Umar A Hunkuyi" />

Mun Bijire Wa Batun Samar Da Filayen Kiwo –Gwamnonin Kudu Maso Gabas

Gwamnonin kudu maso gabashin kasarnan sun kammala taron da suka yi ranar Lahadi a Enugu, inda suka cimma matsayar da ke cewa, ba wani fili daidai da taki da za su bayar a yankunan nasu domin wai a kafa wuraren kiwo na zamani a cikinsu.

Taron, wanda gwamnonin suka yi a gidan gwamnatin Jihar ta Enugu, ya sami halartar Gwamnan Jihar ta Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, Gwamnan Jihar Ebonyi, Dabe Umahi, yayin da gwamnonin Jihohin Abiya da Anambra, mataimakan gwamnoninsu suka wakilce su.

Amma Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, bai halarci taron ba, bai kuma turo kowa ba.

Babban shugaban kungiyar al’ummar Ibo ta, Ohanaeze Ndigbo, Cif Nnia Nwodo, ne ya gabatar da tsarin kungiyar na su kan batun na ‘sake fasalin kiwo’ a wurin taron da ya kai har daren lahadin ana yin sa.

Da yake magana da manema labarai bayan taron, shugaban kungiyar gwamnonin na shiyyar kudu maso gabas, Umahi, ya bayyana cewa, gwamnonin sun cimma matsaya a kan, ba za su bari a kafa wuraren kiwon a yankunan na su ba.

Umahi ya bayyana cewa, rahotannin da ke ta yawo masu nu ni da cewa, wai Jihohin shiyyar ta kudu maso yamma sun bayar da filayen da za a kafa wuraren kiwon kamar yadda gwamnatin tarayya ta nema, duk kanzon kurege ne.

Umahi ya ce, gwamnatin ta tarayya ma ba ta nema ba, ko ma ta nema ba za su bayar da filayen ba.

“Sam gwamnonin kudu maso gabas ba su yarda da kafa wuraren kiwon ba a yankunan na su,” in ji Umahi.

Hakanan, a wurin taron, gwamnonin sun yi tir da kashe-kashen da ake yi a Jihar Filato, inda suka nemi da, “A yi wa mutanan na Filato adalci.”

Gwamnonin kuma sun yi gargadi kan abin da suka kira da barazanar da ke tattare da kwararan makiyayan yankunan kudu maso gabashin na kasarnan.

Inda suka yi matsaya kan ganawa da shugabannin jami’an tsaron kasarnan kan lamarin.

A bisa takardar da hadaddiyar kungiyar ta su ta Ohanaeze, ta gabatar, gwamnonin na kudu maso gabas, sun jaddada matsayin su na a sake fasalin zamantakewan kasarnan.

“An gabatar da matsayar Ndigbo a kan sake fasalin zamantakewar Nijeriya ga kungiyar gwamnonin ta kudu maso kudu, wanda shugaban kungiyar Ohanaeze ya gabatar, bisa tattaunawar da suka yi da sauran al’ummun yankin na Igbo a garin Awka.

“Shugaban na Ohanaeze ya gabatar da abin da suka tattaunan ga gwamnonin. Kungiyar gwamnonin kuma ta yi ma Ohanaeze godiya kan aiki nagarin da ta yi, gwamnonin kuma sun sake jaddada matsayar su na cewa, sake fasalin zaman Nijeriyan shi ne kadai mafita ga ci gaban Nijeriya.

 

Exit mobile version