El-Zaharadeen Umar" />

Mun Ba Ku Kwana Biyu Ku Mika Wuya – Masari Ga ’Yan Bindiga

Gwamnan jihar Katsina ta yi gargadin cewa zata dauki matakin ba sani ba sabo ga ‘yan bindigar da ba su mika wuya ba cikin kwanaki biyu tare da shan alwashin ba zata sake yin zaman sulhu da kowa ba

Gwamnan jihar Katsina Aminu Beloo Masari ya bayyana a ta bakin sakataran gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammadu Inuwa jim kadan bayan kammala wani taron gaggawa tare da ‘yan bindigar da suka mika wuya a thohon gidan gwamnatin jihar Katsina.

Dakta Mustapha Muhammad ya kara da cewa kuma dole ‘yan bindigar su saki wadanda suke tsare da su ba tare da wani sharadi ba kafin ayi amfani da karfin soja akan su.

“To mun gaya masu cewa wannan shi ne taro na karshe da za mu yi da su, domin a tattauna maganar sasanshi, ko dai su karbi zaman lafiya ko kuma abinda ake guje masu jami’an tsaro su zo su shiga don dole ma su amshi zaman lafiya. Kuma mun gaya mu su karara cewa wadannan mutane da suke da tsare da su musamman a wajan Jibia da Batsari da sauran wurarae da suke yin dauki dai dai daya kamar wajan Bakori to babu wani sharadi kawai su sake su dole daga nan zuwa yau alhamis du dawo da su,” in ji shi.

Kazalika sakataran gwamnatin ya ce za su dauki duk irin matakin da ya da ce akan wadanda suka ki amincewa da wannan shiri na zaman lafiya domin tabbatar da tsaro a yankin arewa masu yammacin Najeriya.

A cewarsa wadannan ‘yan bindigar suna neman sawa wankin hula ya kai gwamnati dare saboda yadda suke kokarin ganin sun hana ayyukan cigaban musamman a wuraran da suke tada karar baya da sace jama’a domin neman kudin fansa

Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya ce za su yi amfani da dukkan jami’an tsaro wajan tunkarar wadannan mutane domin a tabbatar da zaman lafiya a jihar katsina da bangaran arewa masu yamma musammnan Katsina da Zamfara da Kaduna da Sakwato da Kebbi da kuma Neja, akan haka babu wata maganar sassautawa acikin wannan al’amari.

Dakta Mustapha Muhammad yana mai cewa hakurin gwamnati ya kusa karewa saboda haka wannan taro da suka yi da ‘yan bindiga alamu na nuni da cewa an zo gargara.

Sannan ya ce suna godiya ga wadanda suka rungumi shirin zaman lafiya kuma suke taimakawa jami’an tsaro da gwamnati wajan ganin an samu nasarar da ake bukata a wannan yaki da ake yi da masu tada kaya baya.

Matsalar tsaro a jihar Katsina na cigaba da dauka sabon salo, duba da irin sulhun da gwamnati ta ce ta yi da ‘yan bindiga amma har yanzu abin yaki ci yaki cinyewa lamarin da yanzu ake tunani daukae matakin soja kamar yadda gwamnati ta yi ikirari.

Exit mobile version