Ministan ma’aikatan ayyuka da gidage, Babatunde Fashola ya bayyana cewa, gwamanatin tarayya ta kammala biyan dukkan kudaden da gwamnatin jihohi ke bin ta bashi na gyaran hanyoyi mallakar gwamnatin tarayya. Haka kuma ya bayana cewa, a yanzu haka gwamnatin tarayya yana ginawa da kuma gara hanyoyi wanda ya kai kilomita 35,000, inda a yanzu haka ta samu nasarar kammala kilomita 13,000 na hanyoyin tarayya da ke fadin kasar nan. Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da ake fira da shi kai tsaye a wani shiri na gidan talabijin da ke garin Abuja.
Lokacin da aka tambaye shi ko dai gwamnatin tarayya za ta ci gaba da amincewa gwamnatocin jihohi su gyara hanyoyi mallakar gwamnatin tarayya daga baya ta biya su, ministan ya amsa da cewa.
“Hakan ba zai yuwu ba a halin yanzu, domin an bayar da umurni a kan haka. Haka kuma su ma gwamnatocin jihohi suna da na su hanyoyin wanda har yanzu ba su kammala ba, ya kamata su mayar da hankali a kan gyaran hanyoyinsu kafin su zo na gwamnatin tarayya.
“Shugaban kasa ya bayyana cewa, na gaji basuka daga gwamnatin da ta gabata na gyaran hanyoyin gwamnatin tarayya masu yawan gaske, amma a yanzu ina farin ciki da kammala dukkan wadannan basuka da na samu.
“Idan mutane suna cewa muna amso basukan kudade, ba su san cewa muna biyan basukan da muka gada daga gwamnatin da ta shude, inda suka yi amfani da kudaden da muka samu wajen biyan basukan hanyoyin,” in ji Fashola.