Muller Ya Sake Sabon Kwantiragi A Bayern Munchen

Dan wasa Thomas Muller ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar shekara biyu, domin ya ci gaba da buga wasa a kungiyar ta Bayern Munich, kamar yadda shugabannin kungiyar suka tabbatar a ranar Talata.

Hakan na nufin kwantiragin Muller zai kare a kungiyar ta Munich a karshen kakar wasa ta shekara ta 2023 wanda kuma daga nan ne zasu iya kara masa sabon kwantiragi idan har yana buga abinda yakamata.

Dan wasan tawagar Jamus din mai shekara 30 a duniya ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich wasanni sama da 500, ya kuma lashe manyan kofuna guda 16 tun bayan da ya fara buga mata kwallo a shekarar 2009.

Haka kuma Muller ya ci wa Bayern Munich kwallo 116 kawo yanzu sannan kuma yana bugawa tawagar ‘yan wasan kasar Jamus wasa kuma yana cikin tawagar data lashe kofin duniyar da aka buga a kasar Brazil a shekara ta 2014.

Kungiyar ta Bayern Munchen tana ta daya akan teburin Bundesliga na bana da tazarar maki hudu tun kan a dakatar da wasanni ranar 30 ga watan Afirilu, sakamakon bullar coronabirus duk da cewa ba tayi barna ba sosai a kasar Jamus.

Ranar Litinin ‘yan wasan Bayern Munich sun yi atisaye sai dai ba su hada jikinsu ba, kamar yadda aka dauki matakan hana yada annobar sannan kuma ana saran ragowar kungiyoyi zasu dawo a kokarin da hukumomi sukeyi na dawowa domin ci gaba da buga wasanni.

 

 

Exit mobile version