Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

Mummunan Hari A Filato: Rayuka Sama Da 29 Suka Salwanta

by Tayo Adelaja
October 17, 2017
in MANYAN LABARAI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Mustapha Hamid

Dole A Taka Wa Haukar Nan Burki – Buhari

Sama da mutane 29 ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka ƙaddamar jiya a ƙauyen Nkiedonwhro da ke garin Irgwe na ƙaramar hukumar Bassa ta Jihar Filato. Mata da ƙananan yara ne wannan hari ya fi rutsawa da su.

Idan dai ba a manta ba, an samu wasu jerin hare-hare kwanakin baya a wasu ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar, wanda hakan ta tilasta wa Gwamna Simon Lalong ayyana dokar ta ɓaci a yankin.

Yayin da majiyarmu ta tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Matthias Tyopeɓ, ya ce ba zai ce komi ba har sai ya samu cikakken rahoto daga DPO mai kula da ƙaramar hukumar  ta Bassa.

Sai dai Shugaban Cibiyar Irigwe, Sunday Abdu ya shaida wa majiyarmu cewa, waɗanda lamarin ya rutsa da su sun samu mafaka ne a wata makarantar Firamare da ke ƙauyen, wanda kuma Rundunar ‘Operation Safe Haɓen’ ne suka samar musu da mafakar.

A ta bakinsa, “Abin da ya faru tamkar wani shiri ne na share mu daga doron ƙasa, saboda an kawo farmakin da ya yi sanadin rayukan mutanen da basu ji ba, basu gani ba. Sojoji ne suka kwashe mutanen suka kai su wannan makarantar Firamare don basu mafaka bayan wani farmaki da aka kawo mana a makon da ya gabata. A nan ne aka zo a ka yi wa musu kisan gilla.

“Muna kan shirye-shiryen yi bizne su a kabarain bai-ɗaya. Mun samu tabbacin mutuwar mutane 27 waɗanda an ƙirga gawawwakinsu. Duk da wasu sun ce an samo gawar wasu ƙarin mutum biyu, amma wannan ba a kawo mana gawawwakin ba tukunna.” Inji shi

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce, dole ne a daƙile wannan haukar domin maharani sun fara wuce gona da iri.

Kalaman na shugaban sun fito ne daga bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya ce, tuni shugaban ƙasan ya umurci jami’an tsaro, waɗanda suka haɗa da sojoji, da ‘yan sanda da su tabbatar da sun kawo ƙarshen wannan aika-aika, tare da samar da hanyoyin hana afkuwar wani abu mai kama da hakan a nan gaba.

Ya ce: “Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na iya ka ƙoƙarinsa wurin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kan Nijeriya, kuma ya na kira ga dukkan al’ummun ƙasa da su zauna da juna cikin lumana da zaman lafiya.

Sakamakon wannan ɗanyen aiki ne, ɗan majalisa mai wakiltar Jos ta Arewa da Bassa, Sulaiman Kwande ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tsaurara bincike bisa wannan lamari da ke faruwa, musamman ma a Masarautar Irigwe.

SendShareTweetShare
Previous Post

Badaƙalar NNPC: Ba A Taɓa Mazambaciyar Gwamnati Kamar Ta Buhari Ba –Lamiɗo

Next Post

Harin Filato: Dole A Taka Wa Haukar Nan Burki – Buhari

RelatedPosts

'Yan Adaidaita

An Sasanta Yajin Aikin ’Yan Adaidaita Bayan… Motocin ‘Kano Line’  Sun Koma Jigilar Jakara-Kasuwa

by Muhammad
1 week ago
0

Babu Hanunmu A Ciki Wannan Yaji – Shugaban ’Yan Adaidaita...

Adaidaita

Yajin Aikin Adaidaita: Acaba Ta Dawo A Kano

by Muhammad
1 week ago
0

Ya Jefa Jama’a Cikin Tsaka Mai Wuya Yadda Aka Koma...

Masu Garkuwa

Tattaunawa Da Masu Garkuwa: Yadda Gwamnonin Kaduna Da Neja Suka Raba Gari

by Muhammad
2 weeks ago
0

Shin Sheikh Gumi Ne Ya Raba Tsakani? Daga Nasir S....

Next Post

Harin Filato: Dole A Taka Wa Haukar Nan Burki – Buhari

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version