Mun Ba ’Yan Nijeriya Kunya, In Ji Salisu Yusuf

Mai koyar da yan wasan tawagar kasar Super Eagles ta Nijeriya, Salisu Yusuf ya ce yan wasan kasar sun yi abin kunya bayan da kasar Morocco ta lallasa su daci 4-0 a wasan karshe na cin kofin nahiyar Africa na yan wasan cikin gida.

Tawagar kwallon kafa ta kasar Morocco ta lashe gasar cin kofin Afrika ta ‘yan wasan da ke taka leda a gida wato CHAN bayan ta lallasa Nijeriya da ci 4-0 a wasan karshe da suka fafata a jiya a birnin Casablanca.

Yanzu haka Morocco ta shiga sahun kasashen Jamhuriyar Demokradiyar Congo da Tunisia da Libya da suka taba lashe wannan kofin.

Dan wasan Morocco Ayoub El Kabi ya taka gagarumar rawa a nasarar da kasar ta samu, in da aka ayyana shi a matsayin gwarzon gasar baki daya, yayin da ya fi kowa zura kwallaye a gasar ta bana, in da ya ke da kwallaye 9.

Sakamakon rawaar da ya taka, ana ganin watakila kocin tawagar kasar ta Morocco, Herbe Renard zai ba shi damar buga wa kasar gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakwanci a bana, in da za su kara da Iran da Portugal da Spain acikin rukuni

Baya ga kofin na CHAN da Morocco ta lashe, har ila yau, an bai wa ‘yan wasan kyautar Dalar Amurka miliyan 1.25.

 

Exit mobile version