Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta fitar da sanarwa cewa, ta kama wanda ya kashe Shugaban Jam’iyyar APC, Marigayi Philip Tatari Shekwor, ya kuma tabbatar da cewa shi ya aikata wannan danyen aiki da kansa.
Rohotun ’yan sandan ya zo ne bayan kwana hudu da sojoji su ka ba da sanarwa cewa, sun kashe mutum uku tare da kama mutum tara, wadanda su ka kashe Shugaban na APC.
Shi ma Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullah Sule, ya bada sanarwar kama madugun masu garkuwa da mutane, wanda ’yan sanda su ka ce shi ne ya kashe Shugaban jam’iyyar ta APC.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da a ke tsaka da taron yaye matasan da su ka samu horon koyon kasuwanci da sana’a ta a gaban Babban Bako kuma Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Gwamnan ya ce, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Mista Bola Longe, ya sanar da shi cewa, rundunar ta kama madugun da ya kashe Shugaban APC a ranar 21 ga Nuwamba, 2020, a gidansa da ke Lafia.
An dai kashe Marigayi Philip Tatari Shekwor ne a ranar Asabar da daddare a garin Lafia, inda a ka yi jana’izarsa ranar Juma’a 27 ga Nuwamba, 2020, a kauyensu da ke garin Yalwa cikin Karamar Hukumar Toto.
Sai dai ranar da a ka yi jana’izar mamacin, Gwamna Sule ya bada sanarwar cewa, Rundunar Soja ta ce ta kashe mutum uku, sannan ta kama mutum tara, wadanda su ka kashe Shugaban jam’iyyar ta APC.