Mulkin Buhari Gaba Kura Baya Siyaki Ne Ga Arewa, Inji Yerima Shettima

Arewa

Daga Khalid Idris Doya,

Kwamred Yerima Shettima, Shugaban kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa, ‘Arewa Youth Consultative Forum’ (AYCF), ya shaida cewar, bangaren Arewacin Nijeriya ne ya fi kowa ne yanki samun koma-baya duk kuwa da cewa dan Arewan, Shugaba Muhammadu Buhari, ne ke kan kujerar shugabancin kasar.

Ya ce, duk da irin tagomashin da shiyyar Arewa ke da shi a lamarin mulkin kasar, amma nan ne aka fi kashe jama’a da kuma yawaitar masu garkuwa, fashi da makami da kuma sace mutane domin neman kudin fansa a zamanin Buhari, wanda ya nuna hakan a matsayin abun bakin ciki ainun.

“Abun bakin ciki ne a yau namu ne shugabanin hukumomin tsaro, namu ne mutum mafi girman mukami a kasar nan (Shugaban Kasa), amma har yanzu mu ne yanki mafiya kara samun koma-baya ga kuma uwa-uba yawaitar kashe-kashe, garkuwa da mutane da ayyukan ta’addanci,” inji shi.

Shettima ya fada wa majiyarmu cewa, “a yau ta fada cikin rikici fiye da yadda ake tsammani; wasu jama’ar Kudu ba su da masaniyar ma abun da ke faruwa a Arewa, ba su san halin da yankin ke ciki ba. Ya kamata a zauna a kalli yanayin tsarin tsaronmu a kasar. Dukkaninmu mu ’yan Nijeriya ya kamata mu fahimci cewa lamarin tsaron kasa ya shafi kowa da kowa.”

Ya kara da cewa, Nijeriya tana matukar bukatar hadin kai da gaggawar daukar matakan da suka dace, domin dakile sake barkewar yakin basasa kamar wanda ya taba faruwa shekaru 51 da suka wuce.

“Wasu daga cikinmu ma ba a haife su ba a lokacin yakin basasa, amma daga abun da muka karanta, ababen da suka taru suka haifar da yakin basasa din, ba a ayyana su ba. Don haka bai kamata mu zura ido mu bari har mu sake asaran irin wadanda aka yi asararsu a wancan lokacin ba,” ya shaida.

“Wannan dalilin ne ya sanya wasu daga cikin matasnamu masu tasowa suka kage kai da fata kan cewa dole ne lamura su dawo tafiya daidai domin kauce wa fadawa wani sabon yaki a kasar nan.

“Idan Nijeriya ta kuskura ta sake fadawa yakin da ya faru shekaru 51 da suka wuce, zai yi wuya kuma kasar ta sake rayuwa daidai. Shekaru 50 da daya suna da nisa ga shi kuma zancen a yau.

“Matsaloli da rarrabuwan kawuka na kara yawaita a tsakaninmu duk da yafiya da sauran abubuwa. Ina addu’ar Allah ya karemu kada mu sake fadawa abun da Nijeriya ta fuskanta shekaru 51 da suka shude.

“Idan har muna son hakan ta kasance, dole ne mu rungumi abubuwa biyu; mu rungumi daidaito da tabbatar da adalci ga kowa; wadannan ne kawai za su karemu daga sake fadawa wani yaki,” a cewar shugaban matasan.

Da ya ke mayar da martani kan cewa an yi watsi da wofintar da shiyyar Kudu masu Gabas a siyasar kasar, ya shaida cewar, “a matakin farko ya kamata ne kuma ma tilas ne shiyyar Kudu maso Gabas ya zama ya aza niyya kuma ya maida hankali. Na sha fadin cewa, ba zai yiwu mutum daya ya cigaba da kokarin jawo tarnaki ga zaman lafiyan kasarmu da ke ta kokarin ginawa ba.

“Na yi imanin cewa a shiyyar Kudu maso Gabas akwai hazikan mutane a cikinsu, amma barin da suke yi wani mutum guda yana magana yadda yake so kuma su jama’ar yankin sun ki yi masa magana balle su taka masa burki.

“Ba za a iya yi mana barazanar iska ba; ba kuma za a yi wa Nijeriya barazana ba. Abun haushi ma shine, ba ya kasar, a lokacin da yake kasar bai yi wani tasiri ba. Dukkaninmu shaida ne ya kafa kungiya mai dauke da bindiga a hannunta; bai kuma dace kawai jama’a sai su nade hannayensu suna kallo hakan ba,” ya shaida.

Exit mobile version