Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

Mummunan Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 20 A Bauchi

by Muhammad
January 11, 2021
in MANYAN LABARAI
1 min read
Mummunan
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya,

 

samndaads

Wani mummunar hatsari mota ya faru a Bauchi inda mutum 20 suka kone da har hakan ya jawo ba a iya gane fuskokinsu.

Bayan da wasu motoci guda biyu suka yi taho-mu-gama da junansu a kan babban hanyar Maiduguri zuwa Bauchi, nan take mutum 20 daga cikin 22 suka mutu, yayin da sauran biyun suka gamu da raunukan masu tsananin gaske.

An gano hatsarin wanda ya rutsa da motar Bas Hummer mallakin kamfanin sufuri ta jihar Borno wacce ta dauko fasinjoji 18 da nufin zuwa Maiduguri daga garin Jos inda suka kara da wata mota Golf wacce take tahowa daga karamar hukumar Misau zuwa cikin garin Bauchi dauke da fasinjoji hudu.

A lokacin da hatsarin ya faru wutar gobara ya tashi da motocin lamarin da ya kai ga kona fasinjojin da har ba a iya gano fuskokinsu kai tsaye, sai dai jami’an ‘yan kwana-kwana sun yi kokarin kashe wutar da har mata biyu daga cikin fasinjoji suka tsira da munanan raunukan a jikinsu.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin’yan sanda jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakil ya shaida cewar an kwashi gawarwakin mamatan zuwa dakin ajiye gawarwaki da ke asibitin koyarwa ta ATBUTH yayin da kuma mata biyu da suka tsira suke amsar kulawar likitoci a wannan asibitin.

Wakil wanda ya ce ba zai iya tabatar da menene musabbbin hatsarin ba zuwa yanzu, amma jami’ansu sun kai dauki cikin gaggawa bayan samun labarin aukuwar lamarin domin kai agaji ga wadanda lamarin ya shafa.

Zuwa aiko da rahoton ba mu samu wani cikakken bayani daga hukumar kiyaye haduta FRSC a jihar ba.

SendShareTweetShare
Previous Post

An Yaba Wa TAJBank A Kokarinsa Na Bunkasa Bangaren Ilimi

Next Post

Zaben Kananan Hukumomin Kano: Yadda Aka Tono ’Yan Kwaya A ’Yan Takara

RelatedPosts

Kawuna

Kawuna Ya Turo Ni Kano Don Yin Garkuwa Da Mutane, In Ji Maryam  

by Muhammad
1 day ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Maryam Muhammad, wadda ta shahara wajen...

Beli

Ka Sake Ba Ni Beli – Maina Ga Alkali

by Muhammad
2 days ago
0

Ya Ce, Da Gaske Ba Shi Da Lafiya Daga Khalid...

Bude Makarantu

Korona: Ba Ja Baya Ga Bude Makarantu – Gwamnatin Bauchi

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta...

Next Post
Ingantaccen zabe

Zaben Kananan Hukumomin Kano: Yadda Aka Tono ’Yan Kwaya A ’Yan Takara

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version