Khalid Idris Doya" />

Mulkin Kama-Karya A Ke Gudanarwa A Jihar Bauchi –Wakilin Birni

ALHAJI YAKUBU SHEHU ABDULLAHI (Wakilin Birni)  dan majalisa ne da ke wakiltar cikin garin Bauchi  a majalisar dokokin jihar Bauchi; kuma wanda ya nemi APC ta ba shi tikitin tsayawa takarar dan majalisar tarayya; a hirarsa da ‘yan jarida ta wayar tarho kan kewaye kewaye gidansa da ‘yan sanda suka yi, ya zargi gwamnan Bauchi da neman yi musu kama-karya. Wakilinmu na Bauchi KHALID IDRIS DOYA na dauke da tattaunawar kamar haka:

Honorabul Yakubu Shehu mun samu labarin jami’an tsaro sun kewaye gidanka akwai wani abu ne da ke faruwa da kai?

Ni dai abun da na wayi gari da samun labarinsa, domin ni na rigaya ma na fita don yin tafiya, sai ake fada min cewar an kawo jami’an tsaro har kusan mota biyu ko uku na ‘yan sanda sun je sun kewaye gidan Dawakaina, inda mukan yin taro wani lokacin mu tattauna hidimarmu ta siyasa.

Amma wannan abun bai kasa nasaba da takarar da ni na tsaya na majalisar tarayya a karkashin jam’iyyar APC, wanda kuma an yi wannan zaben kowa ya shaida a cikin garin Bauchi an yi babu tashin hankali wanda nine na kasance na yi rinjaye da kuri’a dubu 25,577 wanda ya sanya na ci na daya, wanda yake bina yana da kuri’a dubu 12.

A sakamakon haka, bayan an gama zabe sai muka ji an je an sanar da sunan wani wanda shi din ina tsammanin bai wuce na 4 ko na 5 ba ma, sai aka bayyana wai shine ya ci; tun daga wannan lokacin mutane na sun yi ta Allah ya tsine, Allah wadai da abun da aka yi, amma ni sai na jawo hankalinsu kan cewar mu ba za mu bi hanyoyi na tashin hankali ba, akwai hanyoyin da suka dace da zamu bi na mika takardarmu na koke ga uwar jam’iyya na abun da aka yi mana wanda kuma mun yi hakan.

Ni dai a matsayina a yanzu da nake magana da kai ni dan majalisa ne mai wakiltar mazabar cikin garin Bauchi a majalisar dokokin jihar Bauchi kuma ni zababbe ne. a yadda ya dace, yau (ranar Talata) ya kamata mu tafi aikin majalisa sai muka ga an turo mana sakon waya kan cewar shi Kakakin majalisar jihar ya dage zaman majalisar wai sai an sake sanya rana, a cewar sanarwar wai suna Abuja ana ci gaba da sauraron koke-koken sauran ‘yan takarar da ba a yi musu adalci ba. wanda mun yi bincike a wajen sauran shugabanin majalisa suka ce basu da masaniya kan wannan hukuncin. Mai iyuwa hakan bai rasa nasaba da rade-radin da ke cewa za a tsigeshi ne, shi ya sa ya daga zaman don gudun tsiguwa.

Hatta ita kanta majalisar an kai jami’an tsaro an jibge su, an kuma tsare, kai ban ma yi tsammani kowani dan majalisa idan ya je za a barshi ya shiga ba, don ko ma’aikatan wajen ma babu mutum ko daya, don sai da na je na tabbatar tukunna na bar garin Bauchi.

Yanzu an zo an zuba jami’an tsaro a gidana wanda ni ban san meye kuma na yi ba. ni dai dan Nijeriya ne, kuma dokar kasa ta bani damar na yi hulda da kowa muddin ba wani abu na tada hankali zan yi ba, wanda kuma ni mai bin doka ne, hasalima ni mai yin dokar ne. don haka bai kamata ma a sameni da wani abu na taka doka ba, amma yanzu nine ake neman a tursasa a ci min mutunci, ban sani ba ko ni ba dan Bauchi ba ne to ban sani ba.

Ganin dai cewar jami’an tsaron da suka kewaye gidan naka ba kai ne ka gayyace su ba, ya kake fassara wannan lamarin?

Wannan abun da na ke fassarawar yanzu dai mun samu mulki na kama karya, mulki kamar wanda ke kama da mulkin soja na karfi na tursasawa da cin mutunci, shi ne wanda gwamnan jihar Bauchi ya dauko yi akan talakawar jihar Bauchi, mu kuma ‘yan Bauchi ne babu yadda za mu je. Ni a matsayina na mai doka na kai idan na yi wani laifi ne a aike min da gayyata amma ba haka kawai a zo a taramin jami’an tsaro babu izini a gidana ba.

Shi Kakakin Majalisa ya tsaida zaman da ya dace ku zo ku zauna kamar yadda ka fada, daman yana da hurumin yin hakan ne?

Baya da shi! Inda daman yake da wannan hurumin shine inda da sun zauna da jagorori na majalisar suka ga cewar akwai iyuwar hakan, a hakan ma sai sun tuntubemu gabanin su yanke hukunci idan masu rinjaye daga cikinmu sun amince a yi hakan. don haka an yi wannan ne kawai ba tare da jagororin majalisar ba, don mun tambayesu babu wanda ya sani, don jiya (ta ranar da muka yi hirar) muna tare da su kamar Honorabul Adamu Bello, Honorabul Auwal Hassan wanda da shi mataimakin Kakakin majalisa dukkaninsu muna tare da su kuma suna daga cikin shugabanin majalisa, kai hatta shi ‘Leader’ na majalisar ma baya nan domin ya kai dansa makaranta don yanzu haka ma shi baya Nijeriya, don haka shi Kakakin majalisar ne kawai ya yake wannan hukuncin nasa. Kuma ma ya je ya turo jami’an tsaro su killace majalisar ko na ce suka hada baki da gwamnan jihar Bauchi don a turo jami’an tsaro don su hana mu aikinmu na majalisa wanda aka zabemu don mu yi; aikinmu ne, babu wani tashin hankali, ba a yi fada da wani ba, babu wani wanda ya zagi wani, babu wani abu na dalilin hakan, illa iyaka sun sha jinin jikinsu ne na aikata rashin adalci da suke yi wa mutane a wajen zaben fidda gwani, inda suka cire sunayen wadanda suke so suka saka, daga cikin akwai ‘yan majalisu 21 wanda wannan abun ya shafesu don haka ina ganin shi ya sa ake jin tsoron zaman da zamu yi yau (ranar Talata) don kada aje a yi wani abu ko a cire Kakakin majalisar wanda yake jin wani isa-isa don mu majalisa ba mu san da wannan ba, ba mu kuma kawo maganar hakan ba, su dai sun sha jinin jikinsu kan rashin gaskiyar da suke yi.

Me za ka ce ga magoya bayanka da suke cikin garin Bauchi kan halin da kake ciki?

Kiran da na ke ga magoya bayana sun dai sanni ni mai son zaman lafiya ne, kuma su ma magoya bayana din ina kira a garesu su zama masu hakuri da zaman lafiya, mu ba mu da wani wajen da ya wuce jihar Bauchi kuma babu inda za mu je. Su yi hakuri mu ga karshen wannan abun cikin sauki, cikin goyon baya, tun da mun mika al’amarinmu ga Allah, kuma da yardarsa zai ba mu nasara, duk wanda aka zalumci Allah baya barci don haka magoya baya a bi doka a zauna cikin kwanciyar hankali.

Kuma ina kira dukkanin mai kishin jihar Bauchi lallai ya je ya amshi katinsa na yin zabe, mai shi ya kara tanadarwa, marar shi ya tabbas ya je ya mallaka, mu zauna mu jira lokacin nan da ake magana na 2019. Hatta shi kanshi shugaban kasa yana maganar a zabi cancanta, kuma za mu fito mu zo mu zabi cancanta, za mu kasa-mu-tsare mu jira, saboda mun yi a baya shi kansa shugaban kasa abun da ya kawosa kan kujerar kenan, don haka za mu kuma, yanzu ma za mu yi. Ba zai iyu muna ji muna gani a jawo mana asara kan abun da muka gina shekaru uku ko hudu, yanzu lokacin da tattalin arziki ya fara dawowa muna tunanin shugaban kasa zai zo ya yi mana aiki a jihar Bauchi wani ya tunzura jama’a a jihar nan da zai sanya Buhari ya gaza samun kuri’u masu yawa ba zamu sake hakan ba. don haka jama’a su sani shugaban kasa bai da hanu kan hakan gwamnan jihar Bauchi ne kawai ke da hanu kuma za mu fito mu zabi cancanta.

 

Exit mobile version