu ba shida wani abu sama da ganin an kai keyar Ganduje kasa a zaben 2019, haka nan shima, za’a iya cewar Malam Shekarau na fatan ganin dan takararsa Malam Salihu Sagir Takai ya kai ga nasara a wannan zaben ya kayar da Ganduje.

Koma dai ya za ta kaya tsakanin Gwamna Ganduje da kuma Sanata Kwankwaso, wannan dambarwa tsakaninsu ba za ta haifar musu da da mai ido ba a Siyasance, domin ba abin da za’a yi sai haihuwar Guzuma, ‘ya kwance, uwa kwance. Kuma wannan rikici ba komai zai kara yi ba, illar Karin samun nasarar jam’iyyar PDPmai adawa, wadda ake ganin in ta tsayar da Takai, wanda shima a makon nan ne ya kaddamar da sunayen ‘yan kwamitin yakin neman zabensa, to ba makawa wannan rikici na Kwankwaso da ganduje ya sa Malam Salihu Sagir Takai zai samu nasarar zabe a bagas.

Exit mobile version