Mun Biya Kudin Tallafin Karatun Da Gwamnatin Kwankwaso Ta Kasa Biya – Ganduje

Dala

Daga Abdullahi Muhammad Sheka

Gwamnatin Kano ta ce ta kashe Naira Biliyon daya da Miliyon dari takwas wajen biyan kudaden tallafin karatun daliban Jihar Kano da ke karatu a jami’o’i masu zaman kansu a fadin kasar nan da Gwamnatin bayan ta kasa biya. Kamar yadda Babban Daraktan yada labaran Gwamnan Jihar Kano Abba Anwar ya shaidawa LEADERSHIP A Yau.

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahu Umar Ganduje ne ya bayyana haka a yayin mika shahada ga dalibai 20 ya yin zaman majalisar zartaswa ta Kano a ranar Laraba data gabata.

Daliban da aka mikawa shaidar sun kammala karatunsu ne a jami’ar AUN Yola, inda biyu suka samu shaidar kammala karatu ta farko wato (first class) ya yin da 18 kuma suka samu mataki na biyu.

A cewar Ganduje zaliban suna cikin wadanda tsohuwar Gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso ta dauki nauyin karatun su, amma ta biya musu kaso goma ne kawai na abin da ya kamata a biya.

A cewarsa sai da Gwamnatinsa ta zo ne kuma ta bibiyi al’amarin ta kuma ci gaba da biyan kudin daliban.

Jamio’in da Gwamnatin ta tura daliban sun hadar da American Unibersity of Nigeria (AUN) Yola, sai kuma Jami’ar Crescent da jami’ar Alkalam da ke Katsina, da kuma jami’ar Bells  da ta Igbinidiom Okada.

Da ya ke taya daliban da suka kammala murna,  Gwamnan ya bukaci su yi amfani da abinda suka koya yanda ya da ce ta yadda al’umma za su amfana da su.

Exit mobile version