Abba Ibrahim Wada" />

Mun Fasa Sayar Da Sancho, Cewar Dortmund

Kungiyar kwallon kafa ta Dortmund ta bakin babban daraktan kungiyar, Machael Zorc, ta bayyana cewa ta fasa sayar da dan wasa Jardon Sancho kuma zai ci gaba da buga wasa a kungiyar har zuwa kakar wasa mai zuwa

Tuni dai kungiyar ta sanya sunan dan wasan mai shekara 20 cikin jerin wadanda za su yi atisaye a sansanin kungiyar da ke Switzerland kuma wannan na zuwa ne a daidai ranar da kungiyar ta tsayar domin kammala cinikin Sancho, wanda shi ne babban dan wasan da Manchester United ta sanya a gaba a wannan kakar.

Daman dai kungiyar ta Borussia Dortmund tana shirin kara bawa dan wasan sabon kwantiragi domin ya ci gaba da zama a kungiyar idan har Manchester United ta kasa biyan abinda kungiyar take bukata.

Manchester United dai ta kai tayin kudin da yakai fam miliyan 89 domin kungiyar ta kasar Jamus ta sallama mata matashin dan wasan dan asalin kasar Ingila mai shekara 20 bayan da kungiyar ta samu tikitin buga gasar cin kofin zakarun turai na shekara mai zuwa.

“Mun gina kungiyar mu da Sancho a wannan kakar  saboda haka mun fasa sayar dashi ga kowacce kungiya wannan kuma ita ce matsayar mu ta karshe ina kuma ganin hakan zai amsa dukkan tambayoyi.” In ji Zorc

Ya ci gaba da cewa “A bara muka kara masa albashi domin ya yi daidai da kokarin da yake domin haka, a fakaice mun kara kwantaraginsa ne zuwa shekara ta 2023 sannan mai koyarwa yayi lissafi dashi a bana.”

Kungiyar da ke buga Bundesliga na neman fam miliyan 100 ne kan dan wasan na Ingila, wanda suka dauko daga Manchester City a 2017 kan kudi fam miliyan 10 kuma Dortmund ta tsayar da lokacin da ta ke bukata a kammala wannan cikinki tsakaninta da Manchester United, saboda ta mayar da hankali kan shirye-shiryen sabuwar kakar da za a shiga ta 2021 da 2022.

Za a fara sabuwar kakar wasanni a Budesliga a ranar 18 ga watan Satumbar gobe, yayin da za a rufe kasuwar musayar ‘yan wasa a ranar 5 ga watan Oktoba hakan yana nufin har yanzu akwai lokacin da kungiyoyin biyu za su ci gaba da tattauna wa duk da matsayar Dortmund din.

 

Exit mobile version