Connect with us

LABARAI

Mun Bankado Yunkurin Kai Hari Da Sunan Dogara, Inji Iliyasu Zwul

Published

on

A Jiya ne wasu da suka kira kansu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a kananan hukumomin Dass, Bogoro da kuma Tafawa Balewa suka bayyana cewar sun gano wata shirin da aka kimtsa inda za a yi amfani da wasu matasa ‘yan daba da ‘yan sara-suka domin kai hari ofisoshin jam’iyyar APC a mazabar Dogara daga nan kuma a akala daukan nauyin hakan wa Dogara.

Kungiyar masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, sun bayyana haka ne a sakatariyar ‘yan jarida da ke Bauchi, inda Honorabul Iliyasu Zwul da Dakta Abdu Gani suka yi bayani wa manema labaru a madadin mambobin kan shirin da suka bankado.

Da yake tasa jawabin, Honorabul Iliyasu Zwul cewa, yake yi, wannan shirin an yi ne kawai da nufin bata wa Kakakin Majalisar tarayya suna a idon duniya, inda kuma ya yi zargin cewar daga bisani ne kuma sai a yi amfani da damar wajen korarsa daga jam’iyyar APC.

Ta bakinsa; “Muna da labarin an shirya da wasu ‘yan daba, ‘yan bangan siyasa da nufin za su je su tayar da zaune tsaye a mazabar Kakakin majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, na Dass, Bogoro da Tafawa Balewa. Idan sun kai wannan harin a wannan yankin, ba ko’ina za su nufa ba, illa za su kai hari ne ofisoshin jam’iyyar APC ne a wannan kananan hukumomi uku. Idan suka tayar da wannan rigamar za a laka a ce shi Yakubu Dogara ne ya dauki nauyin kai wannan harin,” In ji Zwul.

Ya ci gaba da cewa; “Don haka ne wasu za su yi amfani da wannan damar wajen bata masa suna, kuma a koreshi a jam’iyyar APC. Ganin wannan ne, a matsayinmu na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a wannan yankin, muka ga bai kamatu mu yi shiru ba, don haka ne muke sanar da duniya wannan shirin da aka kitsa,” Kamar yadda Iliyasu ya bayyana.

Ya ce, baya ga nan kuma, suna sanar da dukkanin masu wannan yunkurin da cewar suna da masaniya kan shirinsu, inda ya bayyana cewar wannan yunkurin ba zai taba kaiwa ga nasara ba.

Ya kara da cewa; “Shi Kakakin Majalisar Tarayya mutum ne mai son ci gaba, mutun ne mai son zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya kawo mana ci gaba sosai a cikin al’ummarmu, kuma mutum ne mai dumbin masoya, don haka kitsa irin wannan da sunansa matsalace, domin kowa ko a siyasa ta gaba Dogara ya fito jama’a za su zabeshi,” A ta bakinsa.

Ya bayyana cewar wannan yunkurin ya fitone daga wasu wadanda ba su son kawo ci gaba wa jama’a, “Irin wannan zai taimaka wajen kauda hankalin Dogara daga aiyukan alkairi da yake yi, mu kuma ba za mu so haka ba. don haka ba za mu amince wasu su kokarin dakile ci gaba ba. domin abubuwa da dama sun faru a baya, akwai lokacin da Dogara ya yunkura kawo asibitoci da massalatai a wasu yankuna aka zo aka hana a jihar Bauchi, kunga babu wani mai kishin jihar nan da zai hana hakan,” in ji Honorabul Iliyasu Zwul.

A tasa bangaren, Dakta Audu Gani ya bayyana cewar tun bayan da suka samu wannan rahoton shirin masu kitsawan ne suka dauki matakin sanar da hukumomin tsaro domin daukan mataki, sai dai bai bayyana wa manema labaru wadanda suke zargi da shirya wannan lamarin ba, illa dai ya bayyana cewar wasu ‘yan sara-suka ne da aka dauki hayansu da nufin gudanar da wannan aikin don bata wa Dogara suna a idon duniya.

Audu ya bayyana cewar wanna shirin da aka kitsa ba zai taba kaiwa ga nasara ba, domin kuwa Dogara mutum ne da jama’an yankin ke matukar so, kuma suna da masaniyar dukkanin abun da zai yi da wanda ba zai yi ba.

Audu Gani ya sanar da jama’an jihar Bauchi kan wannan shirin inda ya nemi su hada kai wajen yin tofin Allah wadai ga masu neman tada husuma a jihar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: