Aliyu Dahiru Aliyu dahirualiyualiyu@gmail.com
Tarihi shi ne hanya mafi sauki da mutum zai duba bayansa domin ya yi nazarin abin da zai wakana a gabansa don ya kauce wa hadurran da zai iya fuskanta a nan gaba. Daga Ibn Khaldun zuwa Arnold J. Toynbee, duka masana falsafar tarihi sun bayyana cewa, ci gaban al’umma ko faduwarta yana ta’allaka ne da yadda take karantar tarihinta kuma ta fitar da natijar ci gabanta. Hatta marubuta ‘yan kasar nan da suka fahimci falsafar tarihi, kamar Dr. Yusufu Bala Usman da Dr. Tijjani Naniya, sun yi bayanin cewa, rashin ci gaban Afirka yana ta’allaka ne ga yadda
take watsi da tarihinta. Tana kallon abin da ya faru a baya kamar wani abu da ya wuce kuma ba zai dawo ba balle har ta koyi wasu darussa da za ta amfana da su wajen tafiyar da rayuwar ‘yan cikinta.
Shekara hamsin kenan bayan yakin basasa da aka yi bayan juyin mulkin shekarar 1966 ya bar labarai da yawa marasa dadin ji. Ya bar kasar nan cikin rudu, dimuwa da hargitsi. Dubunnan mutane suka mutu, kuma miliyoyi suka rasa guraren zamansu. Yunwa ta yi walagigi da
Marubuta da yawa sun yi rubutu a kan yadda abin ya faru tun daga farawar balahirar a watan Yulin shekarar 1967. Daga tsohon shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo, a littafinsa “My Command” (1980) da kuma wani sashi a cikin kundin farko na littafinsa “My Watch” (2014) zuwa Adewale Ademoyaga a cikin “Why we Struck” (1981).
Abin da ya janyo wancan tashin hankalin ta bangaren Ojukwu shi ne dai yake kara kokarin tayar da wani hankalin ta bangaren Nnamdi Kanu a yanzu. Duk da ba dukan ‘yan kabilar Ibo su ne masu ganin lallai su za su mulki kasar nan ko a ware ba, amma mafi yawansu ba su aminta su ga dan’arewa ko Hausa/Fulani a kan mulkin kasar nan ba. Juyin mulkin Aguiyi Ironsi da yadda aka kashe manya daga Arewa masu yawa shi ne ya nuna haka. Tare da cewa, wadanda su kai juyin mulkin sun nuna cewa suna so su dawo da kasar ne kan turbar dai-dai, amma a zahiri abin yake cewa tsanar mulkin ‘yan’aArewa ne kawai a ransu amma ba ci gaban kasar ba.
Burinsu su hana duk wani dan’arewa shiga a dama da shi a cikin siyasar kasar nan ko shugabancinta. Haka shima fafutukar neman kasar Biafra a yanzu. Karya ce kawai da take fake wa da neman ‘yanci amma tsantsar tsanar a ga dan’arewa ne a kan mulki. Idan neman kasar ne a ransu me ya sa ba su fara komai ba sai bayan da Muhammadu Buhari ya hau mulki?
Me ya sa a ka hango Nnamdi Kanu a wani fefen bidiyo a Ingila yana cewa ba za su yarda wasu su zo su rabamusu kasa ba? Me ya sa bayan Buhari ya hau mulki sannan kuma shi ya jagoranci raba kasar?
Abin da Nnamdi Kanu da kungiyarsa ta ‘yanta’addan IPOB (kamar yadda hukumar sojoji suka ayyana ta) suke aikata wa alamace ta wadanda suke jin haushin sakamakon siyasar da ya ba wa dan’arewa damar jagorancin kasar nan. Wannan haushin ya sa a lokaci da yawa ya dinga kalaman kiyayya da zage-zage ga al’ummar Hausawan da yake ganin su ne ke jagorantar kasar a yanzu. Wannan damuwar da fushin na sakamakon siyasa shi ne ya tunzoro shi har yake kiran ta dole sai an raba kasar nan ko kuma su buga gangar yaki. Duk wannan iri daya ne da abin da ya faru kafin yakin basasa da kuma juyin mulkin da aka yi a shekarar 1966, kamar yadda yake a rubuce a cikin litattafan tarihi. Tamkar Ojukwu, daga karshe Nnamdi Kanu shima neman tsere wa zai yi tunda dama an ce yana da takardar zama ta Birtaniya ya bar ‘yan’uwansa da samarin da ya jefa cikin musifa a gurarensu.
Wancan lokacin da aka yi yakin basasa karkashin Ojukwu wanda yake yana da madafun iko da kuma sojojin da suke goyamasa baya shima bai yi nasara ba, sai dai rasa rayukan da aka yi kawai. To wannan ma ba abin da zai janyo a karkashin farar hula kamar Nnamdi Kanu da ya tara samari marasa aikin yi sai asarar rayuka da dukiyoyi. Karantar tarihi yana da muhimmanci don a gane abin da zai iya wakana. Tsofaffin da suka samu ganin wancan lokacin su gaya wa samarin ‘ya’yansu cewa, shi yaki ba abu ne mai dadi ba. Kamar yadda aka fara wancan ana zaton za a gama a ‘yan kwanaki amma sai da ya dauki shekaru to shima wannan idan aka fara to sai yadda Allah ya yi kawai. Yaki babu dadi. Iya abin da muke fuskanta a Arewa na Boko-haram ya sa na kara tsanar yaki da tashin hankali.
Mutum ya baro iyalinsa alhalin bai tabbatar da komawarsa gida ba! Ana tsoron shiga hatta kasuwa ko guraren ibada saboda tsoron yaki. Kuma dai rig-kafi ya fi magani. Tun yanzu da aka fara “Edercise Phyton Dance II” to kada a bari abin nan ya zama yaki don samun zaman lafiyarmu a kasa. Yakin Syria daga zanga-zanga ya fara amma kalli yadda ya zama! Yakin Libya daga juyin mulki kalli yadda kasar ta lalace! Yakin Yemen daga bukatar sanja shugaban kasa kalli yadda ya bar yara da mata a cikin kunci! Maganin kar a yi to fa kada a soma. Waye ya san wannan yakin wani hali zai iya kai mu?!
Su kuma ‘yansiyasa da suke burin a raba kasar nan domin su samu sababbin madafan iko, su yi hakuri su fara barinmu mu zauna lafiya da juna don kada su kara jefa mu cikin sabon bala’i. Maimakon Nnamdi Kanu da ‘yan’uwansu na IPOB su tashi hankalin kasar nan gwara su hada jam’iyyar siyasa su sanya shi Kanu a jagoranta ko dantakararta har sai ya kai ga nasarar zama shugaban kasa. Irin wannan shi ne abinda Oju kwu ya gane kenan daga karshen rayuwarsa har ya kafa jam’iyyar APGA da ya yimata takarar da bai samu nasara ba. Nijeriya kasa ce mai bin tsarin dimokradiyya da ta zuba kaidojin yin takara ga duk mai sha’awar shugabanci. Duk wanda yake ganin akwai ci gaban da zai iya kawowa kabilarsa ko al’ummarsa to sai ya fito takara ya nemi taimakon Allah har ya samu nasara. Wannan shi ne hanyar da za ta kai mu ga nasara ba ta da jijiyar wuya ko neman sai an bawa wasu shugabanci ko kuma ayi yaki ba.