MUKALAR ALHAMIS: Mu Tashi, Mu Farka ’Yan Arewa…

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@gmail.com          +23408099272908

A baya anyi mana wawar hasarar Sa Abubakar Tafawa Balewa da su Sa Ahmadu Bello da JS Tarka, Joe Garba da sauransu, wadanda ba dan komai aka kashe su ba sai dan tsayawarsu wajen ganin anyi adalci a shugabancin tarayyar Nijeriya.Watakila kuma dan kasancewarsu ‘yan Arewa ne. Mu ne mutanan Arewa saboda Alkawari da son zaman tare muka dauki Shugabancin tarayya da ke hannunmu muka dauka sukutum muka mikashi ga Obasanjo! Anyi hakan da kyakkyawar niyya ko akasin haka Allah shi ne mafi sani.

Tun bayan waccan dama da ta subuce mana, inda Obasanjo da aka bashi amana ya dinga gasa mana aya a hannu, har ta kai mun kai wani mataki da muke ta magagin yadda waccan dama da muka dauka da hannunmu muka bayar muke fatan dawowarta hannunmu. Tun a shekarar 2003 da 2007 da kuma 2011 ake ta wannan fafutuka ta ganin cewar ikon tarayya ya koma hannun mutanan Arewa, domin da yawan mutanen Arewa sunyi imani cewa, babu wani dan kudu da zai yi mana Adalci face idan har namu ya samu, shi yasa muka makance muke nema ido rufe. Amma ya zuwa yanzu, da dan Arewa ya samu, kuma aka ci rabin wa’adin mulki meye makomar Arewa a siyasance? Shin Arewa ta amfana da wannan shugabancin danta da akai ta fatan samu ko ana ha-maza ko ana ha-mata? Wadanne irin manyan ayyuka ne Arewa ta rabauta da su? Ina makomar shirin nan na yashe kogin Kwara da gwamnatin marigayi tsohon shugaban kasa Umaru YarAdua ta somo? Ina ganin lokaci yayi da zamu yi karatun baya mu kallai abubuwan da suka wakana, da yadda aka faro da kuma inda ake a yanzu.

A halin da ake ciki, da kuma abubuwan da suke faruwa, ina ganin wasu daga cikin mutanen Arewa sun fara farkawa daga barcin da suke yi. Domin yanzu dai Gwamnatin da mutanen Arewa suka tsuguna suka haifa da taimakon Allah na neman zamar musu inuwar giginya, na nesa kan sha dadinki. Tun farkon kunshin wannan gwamnati. Domin manya-manyan ayyukan raya kasa na ma’aikatar ayyuka kusan fiye da rabi sun karkata ne ga wani yanki guda daya, in banda ‘yan tsiraru da aka raba wa sauran bangarorin kasar nan.

Abu mafi muhimmanci da ya kamata a koda yaushe mutanen Arewa su sani kuma su yi la’akari da shi shi ne, a koda yaushe mu nemi mutumin da zai yi mana adalci a kunshin shugabancin kasarnan, ba sai lallai dan Arewa ne kadai zai yi mana adalci  ba. Domin ko ba dade ko ba jima sai dan kudu ya shugabancin kasarnan matkkar ana kan wannan tsarinda ake kai, ko dai ya zama ta hanyar zabe ko kuma ta hanyar da Goodluck Jonathan ya zama. Saura da me? Abin da ya zamar mana tilas shi ne, sani kasarb nan, Allah ne ya hada mu, kuma tilas mu koyi hakurin zama da juna. Sannan a kodayaushe mu yi  fatan samun shugaban da zai yi mana Adalci ba tare da nuna wariya ko bambanci ga wani bangare ko sashin kasarnan ba. Allah madaukakin Sarki ma cewa yayi, Mulki yana tabbata da Adalci ko da kuwa a hannun wanda bai yi Imani bane, amma mulki baya tabbata a hannun wanda yayi Imani indai ba adali bane.

Yau ko raba kasarnan aka yi tilas ne mu yi  makwabtaka da juna tsakaninmu da sauran mutanan kudanci. Abin da ya faru a kasashe Sudan da Sudan ta Kudu da kuma Habasha da Eritiriya ya isa ya zama misali a garemu, musamman wasu tsagerun da suke kiran lallai a yayyaga wannan kasa kowa ya kama gabansa. Mutanean Sudan Ta Kudu da suka nemi ballewa daga Sudan kuma aka ba su dama suka balle din, karshe wa gari ya waya? Sai gashi mutanen kudanci da suka nemi ‘yancin da aka zuga su akansa, suna rokon kasar Sudan ta bude musu kan iyaka, domin su shigo neman mafaka. Don haka a zabubbukan da suke tafe a shekarar 2019, sai an duba meye makomarmu. Ya kamata Arewa ace tana da wata ajanda wadda zata inganta batun sha’anin tsaro, ilimi, da lafiya, da tattalin arziki, da noma, da kasuwanci da ayyukan raya kasa a Arewa. Rashin samun kyakkyawan tsarin da ya kamata mu tafi akan sa, shi ne ummul habasin dalilin da ya sanya, ko da mun kafa gwamnatin da muke jin cewa tamu ce, sai mu kare da kuturun bawa.

Mutanan Yamma da yake su suna da tsarin da suke tafiya akansa, wanda ya fifita bukatun mutanen wannan yanki, in muka kula ba su da wata fargabar ko waye zai zama shugaban Nijeriya, domin sun kwan da sanin cewa, koma waye shugaban kasa, suna da manufofi da suka fifita mutanen yankinsu, wanda sukan jajirce wajen ganin biyan bukatun wannan yanki nasu. Ya isa abin misali, yadda a wannan Gwamnatin ta Shugaba Muhammadu Buhari Allah ya kara masa lafiya, suka samu manya-manyan mukamai da ma’aikatu masu dan karen kudi. Misali Minista Fashola da aka bashi jan ragamar manyan ma’aikatun da suke da ministoci shida aka bashi shi kadai, ma’aikatar ayyuka da gidaje da lantarki, kusan wadannan sune sahun gaba ko zubin farko na manya manyan ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Bugu da kari mutanen Yamma su ne ke da ministan kudi da ministan ma’adanai da sauransu, sannan kuma ga Gwamnan Babban Bankin Nijeriya da yake dan Kudu ne da kuma Ministan tsare-tsare. Mu mun kare tamkar da kuturun bawa. Gaskiyar magana idan ba tashi muka yi ba, mutanen Kudu ba za mu iya tar da suba a ayyukan ci gaban kasa ba, domin ko a yanzu Legas kadai bana zaton akwai jihar da zata iya cimmata nan kusa.

Daga cikin abin da mutanen Yamma suka yi, wanda ya ciyar da yankinsu gaba, shi ne, yadda suka yadda cewa, Legas itace shalkwatar yankinsu, kuma basu da wani haufi kan duk wani ci gaba da Legas zata samu. Sabanin mu mutanan Arewa da muka bari Hassada da kyashi suka dabaibaye mu.Duk wani Gwamna abu in bai shafi jiharsa baba ruwansa. Yanzu da Gwamnonin Arewa za su hada kai suce tilas sai an ci gaba da aikin yashe kogin kwara yadda za mu samu babbar gabar teku a Arewa, ai da sun kyauta kuma na tabbata zasu samu goyon bayan mutanan Arewa dari bias dari. Amma sai kaga kowane Gwamna bai damu ba.Yanzu dai ance Gwamnonin na Arewa sun yunkuro domin dawo da tsohon Bankin Arewa da aka rusa shi da gangan. Muna fatan Allah yasa wannan haka tasu ta cimma ruwa, wajen dawo da bankin Arewa. Kana kuma, muna fatan Gwamnonin zasu yunkuro wajen dawo da manya-manyan abubuwan Arewa da suka rushe kamar NNDC da kamfanin Buga Jaridu na Arewa NNN, da sauran kamfanunnukan masaku da suka durkushe tsakanin Kano da Kaduna tare da tayar da komadar wadandan da suka gurgunce.

Lallai Gwamnatocinmu na Arewa wanda suke kan mulki da masu zuwa, su sani wannan shi ne gatan da zasu yiwa Arewa. Domin irin yadda mutanan Arewa muke da yawa, kuma adadinmu yake karuwa cikin sauri, tilas a nemarwa al’umma makoma, in bahaka ba, nan gaba abubuwa ba zasu yi kyau ba.

A dan haka ne yake da muhimmanci, a zabubbukan da suke tafe a shekarar zabe ta 2019. Ya zama wajibi Shugabannin Arewa da suka kunshi Gwamnonin Arewa da Sarakunan Arewa da Kungiyoyin Dattawa da Matasa da Dalibai da Manoma da Makiyaya da ‘yan kasuwa da masu masana’antu na Arewa su yi wani shiri mai karfi na shatawa Arewa hanyoyin ci gaba da kuma alfanun da ake fatan samu daga Gwamnatin Tsakiya.

Samar da irin wannan “Road Map” din ne kadai zai tseratar da Arewa daga barazana da zaginmu da ake yina cewa mu cima zaune ne. Irin wannan ne zai sa nan gaba ko waye zai zama Shugaban Nijeriya, Arewa ba ta da wata fargaba akan kowa. Domin muna da tsarin da muke fatan Gwamnatin Trayya zata cika mana su, kamar yadda takwarorinmu na Kudu Maso Yamma basu da wani haufi akan kowaye zai zama shugaban Nijeriya, tunda sun kwan da sanin cewa, bukatunsu da na yankinsu sune kan gaba wajen duk wani goyon baya da zasu baiwa dukkan wata Gwamnati da za’a kafa a Tarayya.

Bayan haka, yana da kyau a Matakai na Gwamnoni da Sanatoci da ‘yan majalisun dokokin tarayya da na jihohi, mutanan Arewa su tsaya su yi karatun ta natsu a wannan zabe. Domin bai kamata mu kwata abin da ya faru a 2015 ba. Mu yi  zabe ido rufe ba tare da duba cancantar mutanen da ya dace a zaba ba. Lallai lokacin yin Makahon zabe ya wuce. Domin dai an gani, a baya yin hakan bai tsinana komai ba, sai da-na-sani, wadda Bahaushe ke cewa keya ce.

 

 

Exit mobile version