Balarabe Abdullahi" />

Mun Fara Kidayar Gwaji Ne: Domin Ga Ne Yawan Al’ummar Nijeriya Da Kuma Gidaje – Durunguwa

Babban kwamishinan hukumar kidaya ta kasa  [NPC] a tarayyar Nijeriya, Dokta Abdulmalik Ibrahim Durunguwa ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, a fadarsa, jim kadan bayan kammala kaddamar da fara kidayar al’umma da kuma gidaje da hukumar ta fara a wasu kananan hukumomi a tarayyar Nijeriya.

Dokta Abdulmalk ya ci gaba da cewar, saboda muhimmancin sanin yawan al’umma da kuma gidaje ne, a cewarsa, hukumar kidaya a Nijeriya ta zabi wasu kananan hukumomi 28 a sassan Nijeriya, wabda, kamar yadda yace, a cikin kananan hukumomin , a kwai kananan hukumomi biyu a jihar Kaduna da suka hada da Kagarko da kuma karamar hukumar Zariya.

A dai jawabinsa, Dokta Durunguwa ya nuna matukar jin ddinsa da kuma gamsuwa na yadda mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, ke bakin kokarinsa wajen bayar da gudunmuwa a duk lokacin da hukumar kidaya ta kasa ta yunkura, domin gudanar da kidayar al’umma a Nijriya, wannan ne ya sa, kamar yadda ya ce jihare Kaduna ke zama na daya ko kuma na biyu ya zuwa na uku, a duk lokacin da aka motsa domin gudanar da kidaya da aka saba yi .

A nan sai babban kwamishinan kidaya a tarayyar Nijeriya mai kula da jihar Kaduna ya yi kira ga sauran sarakunan a Nijeriya su ci gaba da koyi da mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, na tashi wajen ba wannan hukuma duk goyon bayan da ta ke bukata day a shafi wayar wa al’umma da kai, na muhimmancin kidayar da kuma a yadda al’umma da kan su za su hada hannu da wannan hukuma, domin samun nasarar da ta ke bukata a duk lokacin da ta tsara ayyukan da ta saw a gaba.

Da kuma Dokta Abdulmalik Durunguwa ya juya ga ma’aiktan da za su gudanar tare da aiwatar da ayyukan da hukumar ta tsara, sai ya yi kira ga daukacin ma’aikatan da lallai su bi dokokin da aka dora ma su bisa tsari, domin gudun ka da a sami matsaloli a farko ko kuma a karshen ayyuykan da za su yi a karamar hukumar Zariya.

A jawabinsa, mai martaba Sarkin Zazzau, AlhaJI Shehu Idris, nuna godiyarsa ya yi da farko ga mahukumtan wannan hukuma ta kidaya, na yadda suka sa karamar hukumar Zariya a cikin kananan hukumomi 28 a Nijeriya da Za a yi kidayar gwajin a cikinsu.

Alhaji Shehu Idris ya kuma tabbatar wa mahukumtan wannan hukuma cewar, zai ci gaba da ba wannan hukuma duk goyon bayan da suke bukata, domin su sami damar samun nasarar da suke bukata, na wannan kidaya da aka fara a karamar hukumar Zariya da kuma sauran kananan hukumomi da suke sassan Nijeriya baki daya.

Sauran wadanda suka yi jawabi a wajen kaddamar da fara kidayar, sun hada da jami’in hukumar zabe mai kula da karamar hukumar Zariya dad a kuma mataimakin shugaban karamar hukumar Zariya, Malam Aliyu Altukri, wanda ya bayar da tabbacin dambar da karamar hukumar Zariya ta dora na ba ma’aikatan da hukumar ta turo su karamar hukumar Zariya, domin su aiwatar da ayyukan da aka dora ma sun a kidayar al’umma da kuma na gidaje da sukew yankin.

Exit mobile version