Kungiyar ‘Pan Niger Delta Forum’, (PANDEF) a ranar Asabar, ta bukaci Kudu maso Kudu da yankin Kudu maso Gabas da su hanzarta haduwa tare da cimma matsaya kan yankin don samar da shugaban kasa nan da 2023 mai zuwa.
Mai magana da yawun PANDEF, Ken Robinson, wanda ya bayyana hakan a wata hira da jaridar The PUNCH, ya kuma yabawa gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, wanda ya fada a ranar Juma’a cewa mulki ya koma yankin Kudu a 2023 saboda adalci.
Zulum ya fada a wani taron ne a Legas cewa akwai bukatar a yi adalci a kasar nan, ya kara da cewa mayar da hankali gefe daya ya zama babban abin da yake damun ‘yan kasar.
Gwamnan ya kuma ce ya kamata Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu su tashi su fara tattaunawar neman mulki gabanin zaben 2023. Da yake maida martani a ranar Asabar, mai magana da yawun PANDEF ya yaba wa Zulum kan yin magana a lokacin da wasu masu sha’awar bangaranci a kasar suka ce babu wani abu kamar tsarin shiyya-shiyya.
“Don haka, Zulum ya kasance yadin haka ne domin iko ya koma Kudu. Ya kamata a yaba masa saboda fadin gaskiya a tsakanin mutane, yana mai cewa babu shiyya-shiyya. Ya kamata iko ya koma Kudu – tsakanin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas. ”
Mai magana da yawun PANDEF din ya ce kungiyar ta amince da gaskiyar cewa yankin Kudu maso Gabas ba ta mulki kasar nan ba tun lokacin da aka koma mulkin Dimokradiyya a 1999, amma kuma ya nuna cewa a kyale Kudu-maso-Kudu su kammala shekaru takwas wanda tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fara a 2011 kafin barin mulki a 2015.
Ya ce, duk da haka, Nijeriya, a wannan matakin, tana bukatar shugaban da ba zai wakilci wata kabila ko bangaranci ba kawai ya zama shi shugaban da zai wakilci bukatun dukkan ‘yan Nijeriya ne.