Hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa ta EFCC ta fara binciken wasu jami’o’i masu zaman kansu da ta ke zargin na bogi ne a kasar nan, hukumar ta tabbatar da hada gwuiwa da hukumar jami’o’in kasar nan domin gano hanyar dakatar da wadannan jami’o’i da suke aiki ba bisa ka’ida ba ko lasisin gwamnati.
Shugaban riko na hukumar EFCC Ibrahim Magu, a yakin da ya ke na takawa cin hanci da rashawa birki a fadin kasar, Shugaban ya sanar da hakan a yayin da ya ziyarci hedikwatar kamfanin jaridar LEADERSHIP dake Abuja, a ranar talatar makon jiya, yace wannan binciken zai kawo saukin ta’annuti da wasu jami’an gwamnati suke yi wajen amfani da jami’o’i wajen azurta kansu.
Magu, ya ce, hukumar ta yi matukar damuwa da yawan bude wadannan jami’o’i na bogi a kasar nan, wanda suke tatsar kudade daga hannun iyayen yara ba bisa ka’ida ba.