Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home TATTAUNAWA

Mun Aminta Da wakilcin Hon. Garba Datti Babawo – Alhaji Suleiman Yahaya

by Sulaiman Ibrahim
April 9, 2021
in TATTAUNAWA
4 min read
Mun Aminta Da wakilcin Hon. Garba Datti Babawo – Alhaji Suleiman Yahaya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Hon. Garba Datti Babawo na daya daga cikin ‘yan majalisar wakilai da suka fi dadewa a majalisa, haka kuma yana da nasaba da irin kyakaywan wakilcin da yake yi wa al’ummar mazabarsa ta Sabon Gari da ke jihar Kaduna, Editanmu Bello Hamza, ya ttaunawa da Alhaji Suleiman Yahaya, shugaban jam’iyar APC a karamar hukumar Sabo Gari, inda ya bayyana irin ayyukan raya kasa da Hon Datti Garba Babawo ya aiwatar a yankin na Sabon Gari, ya kuma nuna gamsuwar al’ummar karamar hukumar Sabon Gari akan irin wakilcin da Hon Datti Babawo yake musu, ga dai yadda hirar ta kasance.
Za Mu So Ka Gabatar Mana Da Kanka
Sunana Suleiman Yahya, shugaban jami’yyar APC na karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.
Wani tsokaci zaka yi akan yanayin wakilcin Hon. Garba Datti Muhammad Babawo, Wikilin mazabar Sabon Gari a majalisan wakilai ta kasa
Alhamdulillahi da ka yi maganar Babawo ai ka ce hantsi leka gidan kowa. Babawo jama’an Sabon Gari ba ma Sabon Gari kawai ba, jihar Kaduna gaba daya sun amince da wakilcin Babawo suna kuma amfana da abubuwan da ya kawo na cigaba a jihar. Saboda mutum ne mai rikon amana, mutum ne mai gaskiya. Idan ka duba zaka ga ya yi wa’adi da dama a majalisar jiha da na tarayya. Babawo ba Sabon dan majalisa bane duk kudurin da zai kawo zai kawo akan talaka ne akan abun da zai taimaki talaka. Misali a game da kudurin da ya kawo na maganan daidaita albashi na jihohi na ma’aikata kaga wannan kudiri ne mai kyau. Ni kan kaina kudurin da ya kawo ta shafe ni a game da karin albashi cewa Gwamna bazai iya biya ba sai ya rage albashi to misali ba zai iya biya ba sai ya rage ma’aikata misali yanzu da ace ya dauki dai yadda zai iya ne ya biya a kyale ma’aikatan. Ni da ana biya na dubu talatin da ace za a biya ni dubu goma sha biyar da zan yarda zan yi amma ace an rage ma’aikata akan albashi. Yakamata kudurin da Babawo ya kawo ya yi daidai da jihar Kaduna da Nijeriya gaba daya. Gwamna ya san karfin aljihun shi ya san nawa zai iya biya akan ma’aikatan shi domin yawancin jihohi din ba daya ake ba wata tafi wata karfi. Amma aka ce ayi bai daya sai an rage ma’aikata. To anan rage ma’aikatan kaga wa aka cuta? an cuci talakawa. Sannan su yan kwadago baza su iya bin diddigi ba. Akwai kungiyar Malamai ta NUT, don kuwa ni Malami ne sun bi diddigi sun bi diddigi a karshe suka barmu kara zube. Babu wani abu da ya faru. Kaga da ace sun yi hakuri an daidaita albashi daidai da yadda zai iya biya kaga da ba wadda za a rage. A namu ra’ayin ko a namu masaniyar mai girma dan majalisa Hon. Datti Muhammad Babawo Wallahi tallahi wakilin ne na gari. Ba zai kawo abin da zai cuci talakawa ba. Dalilin kenan da ya yi wa’adi mai yawa. Nan gaba muna sa ran ya zaman Gwamna. Saboda Mei? Mutum ne mai la’akari da abin da zai amfani talaka. Saboda idan kazo Sabon Gari zaka ga irin aikace aikace da ya yi.
Da kake maganar ana sa ran ya zama Gwamna, wasu ayyuka ne ya gabatar a matsayinsa na dan majalisa wadanda suka cancanci ya karfafa masa rike jiha?
Toh Alhamdulillahi da ka fadi hakanan. Babawo aikace-aikacen da ya yi. Wallahi tallahi idan na ce zan kawo maka su Wallahi sai in kai gobe war haka ban gama kawo maka su ba. In ka duba sabbabin kwalta da aka yi a cikin garin Sabon Gari wallahi dan majalisa nan shi ya yi, shi ne Gwamna mu, shi ne kansilan mu, shi ne chairman din mu shi ke komai. Idan ka duba asibitoci zaka ga kayayaykin da aka sa a cikin na zamani an kawo an sa. Bayan makarantu akwai nan Samaru zaka ga basu da “Secondary School’ yanzu idan kaje zaka ga ana gina sabon makarantar ‘Secondary School’. Toh duk Ho. Babawo ne ya kawo. Ire- iren wadannan bayan wuta da aka jawo a kauyuaau. Sannan ga tranfimomi da ya bayar a kwanakin baya. Bayan wannan akwai tallafi da yake yi. Akwai mata da aka basu kekunan dinki, da injinan saka. Sannan akwai matasa wandanda aka basu Keke NAPEP na neman kudi na neman sana’a kowa ya yi fito nema da kanshi. Shi Babawo ya dogara da talakawa domin mene? Talakawa suka tura shi suka ce yake ya yi masu aiki kuma aikin talakawa yake yi.
Me zaka ce game da tallafin da ake ba mata da matasa, ina aka kwana?
Toh tallafin da ake ba mata muna kara jadddada goyon bayanmu ga tallafin da ake ba mata. Kwanakin can akwai wani ‘workshop’ da aka yi aka koya ma mata sana’o’i, wadanda suka iya wadannan sana’an aka kawo jali aka basu, suma matasa akwai ‘workshop’ din da suka yi aka kawo jali aka basu. Kowanne akwai wanda aka bashi kusan dubu hamsin hamsin, dubu dari dari. Kowanne take ya inganta sana’ansu. Yadda za su dauki suma matasan wannan ya tada wannan wannan ya tada wannan.
Wani kira kake dashi ga al’ummar mazabar Sabon Gari? Na karin goyon baya ga wannan dan majalisa, musamman ganin irin wadannan ayyaukan cigaba da yake kawo wa.?
To muna kara kira ga ainihin mogaya baya, ba ma magoya bayan jam’iyyarmu ba kawai, dukkan jama’ar karamar hukumar Sabon Gari har da ‘yan jam’iyar adawa ta PDP da su kawo goyon bayan su ga Hon dati Babawo, musamman idan suka yi la’akari da cewa, Hon. Garba Datti Muhammad Babawo baya kyamar kowa, kowa nasa ne duk aikin da zai yi bawai zai ce ayi a gidan dan APC bane, a a kowa yana anfana. Kowa yana gani sannan yana takawa. Anan ne muke jaddadda goyon bayanmu ga mai girma Hon. Garba Datti Babawo. Da a kara bashi goyon baya a wa’adi na gaba, idan zai sake ya daura domin muna sa ran zai zama shuganan majalisa, Idan Allah ya yarda.
Ko akwai wani bayani da kake dashi ga al’ummar Sabon Gari musamman ‘yan jamiyyar APC wanda ban tambaye ka ba?
Alhamdulillahi, game da jamiyyar APC ina kira ga magoya baya. Bama son tashin hankali a zabukan da za su zo. A kwantar da hankali ayi abin da ya dace. Kowa namu ne saboda su kansu ‘yan adawa sun fahimci cewa wannan gwamnatin na ma’iakata ne domin me, Gwamna yana aiki ko ina da aka sani, ayi hakuri idan an baba wani bangare zuwa yanzu, ayi hakuri ana nan tafe.
Mun gode
Nima na gode

SendShareTweetShare
Previous Post

Shawara Zuwa Ga Ma’aurata Masu Husuma Da Masu Niyar Aure

Next Post

Waiwayen Kanun Labarai: Daga Litinin 22 Zuwa 25 Ga watan Sha’aban 1442 Bayan Hijira

RelatedPosts

Gari

Al’ummar Karamar Hukumar Sabon Gari Sun Amince Da Takarar Hon. Yusuf Salihu Shaka -Muntaka Umar Jega

by Muhammad
6 days ago
0

Editanmu Bello Hamza ya tattauana da Malam Muntaka Umar Jega,...

BIDIYO: Manyan ‘Yan Kasuwar Kano Sun Jinjinawa Dangote Kan Rashin Ƙara Farashi

BIDIYO: Manyan ‘Yan Kasuwar Kano Sun Jinjinawa Dangote Kan Rashin Ƙara Farashi

by Daurawa Daurawa
7 days ago
0

A cikin wannan hira za a ji yadda manyan 'yan...

NIRSAL

Shugaban ‘Yan Kasuwar Arewa Mazauna Abuja, Ya Yabawa Manajan Daraktan NIRSAL

by Sulaiman Ibrahim
2 weeks ago
0

Mataimakin shugaban yan kasuwar na Arewacin Nijeriya, wato ‘Arewa Traders...

Next Post
Waiwayen Kanun Labarai: Daga Litinin 22 Zuwa 25 Ga watan Sha’aban 1442 Bayan Hijira

Waiwayen Kanun Labarai: Daga Litinin 22 Zuwa 25 Ga watan Sha’aban 1442 Bayan Hijira

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version