Shafiu Saleh" />

Mun Bada Scholarship Ga Dalibai Sama Da 500 – Wakili Boya

BARISTA ALIYU WAKILI BOYA, shi ne shugaban karamar hukumar Fufore, Sarkin matasa Adamawa kuma shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin jihar (ALGON), ya gana da manema labarai  a gidansa, jimkadan bayan nadashi a matsayin Sarkin Matasan Adamawa da masarautar Lamido Barkindo Aliyu Mustafa ta yi, ranar Asabar da ta gabata, wannan fassarar ganawar ce kamar yadda SHAFI’U SALEH ya rubuto mana.

Ko zaka gabatar mana da kanka?

Sunana Barista Aliyu Wakili Boya, shugaban karamar hukumar Fufore Sarkin Matasan Adamawa, shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin jihar Adamawa ALGON.

Masarautar Lamido Adamawa, ta nada ka a matsayin sarkin matasan Adamawa ya kaji da hakan?

To, na farko dai na godewa Allah mamallakin mamallaka mai kowa mai komai, wanda shi ne yake bada sarauta a lokacin da yakeso ga wanda yakeso, na biyu kuma na yi matukar farin ciki da daukaka da mukamin da Allah ya bani, wanda mai martaba Lamido Adamawa ya tabbatar min dashi, kuma gashi an gudanar da buki lami-lafiya ba tare da an samu wani matsala ba, wannan ya bani farin ciki matuka.

 Bisa la’akari da yanayin da matasa ke ciki ta yaya kakejin zakayi amfani da wannan dama wajen ganin ka taimaki matasa?

To, kamar yadda na ce muku godiya ta tabbata ga Allah da ya bani wannan mukamin, kuma godi ta musamman ga Lamido Adamawa wanda ya ga cancantana da kuma ya ga kamar zan iya ya bani wannan mukamin kuma in Allah ya yardaba zan bashi kunya ba, domin tun ada ma ni kam na matasa ne kafin mai martaba ya bani wannan mukamin, so, wannan zai kara jadadda mini da kuma karfin gwiwar in tsaya inga na taimaka na agaza wajen ganin rayuwar matasa ya canju da fanni daban daban, ta fannin karatu da aikinyi da kuma yadda za mu gyara matsalar shaye-shayen  da matasa ke yi dama aikata wasu abubuwan da basu dace ba.

Guguwar siyasa ta fara kadawa kuma ‘yan siyasa kanyi amfani da matasa a irin wanann lokaci, akwai wata rawar da zaka iya takawa kan wannan matsalar da wannan kujerar?

Eh, insha Allahu Rabbiy za mu yi kokari, domin matasa su ne kashi saba’in bisa dari kuma yanzu lokaci ne na matasa, za mu yi kokarin ganin matasa sunci moriyar tafiyar siyasa domin su suke wahala su suke zabe su suke kamfe, su suke hana magudin zabe su hana tashin hankali a lokacin zabe, to bai kamata a gama zabe ace kuma su suke baya, za mu tabbatar sun amfana.

Jam’iyyar APC ta zo da taken canji, ya zaka kwatanta canjin da gwamnatin ta yiwa rayuwar matasa cikin shekaru uku?

Eh to, a gaskiya fisabilillahi kowa yasan jam’iyyar APC da gwamnatin Janaral Muhammadu Buhari, da na gwamna Muhammadu Bindow sunyi kokari, sun kawo abubuwa da yawa wanda ya canja rayuwar talakawa musamman matasa, kuma in ba domin abun ya dade shekaru da dama ba’adauki matakin taimakawa talaka da matasa ba, da yanzu abubuwan da’akayishi cikin shekara uku zaka ganshi a fili, amma da yake gwamnatin ta zo ta samu akwai abubuwa da yawa, wahalhalu da rashin aiki yayi yawa ga kuma karancin kudin shiga, to shi yasa duk kokarin da gwamnatin tarayya da ta jiha sukayi ba za’a ganshi a fili yanzu ba, Hausawa sunce idan Danbo ya yi yawa bayajin mai, sun samu basussuka ya yi yawa saboda haka akwai matsala, amma gwamnatin tarayya da na jiha, ba karamin kokari sukayi ba wajen kyautata rayuwar matasa.

Daga lokacin da ka shiga ofis a matsayin shugaban karamar hukumar Fufore, kamar me kayi domin kyautata rayuwar matasa ko ince jama’arka?

Alhamdulillah, tun ina shiga ofis na farko na kafa kwamitin da’ake cema, Poberty Allubiation Youth and Women Empowerment Program, wanda mun samu hazikan mutanen da suka san abinda ya kamata suka rike kuma sunyi bakin kokarinsu akan, sun bi ward na 11 sunyi magana da matasa, sunyi kwamiti sun dauki yadda za’a taimaka ta fannin noma da yadda za’a taimakawa yaran ‘yan makaranta (Scholership) ta fannin yadda za’a baiwa wasu jari, da yadda wasu zasu samu aiki da kuma abubuwan da zai kawo ci gaba a wajen matasa, kuma Alhamdulillah, ta fannin noma mun samu mun bude gona hectare yafi dari, matasa sama da dari biyar muka basu horo kan harkar noma, mun taimaka musu da kayan noma da iri, bayan haka kuma munyi kamar S.A program, yara matasa da yawa suna dan samun wani abu kowani wata, a yanzu haka yaran da sukaci moriyar Scholarship sunfi dari biyar, kuma za mu ci gaba yi ga ‘yan makaranta a makarantu daban daban ta yadda ‘yan Diploma da masu Degree, haka kuma ta fannin Kiwon lafiya munyi wani program na free soldering wanda indai mutum yazo yana da matsala na tiyata ne za muce aje ayi mishi kyauta a asibitin Fufore, yanzu haka mutum kusan dari biyu sun amfana da shirin ana ci gaba da yinsa yanzu haka, kuma ta fannin wasanni mun shirya gasar kofin Ciyaman (Chiarman Coup), mun kira dukkan wards dinmu sunzo Fufore sun yi sama da sati biyu, sunyi wasa anyi lafiya an  gama lafiya kuma Club-club na wasannin mun basu abubuwa yadda zai taimaka musu su ci gaba da wasannin domin yana kawo hadinkai na matasa, akwai abubuwa da dama wanda mukayi ko muke ci gaba da yi, wanda kuma yana taimaka musu yana agaza musu, domin wannan nauyin na mu ne  ni matashi ne ba zanso ace matasa basu mori wannan tafiyar ba.

A matsayin ka na Sarkin matasan Adamawa ya ka ji da halartan taron rantsar Sakai da Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya yi?

Na farko dai duk abinda zakayishi a rayuwa ka yi shi tsakaninka da Allah, na biyu duk abinda zakayi in kana yi da mutane akwai ranar su, don dan Adam Allah ya yi shi mai daraja ne so, duk lokacin da kake baiwa dan Adam daraja Allah zai baka daraja, ni kuma Allah yayini ina daraja mutane, shi yasa nima idan lokaci na in yazo abinda na ke so sai Allah yana bane wannan darajan, duk abinda na nema Allah zai taimakamin, don haka aran da na je gurin mai martaba Sarkin Kano na rokeshi nace ga abinda na ke ciki ga abinda kuma na ke son yamin, ya amince domin ba’atabayi a tarihi ba, amma bayan munyi hira dashi wajen sa’a guda ya fahimci manufofina da niyyana da programs da na ke dashi a Sarkin matasa, a take ya kira shugaban ma’aikatansa, na farko dai ya gayamishi masarautar Kano za ta yi sarakunan matasa diga matakin jihar zuwa kananan hukumomi harkan dagaci zasu yi, ya kuma tabbatar cewa abin yana da muhimmanci, kuma yace idan anzo taron sarakuna a Arewa House zai kawo batun cewa duk sarakuna su je suyi sarakunan matasa domin zai taimaka a yanayin da muke ciki, to da Sarkin Kano yaga muhimmancin taron yace zai bar duk abinda yake yi ya halarci gayyatar da na yi mishi, kuma in Allah ya yarda zaizo Yola zaiyi abinda ba’atabayi ba, kuma yazo dashi akayi komai na taron saida aka gama Kilesa sannan mai martaba ya tafi, kuma daga nan ya wuce Paris, kaga saboda muhimmancin program din ya jinkirta tafiyarsa saida ya halarta, yazo son ya nuna mana soyayya ya tabbatar mana shi yana tare da matasa, domin ya gane manufofina da soyayyan da na ke yiwa matasa shi yasa yace idan Allah ya yarda zaiyimin abinda na ke so, domin yasan ina da manufofi masu kyau wanda in an bani dama zan taimakawa matasa sosai, shi ne dalilin da yasa yazo ya karya protocol na masarauta ya kuma ce baiyi damar hakan ba, yace tun da Allah ya bashi sauratarnan baije program da yaji dadi  kamar na mu na Sarkin matasan nan ba.

Daga karshe manene sakonka ga matasa a Adamawa?

Sakona ga matasa na farko dai matasa mu nitsu domin wannan lokacin mu ne, wadanda suke makaranta su tsaya suyi karatu na gaske, masu sana’a su rike sana’arsu, mu daina shaye-shaye da wadansu ayyukan ash sha ba namu bane, don ana cewa yara manyan gobe to goben ta zo fa, yau dinnan itace goben da’ake fada mana bai kamata mu yarda wani abu yazo ya bata mana rayuwa ba, yanzu lokacin mu ne, saboda da haka ina rokon matasa mu nemi sana’a mu hadakai mu yi biyayya, kada mu yarda ayi amfani mu ta wasu abubuwa ko domin siyasa ko don bukatar wani ya biya ko kuma abaka kudin da bai taka-kara ya karya ba ka ci mutunci ko ka zagi wani babban ko kaje kana zage-zage a Facebook ko a inama bai kamata ba, mashi lokaci ya yi da za mu yi abinda zai amfanemu, abinda zai amfani jiharmu da abinda zai amfani kasar mu baki daya, yanzu ba lokaci ne da za’ayi amfani damu abamu taro ko sisi ace muyi wani abu wanda zaici zarafin wani ko wasu ba, lokaci ne da muma za mu ga mun bada gudumuwa a ci gaban jiharmu da kasarmu muga munyi abinda ya dace wanda ya kamata, amma idan munje mun shiga wahala ba zai kaimu ko’ina ba, ba za mu ci gaba ba, kuma ba zaisa mu ci moriyar gwamnati ba.

 

Exit mobile version