Mun Fatattaki Maha’intan Daga Kasuwar PZ — Shaibu Ibrahim Zafi

Daga Idris Umar, Zariya

Alhaji Shaibu Ibarhim Zafi shi ne shugaban masu sayar da wayar salula da ke PZ Sabon garin Zariya a Ƙaramar hukumar Sabon gari Jihar Kaduna.

A ranar Larabar nan ce shugaban na masu sayar da wayar salular ya shaida wa manena labaru halin da Ƙungiyar tasu take ciki a yanzu, musamman ta ɓangaren ci gaman da suka  samu a tsawon shekaru bakwai zuwa takwas da suka  gabata. Amma daga farkon ya fara ne da godiya ga Allah maɗaukakin sarki da har ya ba shi ikon riƙe shugabancin Ƙungiyar cikin nasara da samun cigaban Ƙungiyar bakin ɗaya daidai gwargwadon iko, duk da ƙalubalen da harakar sayar da waya ke da shi kamar yadda kowa ya sani a faɗin Ƙasar nan.

Bayan haka ya ce, sunan Ƙungiyarsu ta masu sayar da waya da ke PZ shi ne, P Z Molti parpors Coopratiɓe Sociaty Limited Zariya, wacce ta haɗa mutane daga garuruwa da dama Zariya da kewaye Kaduna da Kano har jihar Katsina babu jama’ar da ba su a wajan. Kuma shugaban ya bayyana cewa, a lokutan baya sun sami matsaloli da dama ta ɓangare mutane masu rashin gaskiya da suka yi wa sana’ar tasu katutu wanda ya kai ga mafi yawan mutane ba sa amincewa da zuwa sayen waya a nan PZ Zariya. Kuma ga shi mun fi ko’ina arhar wayar da sanin ita kanta wayar salula a ɓangaren gyaranta. Amma saboda kallon da mutane suke wa wasu daga cikinmu sai hakan ya sa muna samun matsala takowane ɓangaren ga rashin gamsuwa da mutane keyi da halayenmu ga matsi da muke samu wajan jami’an tsaro. Saboda duk lokacin da aka yi satar waya a wani waje sai kawai a taho PZ Zariya hakan ya sa ɓarayin ma da sunyo satar wayar sai kawai su nuho PZ Zariya da wayar don su goga maan kashin kaji.To don wani lokacin za ka ga da ɓarawo ya ji dukan jama’a ko jami’an tsaro sai ka ji ya ce PZ ya kawo wayar ya sayar, bisa hakan sai ka ga an zo ana mana wulaƙanci wasu ba su san hawa ba ba su san sauka ba sai dai kawai su tsinci kansu a wajan ‘yan sanda. To hakan ya sa muka tsaya muka duba wace hanya ce za ta magance mana wannan matsalar? Inda take muka ɗauki shawarar magabata cewa, mu kawo Dokoki a gare mu masu zafi don taka wa duk wani mai muguwar aniya burki, don mu wanke kanmu daga ɓata sunan da ake wa masu sana’ar sayar da waya a nan PZ bakin ɗaya.

To mun gode Allah ya zuwa yanzu dai babu wata matsala irin ta baya sai dai wadda ba a rasa ba amma tun daga lokacin da aka ɗora ni a matsayin shugaba na wartaki duk masu ɗauke- dauken kayan mutane, na kori masu ɓata yara ƙanana kuma na nemi haɗin kan ‘yan sanda da duk wasu jami’an tsaro wajan tabbatar da doka da odo a wannan kasuwa ta wayar salula.

Bugu da ƙari bias ga irin gudummawar da nake bai wa jami’an tsaro wajan maganci duk wani abu na rashin gasKiya hakan ya sa har yanzu in za a yi wani mitin da ya shafi binciken wani abu da ya shafi harakar mu, to sukan kira ni don in taimaka masu da wasu shawarwai kuma kamar hukumar tsaron na Jami’ar Ahmadu Bello muna da kyakkyawr fahimta da su.

Ƙarshe shugaban ya yi kira ga gwamnati cewa, don Allah tunda akwai tsari mai kyau a wannan Ƙungiya to in har akwai wani taimako da suke bai wa Ƙungiyoyi to a tuna da Ƙungiyar masu sayar da wayar salula da ke PZ Zariya don suma sun cika duk wani sharaɗin da gwamnati ke buƙata, don haka taimakawa ’ya’yan Ƙungiyar zai ba matasan da suke cikin sana’ar damar zuwa karatu da bunƙasa sana’ar kamar yadda sauran Ƙasashen duniya suke .

Yanzu haka wannan ƙungiya bincike ya nuna cewa babu wata Kasuwar wayar salular da za ta ja da ita a ɓangaren masana gyaran wayar da kuma Kasuwancinta, kuma a halin yanzu suna shirye-shiryen gudanar da zaɓe muƙamai daban- daban don cigaban ƙungiyar wanda hakan ya sa shugabna ya yi kira ga ’ya’yan Ƙungiyar da Kwamitin shiraya zaɓen da su ji tsoran Allah a kan dukkan abin da za su gudanar a kan wannan zaɓen mai zuwa

Exit mobile version